in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nahiyar Afirka tana samun bunkasuwa
2016-12-28 13:19:47 cri

Nahiyar Afirka tana samun ci gaba sama da yadda take a baya. Yanzu kalmomi na buri, da bunkasuwa, da kuma zarafi sun maye gurbin kalmomin talauci, da yake-yake, da kuma kamfar abinci, wajen sifanta wannan nahiya.

Shekarar 2016, muhimmiyar shekara ce ta samun bunkasuwa a nahiyar Afirka, inda aka samu ci gaba a bangaren tabbatar da zaman lafiya a fannin siyasa, da samun sabon zarafi wajen raya tattalin arziki, tare da zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka lami lafiya. A sabili da haka, ana iya cewa nahiyar Afirka tana samun ci gaba sannu a hankali.

A shekarar 2016, an gudanar da babban zabe a kasashen Afirka da dama, kamarsu Kango-Brazzaville, Uganda, kasar Afirka ta Tsakiya, Nijar, Benin, Zambiya, Ghana, Gambiya da sauransu.

Yanzu haka kuma ana ci gaba da samun ci gaba, da aiwatar da kwaskwarima ga salon siyasa, da al'adu na musamman na kasashen Afirka. Kasashe da ke neman hanya mai dacewa a fannin siyasa, lallai ba su shiga yanayin siyasa mai cike da tangal tangal ba a sakamakon gudanar da babban zabe.

Shugaban Kango-Brazzaville, Denis Sassou-N'guesso da na Uganda, Yoweri Kaguta Museveni, sun jagoranci kasashen su har kusan shekaru 20 a jere. A bana sun sake lashe babban zaben kasashen nasu. Kuma shugaba Sassou ya fara wa'adin aikinsa na uku, yayin da shugaba Museveni ya fara wa'adin aikinsa na biyar. Kasashen biyu suna cikin yanayi mai kyau, ba tare da gamuwa da tarzoma ba a sakamakon hakan, matakin da ke nuna cewa, ana ci gaba da bin manufofin gwamnatin kasa yadda ya kamata.

A kasar Benin kuma, bayan da Thomas Boni Yayi ya jogorance ta har tsawon shekaru 10, bai gyara kundin tsarin mulkin kasar domin tsawaita wa'adin aikinsa ba, a sabili da haka, dan takara mai zaman kansa, Patrice Guillaume Athanase Talon ya lashe babban zabe, ya kuma zama shugaban kasar Benin lami lafiya.

Ban da haka, a yayin da ake fama da matsalar hada hadar kudi a duk fadin duniya, hakan ya yi babban tasiri ga bunkasuwar nahiyar Afirka. Amma duk da haka bisa babban karfinta na neman samun ci gaba, ana kiranta "Nahiya mai buri".

Raguwar farashin makamashi da na kayayyaki ta yi tasiri ga kasashen Afirka da dama. Hakan ya kuma kawo babbar illa ga kasashen Afirka masu fitar da man fetur, kamar Nijeriya da Angola da sauransu, da kasashen masu fitar da ma'adinai, kamarsu Afirka ta Kudu, Guinea, Saliyo, Zambiya da sauransu. A daya bangaren kuma, wasu kasashe dake raya tattalin arziki a fannoni daban daban sun sami ci gaba, wadannan kasashe sun hada da Cote d'Ivoire, Ruwanda da dai makamantansu.

Duk da haka kuwa, mafi yawan masana a fannin kididdiga, da hukumomin hada hadar kudi na duniya suna ganin cewa, tattalin arzikin nahiyar Afirka zai ci gaba da bunkasa yadda ya kamata.

Dalili na farko shi ne samun cikakken yanayi na kwadago a nahiyar Afirka. Na biyu kuma akwai kasuwannin kasashen Afirka dake samun bunkasuwa.

Baya ga haka, Sin da kasashen Afirka suna hadin gwiwa tsakaninsu cikin dogon lokaci, wadanda suka taimakawa juna yadda ya kamata. Yanzu Sin ta zama aminiyar cinikayya mafi girma ta Afirka, yayin da Afirka ta zama kasuwar kwangiloli ta biyu ga kasar Sin a ketare, kuma sabon wurin zuba jari na Sin.

Bana shekara ce ta farko da aka daga matsayin sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare tsakanin Sin da kasashen Afirka, zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare daga dukkan fannoni. Bangarorin biyu sun yi hadin gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata, tare da samun sakamako mai kyau.

A watan Yuli na shekarar bana, an gudanar da taron masu shiga tsakani, kan tabbatar da sakamakon da aka samu a taron kolin Johannesburg, na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a birnin Beijing, inda mutane sama da 300 daga kasashe membobin dandalin na Afirka 52 suka halarci taron.

Bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi iri iri har guda 63, yayin da jimillar kudadensu suka kai kimanin dala biliyan 18.3. A ciki, jimillar yarjeniyoyin hadin gwiwa dake shafar jarin da kamfanonin Sin za su zuba a kasashen Afirka kai tsaye, ya kai kimanin dala biliyan 16.2, wanda yawansu ya kai kashi 88.74 cikin dari. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China