in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin shugaban CRI Wang Gengnian game da murnar sabuwar shekarar 2017
2017-01-01 11:48:17 cri


Yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara ta 2017, shugaban Gidan Rediyon CRI Wang Gengnian ya nuna fatan alheri ga masu sauraronmu dake kasashen ketare, inda ya ce, shekarar 2017 shekara ce ta kaza bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Gidan rediyon CRI wanda yake da tarihi shekaru 75 da kafuwa, yana ganin cewa, sabuwar shekarar za ta bude wani sabon shafi.

Kana a cikin sabuwar shekarar 2017 dake shirin kamawa, Gidan Rediyon CRI zai ci gaba da kyautata ayyukansa a fannonin watsa labarai da shirye-shirye masu kayatawarta yadda masu sauraronmu za su kara fahimtar kasar Sin, tare da fatan za su kara kaunar kasar Sin.

Ga jawabin da shugaba Wang Gengnian ya yi:

Abokai:

A wannan muhimmin lokaci da muke ban kwana da tsohuwar shekara 2016, sannan mu ke maraba da zuwan sabuwar shekara 2017, ina muku fatan alheri a sabuwar shekara ta 2017, a madadin Gidan Rediyon CRI da Gidan talabijin intanet na CIBN.

A farkon watan nan, masu sauraronmu dake ketare da dama sun taya CRI murnar cika shekaru 75 da kafuwa, wani mai sauraro a kasar Indiya ya bayyana a shafinsa na intanet cewa, da farko ya saurari labaran da CRI ya watsa ta bidiyo, da kuma shafin intanet, wannan ya sa a halin yanzu, ya sanya manhajan CRI a wayar salularsa, lalle CRI ya sami ci gaba kwarai da gaske cikin shekarun nan da suka gabata, a ko da yaushe yana debe masa kewa, ana sa ran ci gaba da bunkasa Gidan Rediyon CRI.

Kyakkyawan fatan da abokin ya nuna wa CRI ya nuna mana ci gaban da CRI ya samu cikin 'yan shekarun da suka gabata, kuma sabo da fatan alheri da goyon baya da masu sauraro da kuma abokanmu suka nuna wa CRI, sun sa CRI ya sami karfin ci gaba da bunkasa. Don haka, a madadin daukacin ma'aikatan Gidan Rediyon CRI, shugaba Wang yana mutukar godiya gare su.

Shekarar 2016 muhimmiyar shekara ce ga kasashen duniya, kasar Sin ta kuma ci gaba da ba da gudummawa yadda ya kamata, taron kungiyar G20 da aka yi a birnin Hangzhou na aksar Sin ya ci gaba da inganta gudanar shirin zirin tattalin arziki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, inda kasar Sin ta nuna matsayin ba na wata babbar kasa a duniya ba.

Kana, bunkasuwar kasar Sin tana janyo hankulan kasa da kasa, shi ya sa, kasar Sin take dukufa wajen kara fahimtar da kasashen duniya game da kasar. A shekarar 2016, Gidan Rediyon CRI ya karfafa bunkasuwar kafofin watsa labarai daban-daban, da kuma gaggauta hadin gwiwar dake tsakaninsa da abokan hukdar dake sassa daban-daban na kasashen duniya, inda ya gabatar da labaran kasar Sin masu kyau kwarai da gaske ga masu sauraronmu a duniya.

Dadin dadawa, CRI ya kulla yarjejeniyoyi da kafofin watsa labarai na kasashe uku da suka hada da Rasha, Serbia, Bengal, a yayin taron ganawar shugaban Sin da shugabannin kasashen uku. Haka kuma, ba za mu taba mantawa da nuna fatan al'ummomin kasar Sin ga duniya ko kadan ba, wadanda aka bayyanawa a yayin taron kungiyar G20, da kuma kumbon Tiangong-2 da na Shenzhou-11 da aka harba. Dukkan wadannan labaran sun samu karbuwa a wajen masu sauraronmu da ke sassa daban-daban na duniya.

Muna kokarin hada kasar Sin da kasashen ketare. Mun yi kokarin kafa kafofin watsa labaru na China News, da China Radio, da kuma China TV ta wayoyin salula domin masu kallo da sauraromu wadanda suke zaune a duk fadin duniya. Bisa shirin da muka tsara, za mu kaddamar da kafofin watsa labaru na "Sin da Burtaniya" da "Sin da Rasha" da "Sin da Italiya" da "Sin da Japan" da "Sin da Spainiya" da "Sin da Indiya" ciki harsuna iri daban daban. Bugu da kari, ayyukan da muka yi a sabbin kafofin watsa labaru na "IMaker na aiki" da "shirin Danube" sun jawo hankalin masu sha'awa da suka aiwatar da wadannan ayyuka tare da mu a kan wayoyin salula. A waje daya kuma, muna kokarin yin mu'amala da sauran kasashen duniya. Alal misali, mun bullo da wani shirin taimakawa 'yan jaridun kasar Rasha wajen nema da kuma watsa labarun kasar Sin a kan kafofin watsa labaru na zamani, da "taron shugabannin kafofin watsa labaru" a yayin taron tattaunawa na Asiya a garin Bo'ao, da "bikin rera wakokin kasashen Sin da Asean na shekarar 2016" da kuma "taron kara wa juna sani tsakanin daliban jami'o'in kasashen Sin da Amurka" wadanda suka jawo hankulan al'ummomin kasashen duniya sosai.

Ana girban abubuwan da aka shuka ne. A shekarar 2016, gidan rediyonmu na CRI ya samu sakamakon a zo a gani. Yawan mutanen da su ke yin mu'amala da mu ya kai fiye da miliyan dubu 55 da dubu dari 3, a yayin da yawan kulob-kulob na masu sauraronmu ya kai 4115, jimillar mutanen da suke saurara gidan rediyon CRI ya kai wajen miliyan 260. Yawan mutanen da suke sauraran shirye-shiryenmu ta kafofin sada zumunta ya kai fiye da miliyan 80. Idan ma ba ku kasance cikin daya daga cikin wadannan alkalumu ba, ku aminanmu ne.

Kamar yadda Valentina Nikolova, wata 'yar kasar Bulgaria ta rubuta a kan shafinta na sada zumunta, cewar "Gidan Rediyon CRI yana karfafa maka gwiwar neman cimma burinka. Yana kuma sanya ka kara fahimtar kyawawan abubuwa na kasar Sin. Sannan ya sanya ka kara sanin karfin kafofin sada zumunta. Na gode abokanmu daga kasar Sin mai nisa." Wadannan kalmomi tamkar kwarin gwiwa ne da wani tsohon aminmu ya nuna mana cikin sahihanci. Sun sanya mu tsayawa ga manufarmu tare da kokarin neman ci gaba.

Bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, shekara mai kamawa shekara ce ta kaji. A kowace wayewar rana, zakara ya kan yi cara yayin da gari ya waye, domin kowa ya yi haramar fara aiki a kowace rana. A ganin gidan rediyon kasar Sin CRI, wanda yake da shekaru 75 da kafuwa, sabuwar shekara tamkar wani sabon zango ne. Za mu ci gaba da kokarin kyautata kwarewrmu ta watsa muku labaru da rahotanni, ta yadda za ku kara sani da fahimta da kuma kaunar kasar Sin.

Daga karshe dai, ina muku fatan alheri, ina fatan ku da iyalanku za ku kasance cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan Beijing a sabuwar shekara mai kamawa. Na gode muku kwarai da gaske. (Maryam Yang, Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China