in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Zimbabwe ta gabatar da takardun bashi don dawo da imanin ta a idon jama'ar kasar
2017-01-03 14:47:43 cri

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta taba fito da takardar kudin kasar ta biliyan daya a shekarar 2008, lamarin da ya haifar da mummunan hauhawar farashin kaya a kasar. Har ma an taba daukar kudin kasar Zimbabwa a matsayin kudi maras daraja a duniya. Mummunan matsalar hauhawar farashin kaya da ake fama da ita a kasar Zimbabwe, ita ta sa ake amfani da kudin Amurka a dukkan kasar. Sakamakon karancin dalar Amurka da aka fuskanta a kasar a shekarar 2016, gwamnatin kasar Zimbabwe ta gabatar da takardun bashi a karshen watan Nuwanba na shekarar 2016, wanda za a rika amfani da shi a kasar tare da dalar Amurka. Gwamnatin kasar ta bayyana cewa, za ta kayyade yawan takardun bashin da za ta gabatar don dawo da imanin kudin kasar a idon jama'ar kasar.

Tun daga farkon shekarar 2016 ne, ake fuskantar matsalar karancin dalar Amurka a kasar Zimbabwe. Gwamnatin kasar Zimbabwe tana ganin cewa, wannan matsalar ta faru ne sakamkon dogaron da kasar ta yi wajen shigo da kayayyakin yau da kullum daga kasashen waje, rashin karfin sha'anin samar da kayayyaki na kasar, mummunan gibin kudin ciniki na kasar. A kokarin magance matsalar rashin kudin Amurka a kasar, da taimakawa kamfanonin kasar su samar da kayayyaki da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, babban bankin kasar Zimbabwe ya gabatar da takardun bashi da yawansu ya kai dala miliyan 200 tun daga ranar 28 ga watan Nuwanba na shekarar 2016, tare da samar wa kamfanonin kasar takardun bashi kyauta da yawansu ya kai kashi 5 cikin dari na yawan kudin da aka samu daga kayayyakin da aka fitar da su zuwa ketare. Shugaban babban bankin kasar John Mangudya ya bayyana cewa,

"Mun dauki wannan mataki ne don dawo da tsarin amfani da kudade iri daban daban a kasar. Manufarmu ita ce za a kara yawan takardun bashin da za a gabatar bisa yawan kayayyakin da za a fitar da su zuwa ketare. Aikin fitar da kayayyaki zuwa ketare shi ne zai taimakawa wannan matakin."

Ko da yake an gabatar da takardun bashi ne don sassauta matsalar karancin kudin Amurka, amma bayan da aka gabatar da takardun bashin, yawan dalar Amurka da ake iya samu daga wajen bankuna a ko wace rana yana ta raguwa, har ma yanzu haka bankuna da dama ba su iya samar da dalar Amurka kwata kwata. Wata malamar makarantar firamare a kasar mai suna Priscilla ta bayyana cewa,

"Koda yake an gabatar da takardun bashi ne don magance matsalar karancin dalar Amurka, amma hakan ya kara kawo matsala. Sabo da Jama'a ba su da imani kan takardun bashi, don haka sun fi son kiyaye yawan kudin dalar Amurka ko sauran kudade. Sannan suka boye kudadensu a gida, maimakon su yi amfani da su"

Masaniya a fannin ilmin tattalin arziki ta kasar Zimbabwe Monica ta yi nazari cewa, dalilin da ya sa jama'a ba su yi imani da takardun bashi ba, shi ne saboda an sha fuskantar mummunan hauhawar farashin kaya a kasar. A watan Yuli na shekarar 2008, gwamnatin kasar ta ce ana fuskatar hauhawar farashin kaya na kasar da ta kai kashi 2200000 cikin dari. A hakika dai, adadin ya fi wanda aka gabatar. Jama'ar kasar suna damuwa kan cewa, darajar takardun bashi za ta ragu kamar yadda kudin kasar Zimbabwe ya fadi warwas a baya. Monica ta bayyana cewa,

"Ina ganin cewa, takardun bashin suna da amfani, za su taimaka a nan gaba, amma matsalar ita ce, hadarin hauhawar farashin kaya da za a fuskanta. A shekarar 2007 da 2008, yanayin tattalin arzikin kasar Zimbabwe ba shi da kyau sam, kasar ta fuskanci matsalar hauhawar farashin kaya mafi tsanani a tarihi. Matsalar kuwa ta sa ba a iya sayen ko wane kaya a kanti ba, sannan kayayyayin da aka shigo da su cikin kasar ba bisa doka ba suna da tsada kwarai. Jama'a sun fama da yunwa ba domin ba su da kudi ba, sai dai domin kudin ba shi da daraja ko kadan. Don haka, rashin imani ga gwamnati da babban bankin kasar ya kasance kalubale mafi girma da ake fuskanta a halin yanzu. Idan darajar takardun bashi ta inganta a wasu makwanni bayan da aka gabatar da su, to jama'a za su amince da shi sannu a hankali, ganin cewa, ba za su iya rayuwa ba tare da tsabar kudi a hannunsu ba."

Don ganin an magance sake fuskantar matsalar hauhawar farashin kaya a kasar, babban bankin kasar ta Zimbabwe ya kayyade yawan takardun bashi da za a karba daga banki, wato yawan takardun bashi da kowane mutum zai samu daga banki bai iya zarce kimanin dalar Amurka 50 ba a kowace rana, adadin kuwa ba zai iya zarce kimamin dalar Amurka 150 a ko wane mako. Babban bankin kasar ya bayyana cewa, wannan mataki zai tabbatar da cewa yawan takardun bashi da aka gabatar ya dace da bukatun kasuwa, ta yadda za a iya magance gabatar da shi fiye da kima. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China