in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ba da shawarwari kan batun ci gaban duniya
2016-12-05 18:57:03 cri

A yau Litinin ne a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin aka kammala taron musamman na yini 2 don tunawa da da 'Sanarwar 'yancin neman ci gaba' da aka zartar shekaru 30 da suka wuce. Wakilai fiye da 150 daga kasashe, yankuna da kungiyoyi fiye da 40 ne suka halarci taron.

Babban taken taron shi ne 'sanya kowa ya amfana da ci gaban kasa, ta yadda za a samar da karin moriya ga jama'ar kasashe daban daban'. Bisa wannan take ne, mahalartar taron suka tattauna sosai, tare da bullo da wasu shawarwari ga kasashen duniya.

A cewarsu, neman ci gaba hakki ne na kowa, kuma wani bangare ne na hakkin dan Adam. Wannan hakki, a cewar mahalartar taron, ya shafi daidaiku da baki dayan jama'a. Haka kuma, neman ci gaba mai dorewa babban nauyi ne da ya rataya a wuyan duk wata kasa. Sa'an nan ya kamata a yi kokarin tabbatar da hakkin neman ci gaban ko wacce al'umma, da hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban don taimakawa ga nasarar hakan.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China