in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tallafin kasar Sin ga Afirka goyon baya da taimako ne ba mulkin mallaka ba
2017-01-09 11:04:30 cri

Yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ke ziyarar aiki a kasar Madagascar ya bayyana cewa, injiniyoyin kasar Sin sun shiga sassan nahiyar Afirka masu nisa, ciki hadda Madagascar domin bunkasa nahiyar, sabanin ci da gumin jama'ar nahiyar ko gudanar da mulkin mallaka, da kuma nuna musu bambanci kamar yadda 'yan kasashen yammacin duniya suka taba yi a da.

Kasar Madagascar ta zama zango na farko a ziyarar Wang Yi a kasashen Afirka biyar a wannan karo. A cikin shekaru 20 da suka gabata, ko da yaushe Afirka ta kan zama zangon ziyarar farko da ministan harkokin wajen kasar Sin kan yi a ko wace shekara, lamarin da ya shaida muhimmancin da kasar Sin ke sanya wa Afirka a cikin harkokinta na diplomasiyya.

Yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwararsa ta kasar Madagascar Béatrice Atallah suka gana da manema labaru a ranar 7 ga wata, wani dan jarida na kasar Madagascar ya yi wa Madam Atallah wata tambaya mai tsauri, yana mai cewa, yayin da wani kamfanin kasar Sin ke gudanar da ayyukansa a kasar Madagascar, an samu barkewar rigima a tsakanin wasu bangarori biyu bisa rashin fahimtar juna. Ko ministocin biyu sun tattauna wannan batu yayin ganawar tasu, kuma ta yaya za a kai ga warware wannan batu a nan gaba?

Game da wannan, Madam Atallah ta ba da amsa ba tare da boye komai ba. Inda ta ce, yayin da gwamnatin kasar Sin ke nuna wa kamfanoninta goyon baya wajen neman samun bunkasuwa a ketare, ta kan dora muhimmanci sosai kan girma dokoki da ka'idoji, kana da al'adun kasashen waje, ba kawai a Madagascar ba, har ma da sauran kasashen Afirka tana bin wannan ka'ida.

Madam Atallah ta kara da cewa, idan an gamu da wasu kananan matsaloli, abin da ya kamata a yi shi ne a yi kokarin samun hanyar warware su, a maimakon tsananta su.

Bugu da kari, Madam Atallah ta jaddada cewa, tabbas wannan ziyara ta Mr. Wang Yi za ta taka muhimmiyar rawa ga raya dangantakar tattalin arziki da ke tsakanin Madagascar da Sin, wanda hakan zai kara jawo hankulan masu zuba jari na kasar Sin.

A nasa bangaren kuma Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, kamar yadda Madam Atallah ta fada, yayin da gwamnatin kasar Sin ke karfafa zukatan kamfanonin Sin wajen zuba jari da raya ayyuka a Afirka, ta kan bukace su su bi dokoki da ka'idojin wurin, tare da girmama al'adun gargajiya na wurin, da sauke nauyin da ke bisa wuyansu, da kiyaye muhallin halittu na wurin, a kokarin taimakawa jama'ar Afirka samun kyautatuwar zamansu.

Wang Yi ya kara da cewa, yawancin kamfanonin Sin na iya bin wadannan ka'idojin. Ko da yake a kan wasu kananan matsalolin, kamar yadda Madam Atallah ta fada, ba duk da haka ba za a iya mantawa da nasarorin da kasashen biyu suka samu ta hanyar hadin kansu na cimma moriyar juna ba. Haka zakila, kasar Sin na mai da hankali sosai kan warware irin wadannan matsaloli ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.

Wang Yi ya kuma yi tsokaci da cewa, Sin da Madagascar dukkansu kasashe ne masu tasowa, kuma 'yan uwan juna ne. Don haka hadin gwiwa a tsakaninsu ba hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa ne kadai ba, a'a taimako da kuma goyon baya ne da 'yan uwa ke nunawa juna. Kaza lika kasar Sin ta tura injiniyoyinta zuwa Madagascar duk da nisan ta, ba domin ci da gumin jama'ar kasar ko yin mulkin mallaka ba, a maimakon haka, cikin sahihanci ne, kasar Sin na da aniyar tallafawa kasar wajen samun bunkasuwa cikin sauri.

Ban da wannan, Wang Yi ya ba da misali da cewa, a 'yan kwanakin baya, an kira taron koli na kasashe masu magana da harshen Faransanci a kasar Madagascar, kuma ko da yake kasar Sin ba ta halarci taron ba, duk da haka an gudanar da taron ne a cibiyar tarukan kasa da kasa da aka gina bisa taimakon kasar Sin, kan otel din da ya karbi baki, otal ne da aka gina bisa taimakon kasar Sin.

Lamarin ya shaida cewa, lallai kasar Sin ta taimakawa kawarta Madagascar bisa matakai na hakika.

Har wa yau Mr. Wang Yi ya ce ko da a baya lokacin da take fama da talauci, kasar Sin ta tallafawa Afirka. Kuma a nan gaba ma, sakamakon kara bunkasuwar kasar Sin, za ta gudanar da dimbin ayyuka na a zo a gani domin ci gaban kasashen Afirka ciki har da Madagascar, da kuma kyautatuwar zaman rayuwar jama'ar kasashen nahiyar. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China