in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawon bude ido ya ciyar da cudanyar al'adu tsakanin Sin da Afirka gaba
2017-01-06 13:01:50 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai kai ziyara zuwa kasashen Afirka biyar tsakanin ranakun 7 da 12 ga wannan watan da muke ciki, wannan ne karo na 27 a cikin shekaru 27 da ministan harkokin wajen kasar Sin ya zabi kasashen Afirka domin fara kai musu ziyara a farkon shekara. Yanzu dai, bisa zurfafuwar huldar dake tsakanin Sin da Afirka, cudanya da zumunta dake tsakanin al'ummomin sassan biyu su ma suna kara karfafuwa a kai a kai.

A halin da ake ciki yanzu, an kafa wani kamfanin samar da hidima ga masu yawon bude idon da sha'awar zuwa kasashen Afirka, wanda ake kira "Bobu Afirka", Shi Yingying wadda ta kafa kamfanin ta yi mana bayani cewa, "An halacci Dan adam ne daga halittu, shi ya sa kullum suke jin dadin zama a cikin muhallin halittu, amma yanzu akwai wasu dabbobi dake fuskantar barazanar karewa, a saboda haka, wasu tunanin matakin za mu dauka domin warware wannan matsalar."

Shi Yingying ta kafa kamfanin Bobu ne saboda ya dace da sunan wani nau'in itace a nahiyar Afirka mai suna Baobab, ma'anarsa ita ce, ana fatan daukacin al'ummomin fadin duniya za su ci gajiyar halittun Afirka.

Tun farkon kafuwar kamfanin, wasu masu sha'awar daukan hotuna suka yi tattaki zuwa kasashen Afirka, inda suka dauki hotuna da dama, daga bisani suka nuna wa Sinawa wadannan hotunan, kana suka yiwa Sinawa bayani game da kokarin da Sinawa ke yi a kasashen Afirka, misali, masu aikin sa kai na kamfanin Bobu kusan hamsin sun taba yin fassara wasu labarai ko rahotannin da aka buga a jaridu ko mujallun kasashen Afirka zuwa harshen Sinnanci, ta yadda Sinawa dake zaune a Afirka za su karanta, daga baya a kai a kai Sinawa dake gida nan kasar Sin suka nuna sha'awarsu a wadannan takardun, Daga nan ne kamfanin Bobu ya fara samar da hidima ga Sinawa wadanda ke sha'awar yawon shakatawa a Afirka a fannoni daban daban, misali bayanai kan al'adu, da samar da hotunan da abin ya shafa, da bayanai game da kare dabbobi, da aikin samar da taimako ga masu bukata da sauransu. Shi Yingying ta gaya mana cewa, "Mutane da dama su kan bukace mu a lokacin da muka dawo daga kasashen Afirka cewa, ina bukatar wannan kaya, ko wancan kaya, saboda ba su taba zuwa kasashen Afirka ba, shi ya sa suke matukar sha'awar kayayyakin Afirka, kuma suna son su kara fahimtar nahiyar Afirka, a saboda haka, ina ganin cewa, ya dace mu yi kokarin yada al'adun Afirka ta hanyar yin bayani game da kayayyakin nahiyar."

Ban da wannan kuma, kamfanin Bobu yana kokarin yada al'adun kasar Sin a kasashen Afirka, misali yana gudanar da wani aiki mai taken "Bari in kawo maka kasar Sin, idan ba ka samu damar zuwa kasar ba", masu yawon bude ido da suka zo daga kasar Sin suna shiga unguwannin biranen kasashen Afirka domin nuna wa mazauna wurin hotunan da suka dauka a kasar Sin, kuma su kan fassara bayanan kalmomin zuwa Turanci su kuma bai wa mazaunan hotunan kyauta.

Shugabar kungiyar Azizi Life ta kasar Ruwanda Mukamazimpaka Juliet ta bayyana cewa, "Masu aikin sa kai na kamfanin Bobu su kan je kauyuka da unguwanninmu domin su yi hira da mu, abokai da suka zo daga kasar Sin suna iya fahimtar halin da al'ummar Ruwanda ke ciki, mu ma al'ummar Ruwanda muna fahimtar abubuwan da suka faru a kasar Sin, abubuwan da suka fi jawo hankalinmu su ne kwarewar aiki, da yawon bude ido, da kiwon lafiya da kuma aikin ba da ilmi ga yara."

A kokarin da ya ke na kara kyautata aikin hidima, kamfanin ya yi hayar wasu masu aikin sa kai a kasashen Afirka, misali a kasar Kenya, an kafa wata cibiyar kula da yara mai suna Jambo Toto, wato "Maraba yara", shugabar cibiyar Rose Njalale ta bayyana cewa, "Kamfanin Bobu ya taimakawa cibiyarmu da yaranmu, misali, ya samar mana teburan karatu da alkalamin rubuta da kayayyakin da ake amfani da su a dakin dafa abinci. Haka kuma kamfanin ya kan ba mu kyautar tufafi. Hakiki taimakon da kamfanin Bobu na kasar Sin ya ke ba mu zai taimaka mana wajen cimma burinmu."

Shugabar hukumar yawon bude ido ta kasar Kenya Jacinta Nzioka Mbithi tana ganin cewa, cudanyar dake tsakanin al'ummomin kasashen Sin da Afirka za ta taimaka matuka wajen karfafa zumuncin dake tsakanin sassan biyu, tana mai cewa, "Yanzu Sin da Kenya suna gudanar da cudanya dake tsakaninsu yadda ya kamata, zumuncin dake tsakanin sassan shi ma ya kara karfafa, kana masu yawon shakatawa dake zuwa Kenya daga kasar Sin su ma suna karuwa a kai a a kai."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China