in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya tun bayan shigarta WTO
2016-12-12 11:57:08 cri

Ya zuwa jiya Lahadi 11 ga watan Disambar bana, kasar Sin ta riga ta shafe shekaru 15 a kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO. A cikin wadannan shekaru, kamfanonin kasar Sin sun nuna kwazo da himma wajen zuba jari da kuma gudanar da cinikiyya a kasuwannin duniya, kana kamfanonin jarin waje da kayayyakin da kasashen ketare suka kera, sun shiga kasar Sin a kai a kai. A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana sahun gaba a duniya wajen ciniki da kuma saurin samun ci gaban tattalin arziki. Ko shakka babu kasar Sin ta taimaka matuka ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

A kan titunan wasu biranen kasar Amurka, ana iya ganin bas bas masu amfani da lantarki da kamfanin BYD na kasar Sin ya kera. Tun bayan kafuwarsa, kamfanin BYD ya fara kera batir wanda ake iya cajin sa da lantarki. Ya zuwa shekarar 1999, wato a lokacin da aka yi shawarwari game da shigar da kasar Sin cikin kungiyar cinikin duniya, kamfanin ya fara yin kokari domin shiga kasuwannin duniya.

Manajar kamfanin BYD mai kula da sashen tallar kayayyaki Zhang Yue ta yi mana bayani cewa, a wancan lokaci, wasu ma'aikatan kamfanin guda 3 sun taba tafiya kasar Holand domin yin talla. Tana mai cewa, "Sun je Holand da kudi da kuma wasu batir, amma a wancan lolaci, ba a gudanar da ciniki a fadin duniya yadda ya kamata, shi ya sa suka gamu da wahalhalu, kuma ba su iya sayar da batir din kamfanin cikin gajeren lokaci ba."

Daga baya, ya zuwa shekarar 2001, kasar Sin ta yi nasarar shiga kungiyar cinikayya ta duniya. Kamfanin BYD ya samu ci gaba cikin sauri, Zhang Yue tana ganin cewa, kasar Sin ta shiga kungiyar cinikin duniya, lamarin ya samar da damammaki ga kamfaninta. Ta bayyana cewa, "Bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya, kamfaninmu ya samu damammaki da dama. Alal misali, muna iya yin tallar kayayyakinmu ga masu sayayya na nan gida kasar Sin, da kuma na kasashen ketare, ta yadda batir da muke kerawa ya samu karbuwa ga masu sayayya a fadin duniya, da haka kamfaninmu ya samu babban ci gaba a fannoni da dama."

Tun farkon lokacin da aka shigar da kasar Sin cikin kungiyar cinikayya ta duniya, an yi tsamani cewa, kila lamarin zai kawo babbar illa ga sha'anin kera mota na kasar Sin, amma yanzu shekaru 15 suka gabata, ba ma kawai bai kawo illa ga sha'anin kera mota na kasar Sin ba, har ma kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen kera mota, ana iya ganin sakamakon daga ci gaban kamfanin BYD. Duk da cewa kamfanin BYD ya fara kera mota a shekarar 2003, amma ya samu ci gaba bisa fiffikonsa a fannonin kasuwa da kuma fasaha. Manajar kamfanin Zhang Yue ta yi mana bayani cewa, "A baya, kamfanin BYD ya fi mai da hankali kan harkokinsa wajen batir da na'ura mai kwakwalwa, da kuma sadarwa. Yanzu kuwa ana iya yin amfani da wadannan fasahohi yayin da ake kera mota, kuma kamfanin ya nuna fiffiko wajen fasaha da kuma farashi. A saboda haka, kamfanin ya samu ci gaba cikin sauri."

Fu Xiaobai, wata mace ce dake aiki a wani kamfani a nan birnin Beijing, ko da yake tana shan aiki, amma ta kan je kasuwar Carrefour dake kusa da gidanta, ta gaya mana cewa, "Kusan ko wane sati, na kan je kasuwar Carrefour sau daya, saboda kasuwar tana kusa da gidana, na kan sayi kayayyaki na amfanin yau da kullum, kana na fi sha'awar sayen kayayyakin da aka shigo da su daga kasashen ketare, misali taliyar Italiya da sauran kayan abinci."

Da ci gaban da kamfanin BYD ya samu a kasuwannin duniya, da kasuwar Carrefour da Fu Xiaobai take sha'awa, ana iya gano cewa, tun bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya, a bayyane take cewa kasar ta samu bunkasuwa, a sa'i daya kuma, kamfanonin jarin waje su ma sun samu sakamako a nan kasar Sin. Abu mafi jawo hankalin jama'a shi ne, kayayyakin da kasar Sin take shigowa da su daga kasashen ketare sun karu, bayan da aka sauke harajin kwastan, hakan ya amfanawa zaman rayuwar al'ummar kasar Sin matuka.

Bisa alkawarin da kasar Sin ta yi yayin da ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya, kawo yanzu, kasar Sin ta kara bude kasuwarta ga kamfanonin kasashen waje. Kana adadin kamfanonin kasar Sin da suka shiga kasuwar kasashen duniya ya karu bisa babban mataki a cikin wadannan shekaru 15 da suka gabata, inda adadin jarin da kasar Sin take zubawa kai tsaye a kasashen ketare a ko wace shekara ya karu daga dalar Amurka biliyan 3 a shekarar 2001, zuwa dalar Amurka biliyan 140 a yanzu. A bayyane take cewa kasar Sin tana samun bunkasuwa tare da sauran kasashen duniya, bisa tushen cimma moriyar juna tun bayan da aka shigar da ita cikin kungiyar cinikayya ta duniya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China