in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na kara zurfafa hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashen Afirka
2017-01-05 11:09:03 cri

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana kara zurfafa hadin gwiwa mai sada zumunta bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninta da kasashen Afirka, sassan biyu kuma suna gudanar da hadin gwiwa mai moriyar juna a fannoni daban daban yadda ya kamata, musamman ma a shekarar 2016 da ta gabata.

Kenya kasa ce mafi saurin bunkasuwar tattalin arziki a yankin gabashin Afirka, ita ma muhimmiyar kasa ce a nahiyar wace kasar Sin take gudanar da hadin gwiwa da ita a fannonin gina layin dogo, da gina hanyar mota ta zamani, da zirga-zirgar jirgin sama, da masana'antu da kuma samar da kayayyaki, musamman ma a fannin samar da kayayyakin more rayuwar jama'a. Yanzu, Sin da Kenya suna gudanar da hadin gwiwa daga duk fannoni a birnin Mombasa na kasar ta Kenya, kamfanonin kasar Sin da dama suna taimakawa matuka kan aikin samar da kayayyakin more rayuwar jama'a a birnin.

A ranar 9 ga watan Janairun shekarar 2016, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya halarci bikin fara aikin hanyar mota da ta hada tashar ruwa ta Reitz ta birnin Mombasa da filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Moi, wadda kamfanin Wuyi na kasar Sin ne ya gina, inda ya bayyana cewa, aikin yana da babbar ma'ana, yana mai cewa, "Bayan da hanyar nan ta fara aiki, ba ma kawai za a kara samun damammakin samun jari da gudanar da ciniki dake tsakanin kasashen yankin gabashin Afirka kamar su Kenya da Uganda da Ruwanda da Burundi da kasashen dake yankin tsakiyar Afirka ba ne, har ma zata sa kaimi kan yawon shakatawa a kasashen, to, idan adadin masu yawon bude ido da za su zo yankunan suka karu, sai mazauna wuraren su kara samun guraben aiki, musamman ma matasa za su samu moriya daga wajen."

Kawo yanzu, adadin ayyukan hadin gwiwa masu samar da kayayyakin more rayuwar jama'a dake tsakanin Sin da Kenya ya karu bisa babban mataki, har za su taimaka matuka wajen karuwar adadin GDP a kasar.

A ranar 22 ga watan Satumban shekarar 2016, asusun raya Sin da Afirka ya kafa ofishin reshensa na biyar a kasashen Afirka a birnin Nairobin kasar Kenya. Yayin bikin fara aikin ofishin, ministan sufuri da kayayyakin more rayuwar jama'a da gidajen kwana da ci gaban garuruwa da kauyuka na Kenya James Wainaina Macharia ya bayar da wani jawabi, inda ya bayyana cewa, kafuwar ofishin asusun a kasarsa zai kara jawo hankalin kamfanonin kasar Sin domin su zuba jari a kasar ta Kenya, kana zai sa kaimi kan ci gaban jirga-jirgar jiragen sama da samar da kayayyakin more rayuwar jama'a da tasoshin ruwa da aikin kera na'urori a kasashen dake yankin gabashin Afirka. Macharia yana mai cewa, "Kasar Sin ta zabi birnin Nairobi domin kafa ofishin asusunsa, hakan ya nuna mana cewa, kasar Sin tana cike da imani kan hadin gwiwa dake tsakaninta da Kenya, shi ma ya bayyana cewa, Kenya tana taka muhummiyar rawa wajen ci gaban tattalin arziki a yankin."

Game da kasar Ruwanda kuwa, duk da cewa, ta taba gamuwa da kashe-kashen kare dangi a shekarar 1994, amma yanzu ta samu ci gaba cikin sauri, har ta kai sahun gaba a Afirka. Kasar Sin kuma tana gudanar da hadin gwiwa da Ruwanda a fannoni daban daban yadda ya kamata, wasu kamfanonin kasar Sin da dama sun ba da gudummawarsu.

Wata mata 'yar kasar Ruwanda mai shekaru 25 Umubyeyi Sandrine ta gaya mana cewa, aikin gina gidajen kwana Vision City da kamfanin CCECC na kasar Sin yake gudanar a Kigali, babban birnin kasar Ruwanda ya cimma burin samun gidajen kwana na al'ummar Ruwanda. Sandrina ta bayyana cewa, "Kamar yadda shugabanmu Kagame ya fada, bisa muradun ci gaban kasar Ruwanda nan da shekarar 2020, gwamnatin Ruwanda tana kokarin samar da wata kasa mai kyan gani ga al'ummarta, wannan aikin gina gidajen kwana aiki na farko ne da aka samar mana, gaskiya yana da kyan gani."

Kasar Equatorial Guinea tana yamma maso tsakiyar Afirka, ita ma tana gudanar da hadin gwiwa da kasar Sin lami lafiya, ko ina ana iya ganin alamar kasar Sin, misali, tashar samar da lantarki ta hanyar yin amfani da ruwa Djibloho tana samar da lantarki ga yawancin wuraren fadin kasar.

Fei Ming, 'dan kasar Sin ne wanda yake aiki a tashar har tsawon watanni shida, ya gaya mana cewa, "Ina jin dadin aiki a nan, na koyi abubuwa da dama a nan, idan an gamu da matsala, za a samar mana damammakin samun horaswa, kamar yadda ake yi a kasar Sin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China