in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya ce za a kara karfin yakar 'yan ta'adda sakamakon kisan da aka yi wa jakadan kasar Rasha da ke Turkiya
2016-12-20 11:18:59 cri

A daren jiya ne, aka harbe Andrey Karlov, jakadan kasar Rasha dake kasar Turkiya a lokacin da yake halartar wani biki a birnin Ankara, babban birnin kasar Turkiya. A wannan rana da dare, Mr. Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan lamarin, yana mai cewa, wannan rashin mutunci ne da 'yan ta'adda suka aikata. Ya kuma bayyana cewa, masu aikata wannan laifi ba za su samu nasarar lalata dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Turkiya ba.

Shi ma Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiya ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan lamarin, inda ya bayyana kisan jakadan a matsayin takalar fada da nufin lalata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Erdogan ya ce, ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda ya ba da umarnin tura jami'an tsaron kasar Turkiya don su gudanar da bincike game da lamarin.

Bayan aukuwar lamarin, nan da nan, ministan harkokin cikin gidan na kasar Turkiya Suleyman Soylu, da ministan kiwon lafiya na kasar Recep Akdag, da Mr. Isik Kosaner, ministan tsaron kasar Turkiya suka shirya wani taron manema labaru a asibiti, inda aka samar da jinya ga wadanda suka jikkata a sakamakon. Mr. Soylu ya bayyana cewa, wannan lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 da minti 5 na daren 19 ga wata agogon kasar Turkiya. Ko da yake an kai Andrey Karlov zuwa asibitin, amma daga bisani ya mutu.

An bayar da labarin cewa, an harbe dan bindigar mai shekaru 22 da haihuwa har lahari a wurin da lamarin da faru. An kuma gano cewa, dan bindigar wani jami'in dan sandan Turkiya ne mai suna Mevlut Mert Altintas. Bayan ya bude wuta, yana ihu cewa, "kar a manta Aleppo, kar a manta Syria. Muna shan wahala bai kamata ku ji dadi ba."

Rahotanni na cewa, dan bindigar yana sanye ne da bakar kwat da laktaya inda ya harbe jakadan kasar ta Rasha da ke Turkiya lokacin da yake jawabi a bikin bude kolin zane-zane a birnin Ankara.

A daren jiya Litinin, shugaba, Putin ya nuna juyayi ga iyalin Andrey Karlov, inda ya yaba wa ayyukan da jakada Andrey Karlov ya yi a lokacin da yake aiki a kasar Turkiya, ya ce zai nemi ma'aikatar harkokin wajen kasarsa da ta ba shi lambar yabo ta kasar. A waje daya, Mr. Putin ya nuna cewa, harbe jakada Andrey Karlov, tamkar rashin mutunci ne da 'yan ta'adda suka sake aikatawa. 'Yan ta'adda suna yunkurin kawo cikas ga kokarin dawo da huldar dake tsakanin kasashen Rasha da Turkiya yadda ya kamata, inda suke son dakatar da ayyukan kawo zaman lafiya da ake yi a kasar Sham. Yanzu, kasashen Rasha, Turkiya da Iran suna kokarin kawo karshen rikicin kasar Sham. Daga karshe dai, Mr. Putin ya jaddada cewa, hanya daya tak ta magance wannan lamarin, ita ce ci gaba da kara karfin dakile 'yan ta'adda, kuma 'yan ta'adda za su girba abin da suka shuka.

A daren wannan rana, Mr. Dmitri Peskov, sakataren harkokin watsa labaru na shugaban kasar Rasha, ya bayyana cewa, shugaba Putin da takwaransa na kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan sun yi musayar ra'ayoyi kan lamarin, inda suka kudurta cewa, za su kara karfin tsaron ma'aikatan diflomasiyyarsu, sannan bangaren Rasha zai tura wata tawagar bincike zuwa kasar Turkiya domin halartar aikin binciken lamarin kisan da aka yi wa jakadan Rasha. Madam Maria Zakharova, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa, kisan da aka yi wa jakada Andrey Karlov na kasar Rasha dake kasar Turkiya wani harin ta'addanci ne. Sabo da haka, kasar Rasha za ta nemi kwamitin sulhun MDD da ya tattauna batun yakar ta'addanci. Ta kuma bayyana cewa, dimbin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sun riga sun tura wa kasar Rasha sakwannin jaje, kana suka yi tir da wannan lamarin na ta'addanci.

Haka kuma kwamitin sulhun MDD da Mr. Ban Ki-mon, babban sakataren MDD bi da bi sun fitar da sanarwa game da lamarin, inda suka yi alla wadai da kakkausar murya kan kisan da aka yi wa jakada Andrey Karlov na kasar Rasha dake kasar Turkiya.

A cikin sanarwar da kwamitin sulhun MDD ya gabatar wa kafofin yada labaru, ya jaddada cewa, dole ne a gurfanar da wadanda suka shirya, kuma suka aikata wannan danyen aiki a gaban kotu. Bugu da kari, kwamitin sulhun MDD ya jaddada wajibcin tsaron ma'aikatan diflomasiyya dake zaune a kowace kasa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China