in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta tara dalar Amurka kusan biliyan 22.2 domin aikin bada jin kai a shekarar 2017
2016-12-06 11:51:04 cri

A jiya Litinin, hukumar da abin ya shafa ta MDD ta fitar da wani shirin tattara kudi a duk fadin duniya a shekarar 2017 domin tunkarar matsalolin jin kai da za a fuskanta. Wannan shiri ya ce, yanzu duk duniya na fuskantar matsalar samar da jin kai mafi tsanani bayan yakin duniya na 2, wato yanzu mutane kusan miliyan 128 ne ke fama da wahalhalu sakamakon rikice-rikice da bala'u daga indallahi a fadin duniya. Sakamakon haka, yawan kudin jin kai da ake bukata a duk fadin duniya a shekarar ta 2017 mai zuwa ya kai dalar Amurka biliyan 22.2, wannan adadi ya kai wani sabon matsayi a tarihi, ya kuma alamta cewa, yanzu yanayin jin kai da ake ciki a duk duniya yana ta lalacewa. Game da wannan batu, ga rahoton da abokin aikinmu Sanusi ya hada mana.

A yayin taro game da wannan shiri da aka shirya a birnin Geneva a jiya Litinin, Mr. Stephen O'Brien, mataimakin babban sakataren MDD wanda ke kula da harkokin jin kai ya sanar da wannan shiri, inda ya ce, "Wannan shirin tara kudi na shekarar 2017 yana kunshe da karamin shiri na dogon lokaci, da kuma na karamin shiri na daidaita harkokin fama da batun, wanda zai shafi kasashe 33. Jimillar kudin da za a tara zai kai dalar Amurka biliyan 22.2. Wannan ne kudi mafi yawa da hukumomin MDD suke son tarawa, ya kuma alamta cewa, yanzu ana cikin yanayin jin kai mafi tsanani bayan yakin duniya na 2. Kashi 80 cikin 100 na matsalolin jin kai da ake fama da su sun samo asali ne sakamakon rikice-rikicen da aka haddasa su."

A cikin wani bayanin da ofishin daidaita harkokin jin kai na MDD ya fitar a Litinin, an ce, za a yi amfani da wadannan kudade ne wajen samarwa mutane wadanda suke zaune a kasashe 33, kuma suke cikin mawuyacin hali sakamakon rikice-rikice iri iri, da bala'o'i daga indallahi kayayyakin abinci, da wuraren kwana, da magunguna da kayayyakin tsaronsu da kuma ilimin tinkarar matsalolin da suke faruwa cikin gaggawa da sauran kayayyakin yau da kullum.

Wannan sanarwa ta nuna cewa, rikice-rikice dake faruwa a sanadiyyar amfani da nuna karfin tuwo da a kan yi a kai a kai su ne dalilai mafi muhimmanci da suke haddasa matsalolin jin kai. Yawan kudaden da za a yi amfani da su a wannan fanni zai kai kashi daya cikin uku. Daga cikin wadannan kudade, za a kebe wa kasar Sham dalar Amurka biliyan 3.4, kasar Yemen biliyan 1.9, kasar Sudan ta kudu biliyan 1.3, sannan za a kebe wa Najeriya wajen biliyan 1.

Dalilai daban da kan haddasa matsalolin jin kai shi su ne bala'o'i daga indallahi, kamar bala'in fari da ake samu sakamakon sauyin yanayin El-nino, da bala'in ambaliyar ruwa da dai sauransu, wadanda yanzu suke sanya mutane marasa galihu shiga mawuyacin hali matuka. A shekarar 2016, an samar da taimakon jin kai ga kasashe 22 wadanda suka samu bala'o'i daga indallahi masu tsanani. Sakamakon haka, an yi hasashen cewa, a shekarar 2017, wasu kasashe daga cikinsu, kamar Habasha, Somaliya, Haiti, wasu kasashe na kudancin nahiyar Afirka suna bukatar a cigaba da samar musu kayayyakin abinci da ruwan sha, da na'urorin tsabtar yanayin da suke da zama, da na'urorin likitanci.

Madam Kate Halff wadda ke shugabantar kwamitin mayar da martani ga shirin jin kai ta bayyana cewa, "Ba ma kawai matakin jin kai ne ke iya ceton rayukan mutane ba, har ma zai iya taimakawa mutane wadanda suke shan wahalhalu wajen samun karin damar kasancewarsu a duniya tare da martaba."

Amma, a hakika dai, ba a iya tattara kudin jin kai bisa shiri kamar yadda ake fata ba. Musamman, irin wannan hali ya yi tsanani sosai a shekarar 2016. Bisa kiddiddigar da aka bayar, an ce, ko da yake yawan kudin jin kai da ake son tattarawa a shekarar 2016 ya karu daga dalar Amurka biliyan 20.1 zuwa biliyan 22.1, amma ya zuwa yanzu, an samu rabinsu ne kawai, gibin dake kasancewa ya kai dalar Amurka biliyan 10.7. Mr. Stephen O'Brien ya nuna cewa, "Ya zuwa yanzu, yawan kudaden jin kai da muka samu ya kai dalar Amurka biliyan 11.4, wannan ne adadi mafi yawa a tarihi, amma rabi ne kawai bisa yawan kudaden da ake bukata. Mun godewa wadanda suka samar da wadannan kudade, muna kuma fatan za a iya ci gaba da yin kokarin samar da taimako domin cimma burinmu tare."

Bugu da kari, MDD ta kirayi a tsara wani shirin fama da matsalolin jin kai na dogon lokaci, ta yadda za a iya kawar da su gaba daya a duk duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China