in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara mai da hankali kan tsaron jama'a yayin da take kokarin samun ci gaba
2016-12-22 11:07:34 cri

A yammacin jiya Laraba ne, kungiyar da ke binciken yanayin da ake ciki dangane da tabbatar da dokar gudanar da aiki cikin kwanciyar hankali ta zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta fitar da wani rahoto a hukumance, inda aka yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana fuskantar matsaloli masu tsanani a wannan fanni, a saboda haka wajibi ne ta kara mai da hankali kan tsaron jama'a yayin da take kokarin samun ci gaba, ta yadda za a magance aukuwar duk wani mummunan hadari a kasar.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, manyan hadurra a fannin gudanar da ayyuka da dama sun faru a nan kasar Sin, misali, a shekarar 2015, kusan hadarin aiki daya ya faru a cikin kwanaki goma cikin adadin munanan hadurra da suka kai 38. Sai dai wadanda suka fi tsoratarwa su ne abubuwan da suka fashe a dakunan adana kayayyaki masu hadari a tashar jiragen ruwa ta birnin Tianjin, da hadarin zabtarewar kasa a birnin Shenzhen na lardin Guangdong.

Kwanakin baya, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Ping ya gabatar wa zaunannen kwamitin majalsiar wakilan jama'ar kasar Sin wani rahoto game da yanayin da ake ciki a fannin tabbatar da dokar gudanar da aiki cikin kwanciyar hankali, inda ya nuna cewa, yanzu kasar Sin tana fuskantar matsaloli masu tsanani a wannan fanni. Yana mai cewa, "Kawo yanzu ana fuskantar matsalali masu tsanani a fannin gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali, har ma ba a iya hana aukuwar hadurra masu tsanani yadda ya kamata, kana a wasu yankuna, an kasa kula da tsaron jama'a yayin da ake kokarin samun ci gaban tattalin arziki, misali, a wasu filayen hakar kwal da kamfanonin narka karafa, ba sa gudanar da ayyukansu bisa ka'ida, kana hukumomin gwamnatin da abin ya shafa ba su sa ido kan yadda ake gudanar da ayyukan yadda ya kamata ba, a sakamakon haka, munanan hadurra suka faru."

Game da irin wannan mummunan yanayi da ake ciki, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar Sin sun taba bayar da wata takarda mai taken "ra'ayi game da sa kaimi kan kwaskwari a fannin gudanar da aiki cikin kwanciyar hankali", inda aka yi nuni da cewa, za a kara kokari domin cimma burin aiwatar da tsarin sa ido kan harkar gudanar da aiki cikin kwanciyar hankali bisa ka'ida yadda ya kamata nan da shekarar 2020, Wannan zai taimaka wajen rage aukuwar hadurra a fadin kasar, kana za a yi kokari matuka domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a fanni sana'a, a karshe ana fatan, za a cimma burin gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali, tare kuma da samar da wadata ga al'ummar kasar ta Sin baki daya. Zhang Ping ya bayyana cewa, "Idan ana son cimma wannan burin, wajibi ne a kara mai da hankali kan dokar gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali, sannan a nace ga tunanin raya kasa cikin kwanciyar hankali, musamman ma a kara mai da hankali wajen tsaron jama'a yayin da ake gudanar da ayyuka a yau da kullum, wato dole ne a ko da yaushe a ba da muhimmanci ga rayukan jama'a. Idan har aka yi nasarar magance aukuwar munanan hadurra a fannin ayyuka, to, za a kara tabbatar da tsaro ga al'ummar kasa, haka kuma za a kara samar da tsaro ga ci gaban tattalin arzikin kasar. A saboda haka, kamata ya yi gwamnatoci a matakai daban daban na kasar da hukumomi da kamfanonin da abin ya shafa su kara mai da hankali a wannan aikin, tare kuma da kara yin kokari domin magance aukuwar hadurra."

Dokar gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali muhimmiyar doka ce a wannan fannin, idan ana son aiwatar da dokar cikin nasara, akwai bukatar a kara tsara wasu ka'idoji da manufofi da kuma matakai, amma kawo yanzu ba a kammala aikin ba tukuna, wato majalisar gudanarwar kasar Sin ba ta fitar da "ka'idoji game da tabbatar da dokar gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali ba". Saboda haka, kamfanoni daban daban suka bukaci gwamnatin kasar da ta fito da ma'auni game da gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali, Wannan zai kara kyautata ayyukan kamfanoni da kuma aikin sa ido kan kamfanonin. Zhang Ping yana mai cewa, "Kamata ya yi majalisar gudanarwar kasar Sin ta hanzarta fito da ka'idoji ba tare da bata lokaci ba, domin tabbatar da dokar gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali. A sa'i daya kuma, babbar hukumar sa ido kan aikin gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hanhali ta kasar Sin ta bukaci larduna da jihohi masu cin gashinsu da birane daban daban na kasar da su tsara hanzarta fito da ka'idojin tabbatar da dokar gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali a wurarensu. Kana kwamitin kare lafiyar jama'a na majalisar gudanarwar kasar Sin da kwamitin tsara ma'aunin kasar Sin su kara hadin gwiwa tsakaninsu domin bullo da wani ma'aunin gudanar da ayyuka cikin kwanciyar hankali yadda ya kamata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China