in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na ba da jagoranci a cikin harkokin duniya
2016-12-29 11:16:43 cri

Idan aka yi bita kan rawar da kasar Sin ta taka a cikin harkokin waje a fadin duniya a shekarar 2016 mai karewa, abu ne mai sauki a gane cewa, kasar Sin tana ba da jaroganci a fannoni daban daban, misali shirya taron kolin G20, da samar da shirin ta na sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya, da sauransu. Ko shakka babu kasar Sin tana ba da jagoranci a cikin harkokin duniya, kana tunanin gudanar da harkokin duniya na kasar Sin wato "yin shawarwari tare domin samun moriyar juna" shi ma ya samu karbuwa sosai daga al'ummomin kasashen duniya.

A yayin taron kolin G20 da aka gudanar a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake kudu maso gabashin kasar Sin a watan Satumbar bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayar da jawabi, inda ya bayyana cewa, "Gwamnatin kasar Sin tana son sanya kokari matuka tare da bangarori daban daban domin kara ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya gaba, tare kuma da cimma burin tabbatar da dauwamammen ci gaban tattalin arziki a daukacin kasashen duniya baki daya."

Yayin taron, karo na farko aka mayar da kirkire-kirkire a gaban kome, yayin da ake kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya, kuma karo na farko ne aka bayar da sanarwar shugaba kan batun sauyin yanayi, kana karo na farko da aka tsara shirin aiki kan ajandar dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya nan da shekarar 2030. Ban da haka kuma, a karo na farko da aka gabatar da shawarar samar da taimako ga kasashen Afirka da sauran kasashe masu fama da talauci domin raya masana'antu a kasashensu, ana iya cewa, daga taron kolin G20 na Hangzhou, a bayyane take kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin duniya.

Ya zuwa watan Nuwamban bana, an gudanar da taron kolin kungiyar APEC na shekarar 2016 a birnin Lima na kasar Peru. Bana ita ma shekara ce ta cika shekaru 25 da kasar Sin ta shiga kungiyar ta APEC, yayin taron Lima, shugaba Xi Jinping ya gabatar da matsayin da gwamnatin kasar Sin ta dauka, inda ya bayyana cewa, "Za mu tsaya tsayin daka domin kafa yankunan ciniki marasa shinge a shiyyar Asiya da tekun Pasifik, domin samar da tabbaci ga ci gaban tattalin arziki ba tare da rufa rufa ba a shiyyar, kana za mu kara sanya kokari domin kiyaye tsarin ciniki dake tsakanin bangarori da dama, ban da haka kuma za mu kara mai da hankali kan adalci, ta yadda za a cimma burin samar da wadata ga tarin jama'a a fadin duniya."

Kan batun rawar da kasar Sin take takawa a cikin harkokin duniya, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi bayyana cewa, ra'ayin da shugaba Xi ya gabatar a yayin taron Lima na kungiyar APEC ya yi daidai da matsaya guda da aka cimma a yayin taron APEC, wanda aka gudanar a birnin Beijing a shekarar 2014. Kuma hakan ya na da nasaba da sakamakon da aka samu a yayin taron kolin G20 na Hangzhou, dukkansu suna kara karfafawa zuciyar jama'a a fadin duniya.

Shugaba Xi ya taba bayyana ra'ayinsa kan tunanin da kasar Sin ke nacewa wajen gudanar da harkokin duniya, yana mai cewa, "Wane irin tsarin duniya zai kawo moriya ga al'ummomin kasashen duniya, wane irin tsarin gudanar da harkokin duniya zai sa al'ummomin kasashen duniya su samu moriya, wajibi ne al'ummomn kasashen duniya su yi shawarwari, bai kamata masu fada a ji kalilan su rika yanke shawara su kadai ba."

Ana ganin cewa, tunanin gudanar da harkokin duniya na kasar Sin ya sha bamban da na wasu kasashen yamma, wato muhimman abubuwan dake shafar tunanin ta ya hada da yin shawarari tare, da ginawa tare, da kuma samun moriya tare.

Kafin shekaru 3 da suka gabata, kasar Sin ta gabatar da shirin "ziri daya da hanya daya", wanda aka mayar da shi kokarin da kasar Sin ke yi, domin taka rawa a cikin harkokin duniya. Kawo yanzu, an riga an samu wasu sakamako, har ya kawo babbar moriya ga al'ummomin kasashen da abin ya shafa, wato gaba daya adadin jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a wadannan kasashe sama da 30 ya kai dalar Amurka biliyan 14, kana suka samar da guraben aikin yi kusan dubu 60 a kasashen. Shugaba Xi yana mai cewa, "Ana gudanar da shirin ziri daya da hanya daya ba tare da rufa rufa ne, saboda shirin yana shafar nahiyoyi uku wato Afirka da Asiya da kuma Turai, dukkan abokai, wadanda ke da sha'awa kan shirin suna iya shiga wannan babban aiki, muna fatan za mu sanya kokari tare domin samun moriya tare."

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi ya waiwayi sakamakon da kasarsa ta samu a fannin harkar diplomasiya a bana, yana mai cewa, matsayin kasar Sin a fannin ya daga a bayyane, kana kasar Sin tana yin babban tasiri kan tsarin duniya. Kaza lika kasar ta Sin tana kara taka rawa a cikin harkokin duniya yadda ya kamata. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China