in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar da shugaba Xi zai kai a Swiss tana da babbar ma'ana
2017-01-11 11:07:44 cri

Bisa gayyatar da kwamitin tarayyar Swiss ya yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasar tsakanin ranakun 15 da 18 ga wannan wata, kana zai halarci taron shekara shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na Dawos na shekarar 2017, ban da haka kuma, yayin ziyararsa a kasar ta Swiss, shugaba Xi zai ziyarci hedkwatar MDD dake Geneva da hedkwatar hukumar WHO, da kuma hedkwatar kwamitin shirya wasannin Olympic na duniya dake Lausanne. A jajibirin ziyarar, jakadan kasar Sin dake wakilci a Geneva Ma Zhaoxu ya gaya wa manema labarai cewa, ziyarar da shugaba Xi zai kai a kasar tana da babbar ma'ana.

Jakadan kasar Sin dake Geneva Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai a kasar ta Swiss tana da babbar ma'ana a fannoni da dama, yana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya suna kokarin daidaita tsarin tattalin arziki da tsarin siyasa domin samun kyautatuwa, a karkashin irin wannan yanayi, shugaba Xi zai kai ziyara a kasar Swiss, ana iya cewa, wannan ziyarar wani muhimmin matakin diplomasiyya ne da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda ke karkashin jagorancin babban sakatare Xi ya dauka, haka kuma ziyarar da shugaba Xi zai kai, za ta yi tasiri mai zurfi ga farfadowar tattalin arzikin duniya, da kwaskwarimar da ake gudanarwa kan tsarin tafiyar da harkokin duniya, da karfafuwar ikon MDD, tare kuma da hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa baki daya."

Ma Zhaoxu yana ganin cewa, kasar Sin ta fara gudanar da harkokin diplomasiyyarta ne daga dandalin tattalin arzikin duniya na Dawos a farkon shekarar 2017, lamarin yana da muhimmiyar ma'ana. Yanzu kasashen duniya suna fuskantar rikicin kudi kamar yadda suka yi a baya, kuma wasu kasashe ba su son su samu ci gaba tare da sauran kasashen duniya, kana ana fama da kalubale da dama kamar su hare-haren ta'addanci, da matsalar 'yan gudun hijira, da sauyin yanayi da sauransu. Da gaske ne yanayin da kasashen duniya ke ciki yana da tsanani, har ana cikin zulumi. Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, "Ana gabatar da tambaya cewa, me ya faru? Wane irin mataki ne bil adama za su dauka? Amma, ba a samu amsa ba. Yanzu shugaba Xi Jinping zai halarci dandalin tattalin arzikin duniya na Dawos, kuma zai gabatar da muhimmin jawabi a taron shekara shekara na dandalin na bana, lamarin ya jawo hankalin jama'a matuka. Ana sa ran cewa, shugaba Xi zai gabatar da matsayin kasar Sin kan yanayin tattalin arziki da kasashen duniya ke ciki, kuma zai bullo da matakan da kasar Sin za ta dauka domin warware matsalolin da ake fuskantar, musamman ma wajen tabarbarewar tattalin arzikin duniya. Ana cike da imani cewa, shugaba Xi zai samar da alamar kasar Sin wajen sa kaimi kan karuwar tattalin arzikin duniya da kwaskarima kan tsarin tafiyar da harkokin kasashen duniya yayin da yake halartar dandalin Dawos."

Yayin ziyararsa, shugaba Xi zai halarci taron kolin da za a gudanar domin tattauna batutuwan da suke shafar makomar bil adama, inda zai gabatar da jawabi.

Ma Zhaoxu ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, wasu masana suna ganin cewa, bil adama suna cikin irin wani tsari mai rikici. A yayin taron kolin tunawa da cika shekaru 70 da kafa MDD a shekarar 2015, shugaba Xi ya taba gabatar da jawabi, inda ya yi cikakken bayani kan muhimmin tunaninsa kan makomar bil adama, kuma ya bullo da shirin kasar Sin domin gudanar da kwaskwarima kan tsarin duniya. Yanzu dai, shugaba Xi zai samar da karin haske kan batun. Ma Zhaoxu yana mai cewa, "Shugaba Xi zai halarci taron koli kan makomar bil adama a Geneva, kuma zai gabatar da muhimmin jawabi, domin kara kyautata tunanin yadda za'a ciyar da rayuwar bil adama gaba, lamarin zai kawo babban tasiri ga kirkire-kirkiren manufofin diplomasiyyar kasar Sin, da kwaskwarima kan tsarin tafiyar da harkokin duniya."

Yayin ziyarar da zai yi a Swiss, shugaba Xi zai ziyarci hedkwatar hukumar lafiya ta duniya wato WHO dake Geneva, da hedkwatar kwamitin shirya wasannan Olympic na duniya dake Lausanne, wannan shi ne karon farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a wadannan hukumomin biyu.

Ma Zhaoxu ya nuna cewa, hukumar lafiya ta duniya tana taka muhimmiyar rawa wajen magani da kuma yaki da annoba, da sulhunta harkokin kiwon lafiya a fadin duniya. Ziyarar da shugaba Xi zai kai a hedkwatar ta nuna cewa, kasar Sin tana maida hankali sosai kan aikin kiwon lafiyar duniya.

Ma Zhaoxu ya kara da cewa, shugaba Xi zai kai ziyara a hedkwatar kwamitin shirya wasannin Olympic na duniya, lamarin shi ma ya nuna cewa, kasar Sin tana goyon bayan aikin kwamitin, saboda har kullum kasar Sin tana ba da muhimmanci matuka kan wasannin motsa jiki a kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China