in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na taka muhimmiyar rawa a yaki da cinikin hauren giwa
2017-01-04 12:06:09 cri

A kwanakin baya ne, ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata sanarwa game da hana cinikin hauren giwa da safarar kayayyakin dake da nasaba da hauren giwa, inda aka tanadi cewa, za a hana duk wasu ayyukan da suka shafi amfani da hauren giwa a matakai daban daban a nan kasar Sin kafin ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2017 da muke ciki, domin shawo kan laifuffukan cinikin hauren giwa da sauran namun daji da kuma shuke-shuke. Bayanai na nuna cewa, kudurin da gwamnatin kasar Sin ta tsai da yana da matukar muhimmanci a yakin da ake da cinikin hauren giwa a fadin duniya.

A cikin sanarwar da ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar, an tabbatar da cewa, za a hana a sayar da hauren giwa da kayayyakin da aka samar daga hauren giwa a kasuwanni, ko ta yanar gizo nan da karshen shekarar bana. An kuma bukaci kamfanonin da suke samar da kayayyakin hauren giwa da su daina gudanar da aikin gyara kayayyakin hauren giwa, su kuma daina sayar da kayayyakin. An kuma bukace su da su je hukumomin kula da harkokin masana'antu da kasuwanci na kasar domin gabatar da bukatar soke wasu ayyukan da suka gudanar, ban da haka kuma hukumomin al'adun kasar su samar da damammaki ga masu sana'ar sassaka kayayyakin hauren giwa domin su fara koyon wasu sabbin sana'o'i.

Shugaban kungiyar kare namun daji ta kasa da kasa Peter Knights ya zanta da wakilin gidan rediyonmu kan batun, inda ya bayyana cewa, wannan kuduri da gwamnatin kasar Sin ta bullo da shi, yana da muhimmanci kwarai ga giwaye, yana mai cewa, "Tun bayan da shugabannin kasashen Sin da Amurka wato Xi Jinping da Obama suka sanar da cewa, Sin da Amurka za su hana cinikin hauren giwa a kasashensu a watan Satumban shekarar 2015, muka yi murna da wannan albishirin matuka, saboda gwamnatin kasar Sin ta fitar da nata kudurin. Da zarar an daina gudanar da cinikin hauren giwa, farashin hauren giwa zai ragu nan take, hakan zai hana yin fataucin giwaye a kasashen Afirka. Abu mai faranta ran mutane shi ne, a lokacin da shugaba Xi Jinping ya sanar da kudurin hana cinikin hauren giwa, nan da nan farashin cinikin hauren giwa ya fara raguwa, fataucin giwaye a wasu kasashen Afirka kamar Kenya shi ma ya ragu, ana iya cewa, yanayin kare namun daji yana kyautatuwa a kai a kai, gaskiya wannan albishiri ne ga giwaye, kuma mu ma mun gode wa gwamnatin kasar Sin da ta tsai da wannan kuduri mai matukar muhimmanci."

Rahotanni na cewa, a halin da ake ciki yanzu, akwai kamfanonin kasar Sin kimanin 34 da ke samar da kayayyakin da ke da nasaba da hauren giwa, kana adadin kasuwannin da suke sayar da kayayyakin hauren giwa a kasar ta Sin ya kai 143. A mataki na farko, za a rufe kamfanonin da ke samar da kayayyakin hauren giwa 10 zuwa 15, da kuma kasuwannin sayar da kayayyakin hauren giwa 50 zuwa 60 kafin ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2017, sauran kuma za a rufe su kafin karshen shekarar bana, a sa'i daya kuma, hukumomin gwamnatin kasar Sin da abin ya shafa kamar su hukumar kula da kiyaye gandun daji da hukumar kiyaye tsaron jama'a da hukumar kwastan da hukumar kula da harkokin masana'antu da kasuwanci da sauransu, za su ci gaba da sa ido kan kayayyakin da ke da nasaba da hauren giwa da kamfanoni da 'yan kasar suke adana, ta yadda za a yi yaki da laifuffukan da suke shafar hauren giwa.

Shugaban kungiyar kare namun daji ta kasa da kasa Peter Knights ya bayyana cewa, yana fatan sauran kasashen duniya za su koyi da kasar Sin, kuma su hada kai tare da kasar Sin domin hana cinikin hauren giwa a ko wace fuska. Peter Knights yana cike da imani cewa, idan hukumomin da abin ya shafa na kasashen daban daban suka kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninsu, to, ko shakka babu za a samar da kariya mai karfi ga namun daji yadda ya kamata, yana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu, hukumomin kwastan na kasashe daban daban suna gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata, domin yaki da cinikin namun daji ba bisa ka'ida ba, a saboda haka, muna sa rai cewa, daukacin kasashen duniya za su yi hadin gwiwa, musamman ma tsakanin hukumomin kwastan da 'yan sanda domin hana aukuwar laifuffukan fatauci da kuma cinikin namun daji. Yanzu kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a fannin, har tana ba da jagoranci a wannan aikin, misali, sanarwar hana cinikin hauren giwa da ta bayar."

Tun daga shekarar 2010, ake samun karuwar laifuffukan fataucin giwayen Afirka da laifuffukan fasa kaurin hauren giwa, ya zuwa watan Maris na shekarar 2016 da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta dauki wani mataki game da daina shigo da hauren giwa da kayayyakin da aka samar da hauren giwa daga kasashen ketare har zuwa shekaru 3 masu zuwa, wannan ya taimaka matuka wajen hana da shigo da hauren giwa da kayayyakin da aka samar da hauren giwa daga ketare.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China