in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana kokarin dawowa da gidaje a matsayinsu na kwana, amma ba domin kasuwanci ba
2016-12-19 14:58:17 cri

A cikin sanarwar da aka fitar a yayin taron tattalin arziki na shekara-shekara na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka kammala a kwanan nan, an nuna cewa, dole ne a hanzarta bullo da dokokin da za su dace da hakikanin halin da kasar Sin ke ciki, da ka'idojin da ake bi a kasuwa, ta yadda za a rage yadda ake tsauwala farashin gidajen kwana, da karuwa ko raguwar farashin gidaje fiye da yadda ake zato. Masana sun bayyana cewa, furucin da mahukuntan Sin suka cewa "an gina gida ne domin a samar da gidajen kwana, ba domin kasuwanci ba", wannan ya alamta cewa, a nan gaba, za a mayar da gidajen da ake ginawa a matsayin gidajen kwana. A shekara mai zuwa, za a kara sa ido kan yadda ake sayar da gidajen da aka gina cikin hanzari, amma kuma ba a sayar da su kwata kwata ba a matsakaita da kananan birane. Mr. Qiu Baoxing, mataimakin ministan kula da harkokin gidajen kwana da bunkasa birane da yankunan karkara na kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin wannan sanarwar da aka fitar, an nuna cewa, "an gina gida ne domin samar da gidajen kwana, ba domin kasuwanci ba", wadannan kalamai sun tabbatar da cewa, an gina gidaje ne domin samar da gidajen kwana ga jama'a, ba domin neman karuwar tattalin arziki ba. Mr. Qiu yana ganin cewa, sanarwar, ta tabbatar da cewa, a lokacin da ake kokarin rage saurin karuwar farashin gidaje fiye da kima a kasuwa, dole ne a yi rigakafin tashi da saukar farashin gidaje fiye da kima. Amma wane irin mataki ya kamata a dauka a nan gaba? Mr. Qiu ya ce, "Daga farko dai, ya kamata gwamnatin tsakiya ta hanzarta kafa dokokin da za su dace da hakikanin halin da kasar Sin ke ciki, da ka'idojin da ake bi a kasuwa domin tabbatar da ganin an bunkasa kasuwar samar da gidaje lami lafiya. Haka kuma, bai kamata a tattauna matsalolin da ake fuskanta a yanzu kawai ba. Sannan, a dauki matakan hana zuba rancen kudi a kasuwar cinikin gidaje domin neman riba. Muddin aka dauki wadannan matakai, nan da nan za a iya ganin sakamako wajen shawo kan matsalar karuwar farashin gidaje fiye da kima. Bugu da kari, ya kamata a bambanta halin da kowane birni yake ciki. Ya kamata a samar da karin filayen gina gidaje a birane, inda farashin gidaje ke karuwa cikin sauri fiye da kima. Bai kamata a daina samar da filaye a birane wadanda suke da mazauna fiye da miliyan 5 ba. A waje daya kuma, a wasu manya manyan birane ana fuskantar matsalar saurin karuwar farashin gidaje fiye da kima. Sabo da haka, ya kamata a mayar da wasu ayyukan da ake da su a wadannan manya manyan birane zuwa wasu matsakaita ko kananan birane. Daga karshe kuma, ya kamata a dauki matakai iri iri , kamar su, shimfida karin hanyoyin mota daga manya manyan birane zuwa matsakaita ko kananan birane, samar da ingantattacen ilmi da kayayyakin kiwon lafiya a kananan birane domin a yi kokarin rage gidajen kwanan da aka gina wadanda har yanzu ba a sayar da su ba a matsakaita da kananan birane."

A ganin Mr. Yang Weimin, mataimakin direktan ofishin ba da jagoranci kan harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS, a shekara mai zuwa, za a kara sa ido kan yadda za a rage gidajen kwana da aka gina amma har yanzu ba a samar da su kamar yadda ya kamata ba a matsakaita da kananan birane. Mr. Yang ya bayyana cewa, "Dole a tsara manufofi bisa hakikanin halin da kowane birni yake ciki. A lokacin da ake kokarin rage gidajen da ba a sayar da su duka ba, dole ne a mai da hankali kan fannoni 4, wato shigar da manoma wajen miliyan dari 1 zuwa birane, kara saurin gyara tsoffin wuraren kwana marasa inganci, aikin samar da gidajen kwana masu rahusa, da kasuwar ba da hayar gidajen kwana."

Wasu masana sun kuma bayyana cewa, idan ana son bunkasa kasuwar samar da gidajen kwana yadda ya kamata a nan gaba, abin da ya fi muhimmanci shi ne a soke harajin gidajen kwana da ake biya domin rage yawan kudaden da ake zubawa a kasuwar gina gidaje, da kasuwar sayen gidaje domin neman riba kawai.

Mr. Jia Kang, wani masanin nazarin tattalin arziki ya bayyana cewa, "Yanzu ba za a iya daidaita matsalar ba bisa manufofin daidaita da rage yawan rancen kudi da ake samarwa. A lokacin da ake kokarin sassauta matsalar, ya kamata a hanzarta bullo da dokar biyan haraji kan gidajen kwana."

Amma, Mr. Xu Shanda, tsohon mataimakin direktan babbar hukumar biyan haraji ta kasar Sin yana ganin cewa, buga haraji kan gidajen kwana a nan kasar Sin, wannan ba ita ce matsalar dake gabanmu a halin yanzu ba ne, muhimmin batu shi ne a kafa doka bisa halin da kasar ke ciki. A nan kasar Sin, dukkan filayen birane suna karkashin gwamnati ne, kuma dukkan gonaki dake yankunan karkara suna hannun kungiyar manoma ne, ba hannun daidaikun mutane ba. Sabo da haka, ba a iya biyan haraji kan filaye ko gonaki, wadanda aka gina ko za a gidaje ba a kansu. Ana biyan harajin gidajen kwana ne kawai, in ji Mr. Xu Shanda. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China