in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mayar da da'a a gaba da kome yayin da take taimakawa Afirka wajen samun ci gaba mai dorewa
2017-01-10 12:02:50 cri

Yayin da Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin da takwaransa na kasar Tanzaniya Augustine Mahiga suka gana da manema labaru tare a ranar 9 ga wata, mista Wang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta bada muhimmanci kan da'a da kuma moriya, inda za ta mayar da da'a a gaba da kome, yayin da take taimakawa kasashen Afirka wajen tsayawa da kafarsu da kuma samun ci gaba mai dorewa.

Abokiyar aikinmu Tasallah na dauke da rahoto dangane da batu.

Minista Wang ya bayyana cewa, a yayin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kai ziyarar aiki a kasashen Afirka a shekarar 2013, ya gabatar da manufar kasar game da yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, wato nuna sahihanci wajen yin hadin gwiwar a-zo-a-gani da 'yan uwanmu na Afirka, da kyautata dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka ba tare da rufa-rufa ba, hakan ya bude sabon shafi wajen kyautata hadin kan da ke tsakanin Sin da Afirka. Sa'an nan shugaba Xi ya gabatar da wata muhimmiyar ka'ida wadda ba a ga irinta a baya ba, dangane da yadda za a zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashe masu tasowa a sabon zamani da muke ciki, wadda ta kunshi matakin sa muhimmanci kan da'a da moriya tare, amma a mayar da da'a a gaba da kome. A fannin hada kai da kasashen Afirka kuwa, kasar Sin za ta kara hada makomarta da makomar kasashen Afirka tare, za ta taimaka musu tsayawa da kafarsu da kuma samun ci gaba mai dorewa ta hanyar yin hadin gwiwa tare da su, a kokorin tabbatar da wadatuwar Sin da Afirka.

Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya ce, wannan muhimmiyar ka'ida da shugaba Xi ya gabatar dangane da yadda za a zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashe masu tasowa a sabon zamani da muke ciki, wato bada muhimmanci kan da'a da moriya tare, amma a mayar da da'a a gaba da kome, ya yi matukar nuna halin musamman na kasar Sin a sabon zamani, wadda ta gaji kyawawan manufofin diplomsiyya na kasar Sin, tare da dacewa da yadda ake gudanar da harkokin tattalin arziki da kasuwanci da kuma dunkulewar duniya baki daya. Yayin da kasar Sin take hada kai da kasashen Afirka, za ta ci gaba da bin manufar rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen, da rashin gindaya sharadin siyasa, da rashin tilastawa wani yin wani abu, da magance gurbata muhalli. Haka kuma kasar Sin za ta bi manufar nuna sahihanci wajen yin hadin gwiwar a-zo-a-gani da 'yan uwanmu na Afirka, da kyautata dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka ba tare da rufa-rufa ba, haka zalika za ta yi kokarin samun zaman daidaituwa da tabbatar da moriyar juna, tare da bin dokokin kasashen Afirka da girmama al'adun gargajiyar al'ummar Afirka.

Bayan haka kuma, a yayin taron manema labarun, Wang Yi ya ci gaba da cewa, yanzu haka, kasashen Sin da Afirka suna himmatuwa wajen aiwatar da ra'ayi daya da aka cimma a fannoni daban daban a yayin taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, suna tafiyar da manyan shirye-shirye guda 10 na yin hadin gwiwa a tsakaninsu, inda suka mayar da masana'antun Afirka da zamanintar da aikin gona a nahiyar a matsayin muhimman burika da ake fatar cimmawa. Kullum kasar Sin za ta sa muhimmanci kan da'a da moriya tare, amma a mayar da da'a a gaba da kome, za ta ci gaba da hada manufofinta na raya kasa da manufofin kasashen Afirka tare, ciki har da na kasar Tanzaniya, a kokarin farfado da nahiyar Afirka da bunkasa Afirka da Sin.

A wannan rana kuma, yayin da ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Tanzaniya suka yi shawarwari a tsakaninsu, Wang Yi ya nuna cewa, duk wani irin ci gaban da kasar Sin za ta samu, har kullum tana matsayin wata kasa mai tasowa, don haka za ta ci gaba da himmatuwa wajen kiyaye moriyar bai daya ta kasashe maso tasowa ba tare da kasala ba. Kasar Sin tana son inganta tuntubar juna da kasashen Afirka, ciki har da kasar Tanzaniya, karkashin tsarin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da sauran tsare-tsare, tana son zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da su a harkokin bangarori 2 da ma al'amuran duniya, a kokarin kara azama kan ci gaban Afirka, da kuma kiyaye moriyarsu ta bai daya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China