in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin bincike na kasashen BRICS sun tattauna kan yadda za su yi hadin gwiwa wajen yaki da laifin cin rashawa
2016-12-02 11:45:49 cri

A jiya Alhamis 1 ga watan Disamba, an shirya wani taron shugabannin hukumomin gabatar da kararraki ga kotu na kasashen BRICS a birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. Shugabannin hukumomin gabatar da kararraki wadanda suka halarci taron sun tattauna kan yadda za su yi hadin gwiwa wajen yakar laifin cin hanci da rashawa bisa jigon taro na "dakile laifin cin hanci da rashawa domin tabbatar da bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma ba tare da wata tangarda ba". Sun bayyana cewa, za su yi kokarin kyautata dokokin yin hadin gwiwa, da kara yin musayar bayanai da kuma dawowar kudaden da aka sata, ta yadda za su iya yin rigakafi da kuma yaki da laifin cin hanci da rashawa da a kan yi a tsakanin kasa da kasa. Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi ya hada mana.

Bayan da ministocin kasashen BRICS, wato Sin, Brazil, Rasha da Indiya suka yi tattaunawa karo na farko a shekarar 2006, an shafe shekaru 10 ana hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS. A shekarar bara, hukumomin gabatar da kararraki na Sin da Rasha sun ba da shawarar kafa tsarin yin taron shugabannin hukumomin gabatar da kararraki na kasashen BRICS, ta yadda za a iya kyautata aikin yakar laifuffukan da aka aikata a tsakanin kasa da kasa domin tabbatar da ganin an bunkasa kasashe masu cigaban tattalin arziki tare.

A yayin taron shugabannin hukumomin gabatar da kararraki na BRICS da ake yi a birnin Sanya na kasar Sin, Mr. Cao Jianming, shugaban hukumar gabatar da kararraki na kasar Sin ya bayyana cewa, "Yaki da laifin cin hanci da rashawa domin kafa wani yanayin neman bunkasuwa mai armashi dake da adalci, kuma babu laifin cin hanci da rashawa, muhimmin aiki ne da ke wuyan hukumomin gabatar da kararraki na kasashen BRICS. An tabbatar da wannan jigo domin kasashen BRICS suna bukatar fama da kalubalolin neman bunkasa duk duniya baki daya da kuma bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummarsu. Sakamakon haka, za a iya kaddamar da hadin gwiwa irin ta a zo a gani tsakanin hukumomin gabatar da kararraki na kasashen BRICS."

Mr. Cao Jianming ya kuma nuna cewa, sabo da akwai bambancin matsayin tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma, musamman bambancin tsarin siyasa da dokoki da suke kasancewa a kasashe daban daban, ana da matsalar zurfafa yin hadin gwiwa wajen yakar laifin cin hanci da rashawa a tsakanin kasa da kasa. Ya kamata hukumomin gabatar da kararraki na kasashen BRICS su dogara da tsarin yakar laifin cin hanci da rashawa na G20, inda za su iya tattauna manyan ka'dojin yin hadin gwiwar yakar laifin cin hanci da rashawa da kuma fahimtar dokoki da al'adun shari'a na kasashe daban daban. Sabo da haka, Mr. Cao Jianming ya kara da cewa, "Ya kamata hukumomin gabatar da kararraki na kasashen BRICS su mayar da martani ga 'muhimman ka'idojin yin awon gaban masu cin hanci da rashawa' da 'shirin daukar matakan yakar cin hanci da rashawa' da aka zartas da su a yayin taron shugabannin kasashen G20 a inuwar 'yarjejeniyar yakar cin hanci da rashawa ta MDD', sannan su kara yin musayar bayanai da fasahohin yakar laifin cin hanci da rashawa da ma'aikatansu domin ciyar da yin hadin gwiwar yakar laifin cin hanci da rashawa tsakanin kasashen BRICS gaba."

A yayin taron, Mr. Vladimir Malinovsky, mataimakin shugaban hukumar gabatar da kararraki na kasar Rasha ya yaba da matakin "Ragar Sararin Sama" da kasar Sin ta dauka a shekarar bara domin farautar masu aikata laifin cin hanci da rashawa wadanda suka gudu zuwa ketare. Mr. Malinovsky ya ce, kasar Rasha ma tana yin kokarin dawowa da kudaden da aka sata kuma aka ajiye su a ketare, tana kuma kokarin kyautata dokokin shari'a da tsarin aiwatar da su. Mr. Malinovsky ya bayyana cewa, "Ya zuwa yanzu, an samu wasu kyakkyawan sakamako wajen yin hadin gwiwar yakar da laifin cin hanci da rashawa tsakanin kasa da kasa, kuma tsakanin yankuna daban daban. Amma har yanzu ana da bambancin ra'ayi kan yadda za a iya dawowa da kudaden da aka sata kuma aka ajiye su a ketare, ciki har da kudaden da masu cin hanci da rashawa suka sata. Sabo da haka, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta kara mai da hankali kan batun. A kasar Rasha, wasu hukumomin da abin ya shafa suna hadin gwiwa wajen kokarin dawowa da kudade da dukiyoyin da aka sata kuma aka ajiye su a ketare."

Bayan da aka yi musaya da kuma more ra'ayoyi daban daban, an tsai da kudurin cewa, za a yi taron shugabannin hukumomin gabatar da kararraki na kasashen BRICS na shekara mai zuwa a kasar Brazil. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China