in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Sin ta samu lambar yabon kiyaye zaman rayuwar al'umma
2016-12-14 11:18:27 cri

Kwanakin baya ba da dadewa ba, gwamnatin kasar Sin ta samu lambar yabo ta kiyaye zaman lafiyar al'ummar kasa, wadda kungiyar kiyaye zaman rayuwar al'ummomin kasashen duniya ta bayar, bisa babban sakamakon da ta samu a fannin.

Jiya Talata, daraktan cibiyar kula da aikin inshura kan zaman rayuwar jama'a ta ma'aikatar kiyaye zaman rayuwar al'ummar kasa da sarrafa albarkatun kwadago ta kasar Sin Tang Jisong ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, nan gaba gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da kokari, domin kara kyautata aikin kiyaye zaman rayuwar al'ummar kasar, tare da cimma burin tsara tsarin kiyaye zaman rayuwar al'umma a fadin kasar nan da shekarar 2020.

A yayin babban taro karo na 32 na kungiyar kiyaye zaman rayuwar al'ummomin kasashen duniya da aka gudanar a kasar Panama, kwanakin baya ba da dadewa ba, kungiyar ta baiwa gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin lambar yabon samun babban sakamakon kiyaye zaman rayuwar al'umma tsakanin shekarar 2014 da ta 2016, domin nuna yabo ga gwamnatin kasar Sin bisa babban sakamakon da ta samu a fannin kiyaye zaman rayuwar al'umma a cikin 'yan shekarun da suka gabata.

Bisa alkaluman da aka samar, an ce, a halin da ake ciki yanzu, adadin mutanen da suka shiga inshorar ritaya a kasar Sin ya kai miliyan 870, kana adadin Sinawan da suka shiga inshurar jinya ya kai biliyan 1 da miliyan 300, kana adadin wajen raunin aiki ya kai miliyan 216, adadin wajen rasa aikin yi ya kai miliyan 178, adadin wajen haihuwa ya kai miliyan 182.

Darakta Tang Jisong ya bayyana cewa, kawo yanzu an riga an kafa tsarin kiyaye zaman rayuwar al'umma da ya hada da mafi yawan mutane a duniya a nan kasar Sin, adadin da ya daga matsayin kiyaye zaman rayuwar al'ummomi a fadin duniya da kaso 11 bisa dari, har ya sa ma'aunin ya kai kaso 61 bisa dari a kasashen duniya. Tang Jisong yana mai cewa, "Daga adadin mutanen da suke samun moriya daga tsarin kiyaye zaman rayuwar al'ummar kasar Sin, ana iya gano cewa, adadin ya kara habaka daga dukkan fannoni. Misali daga garuruwa zuwa kauyuka, da kuma daga kamfanonin hukumomin gwamnatin kasar zuwa kamfanoni masu zaman kansu, kana daga mutanen da suke da aiki zuwa wadanda suka rasa aiki, a bayyane take cewa, ana gudanar da tsarin kiyaye zaman rayuwar al'umma mai adalci a kasar Sin, saboda adadinsu shi ne mafi yawa a duniya, kuma babu banbanci tsakaninsu, duk da cewa, kila suna aiki a kamfanoni daban daban, ko ma basu da aikin yi."

Domin kara kyautata aikin, a shekarar 2014, gwamnatin kasar Sin ta fara aiwatar da shirin sa kaimi kan daukacin al'ummar kasar domin su shiga inshora iri iri da suke bukata, kuma tana sanya kokari mutuka domin cimma wannan buri nan da shekarar 2020. Tang Jisong ya ce, "Ana gudanar da wannan aiki ne ta hanyar yin hadin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati daban daban. Misali, ana tantance bayanai game da al'ummar kasar domin tabbatar da cewa ko sun riga sun sayi inshora, ko ba su saya ba. Da kuma ko suna ci gaba da saya. A sa'i daya kuma ana kokarin yada manufar gwamnatin kasar domin samar da hidima ga al'ummar kasa yadda ya kamata."

Tang Jisong ya yi nuni da cewa, yanzu wasu mutane suna yin aiki mai hadari, a saboda haka ma'aikatar kiyaye zaman rayuwar al'ummar kasar Sin ta gabatar da shirin samar da taimako gare su, domin samar da inshora ga wadanda suka samu rauni yayin aiki. Yana mai cewa, "Yanzu haka wasu ma'aikata suna gudanar da sabbin ayyuka. Misali, jigilar kaya na masu sayayya cikin sauri, da kuma aikin dake da nasaba da yanar gizo. A baya ba a kula da su sosai ba, shi ya sa muke kara kokari domin kyautata aikinmu a wannan fannin. Kafin karshen shekarar bana, za mu gudanar da aikin rajista a yawancin yankunan kasar, domin samar da hidima ga daukacin al'ummar kasar Sin, ta yadda za su yi inshorar da suke bukata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China