in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta tsara sabon burin karuwar kudin shiga na manoma nan da shekarar ta 2020
2016-12-08 11:22:52 cri

A kwanan baya, ofishin kula da harkokin yau da kullum na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata takarda kan yadda za a kara yawan kudin shiga na manoma. Bisa takardar, za a ninka yawan kudin shiga na manoma sau daya nan da shekarar ta 2020 bisa na shekara ta 2010. A bayane ne an nuna cewa, za a taka rawar gani a kasafin kudi a lokacin da ake kokarin kara yawan kudin shiga na manoma, da kuma shigar da karin kudin al'umma a sha'anin noma a kauyuka. Kafin a fitar da wannan takarda, gwamnatin kasar ta fitar da jerin sabbin manufofin tabbatar da karuwar kudin shiga na manoma daya bayan daya.

Bisa wannan takarda mai taken "Wasu ra'ayoyi kan yadda za a kyautata manufofin nuna goyon baya ga matakan karuwar kudin shiga na manoma", an ce, nan da shekara ta 2020, za a ninka yawan kudin shiga na manoma sau daya bisa na shekara ta 2010. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta bayar, an ce, matsakaicin yawan kudin shiga da manoman kasar Sin suka samu a shekara ta 2010 ya kai kudin Sin yuan 5919. Bisa wannan sabon shiri, matsakaicin yawan kudin shiga da manoma za su samu a shekara ta 2020 zai kai kudin Sin yuan dubu 11 da 838, wato kimanin dalar Amurka 1720 a kowace shekara.

Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai iri dabam dabam domin tabbatar da cimma wannan buri. Ba ma kawai za ta ci gaba da zuba karin kudade kan kayayyakin yau da kullum na aikin noma da ba da tallafi ga aikin noma da kuma daidaita tsarin aikin noma da kyautata tsarin farashin kayayyakin amfanin gona ba ne kawai, har ma za ta shigar da aikin tattara kudade a yankunan karkara.

Mr. Hu Dinghuan, wani manazarci na cibiyar nazarta tattalin arzikin aikin noma da bunkasuwarsa ta hukumar nazarin harkokin aikin noma ta kasar Sin yana ganin cewa, tabbas ne za a iya ingiza kamfanoni da kuma mutane da su zuba jarinsu a yankunan karkara. Mr. Hu ya ce, "Wata muhimmiyar matsala ita ce, dole ne a sanya mutane su gane cewa, a lokacin da ake bukatar zuba karin kudade wajen kokarin zamanantar da aikin gona ne za a iya samun kudi. Amma dole ne mu gane cewa, ana bukatar zuba jari kan aikin gona cikin dogon lokaci ba tare da tangarda ba. Baya ga wannan kuma, ko da yake ba a iya samun riba mai yawa ba a kowace shekara, amma za a iya samun ribar aikin gona ba tare da tangarda ba."

Bisa wannan takarda, gwamnatin kasar Sin za ta karfafa manufofin taimakawa wadanda za su bunkasa sana'o'in aikin gona a yankunan karkara domin kokarin horas da wasu sabbin manoma wadanda za su fahimci sabbin fasahohin sana'o'in aikin gona. Bugu da kari, za a kara yin gyare-gyare kan ikon mallakar gonaki. Game da wannan batu, Mr. Hu Dinghuan yana ganin cewa, wannan hanya ce da aka wajabta mana mu bi a lokacin da muke zamanantar da aikin gona. "A lokacin da ake zamanantar da aikin gona, da farko a kara girman sana'ar aikin gona, wato yaya za a iya samar wa manoma wadanda suka kware wajen yin amfani da dimbin gonaki? Na biyu, wanene yake da ikon yin amfani da gonaki? A cikin wannan takarda, an ambata cewa, za a yi gyare-gyare kan ikon mallakar gonaki, an kuma ce, za a shirya kwasa-kwasan horaswa ga manoma."

A 'yan shekarun nan, manoma wajen miliyan 4 da dubu 500 wadanda suka yi aiki a wasu garuruwan sun koma garuruwansu domin kafa kamfanoni iri iri. Sabili da haka, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan nuna musu goyon baya a fannonin kiwo da sarrafa amfanin gona da tafiyar da sana'o'in yawon shakatawa a yankunan karkara da dai sauran sabbin sana'o'i da sabon salon bunkasa aikin gona, ta yadda za a iya kara kudin shiga da suke samu. Mr. Li Guoxiang wanda yake nazarta yankunan karkara a cibiyar nazarin zaman al'ummar kasar Sin yana mai cewa, "Mai yiyuwa ne wasu manoma su samu sabbin fasahohi da kudade a lokacin da suke aiki a garuruwa ko birane. Sun san hanyar kafa wani kamfani, amma suna damuwa game da tara kudade. A cikin wannan takarda, an bayyana cewa za a kyautata aikin ba da hidimar tara kudi a yankunan karkara. Sakamakon haka, wadanda za su koma yankunan karkara za su iya samun filaye a yankunan karkara ta hanyar harhadar kudi domin bunkasa sabon salon aikin gona." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China