in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya bukaci Korea ta Arewa da ta daina kera makaman nukiliya da makamai masu linzami
2016-12-01 12:11:16 cri

Jiya Laraba kwamitin sulhun MDD ya zartas da wani sabon kuduri game da kasar Korea ta Arewa, inda ya kai suka ga kasar saboda ta yi gwajin nukiliya a ranar 9 ga watan Satumban bana, kuma ya bukace ta da ta soke shirin kera makaman nukiliya da makamai masu linzami, kana ya tsai da kuduri cewa, zai sanya wani sabon takunkumi kan kasar.

Da safiyar jiya Laraba ranar 30 ga watan da ya gabata bisa agogon wurin, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lambar 2321, inda ya kai suka da kakkausar muriya ga kasar Korea ta Arewa da ta saba wa kudurin kwamitin sulhun MDD da abin ya shafa, kuma ta kasa kula da bukatun kasashen duniya, har ta gudanar da gwajin nukiliya sau da dama. Kwamitin sulhun ya sake jaddada cewa, wajibi ne Korea ta Arewa ta daina gudanar da daukacin ayyukan da suke da nasaba da shirin kera makamai masu linzami, ta soke shirin kera makaman nukiliya nan take ba tare da bata lokaci ba.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi maraba da wannan kuduri, inda ya bukaci kasar ta Korea ta Arewa da ta sauya matsayinta tun da wur wuri, kuma ta shiga shirin hana kera makaman nukiliya a zirin Korea, kana ya bayyana cewa, sanya takunkumi kan kasar ba dabara mafi dacewa ba ce, ya kamata a ci gaba da yin kokari ta hanyar yin shawarwarin siyasa, da haka za a daidaita batun cikin kwanciyar hankali. Ban Ki-moon yana mai cewa, "Ina maraba da kudurin da aka zartas, kuma ina farin ciki saboda ba wanda ya nuna rashin amincewa kudurin, ana iya cewa, kasashen duniya suna hada kai sosai kan batun tinkarar matsalar tsaro a zirin Korea, kuma suna son a cimma burin tabbatar da zaman lafiya a yankin. Wajibi ne Korea ta Arewa ta sauya matsayinta, kuma ta shiga shirin hana yaduwar makaman nukiliya a zirin Korea ta hanyar yin shawarwari, a nan bari in sake jaddada cewa, ina fatan Korea ta Arewa za ta yi wajababben kokari domin sassauta mawuyacin yanayin da zirin ke ciki. Sanya takunkumi na daya daga cikin dabaru da za su taimaka wajen tabbatar da zaman karko da zaman lafiya, har kullum muna nacewa ga hanyar yin shawarwarin siyasa domin warware matsalolin da ake fuskanta cikin kwanciyar hankali."

Bisa sabon kudurin da aka zartas, an kimmanta cewa, za a rage adadin cinikin waje na kasar ta Korea ta Arewa har zai kai kashi 25 cikin dari, kana kuma kudurin ya tanadi cewa, za a kayyade adadin kwal da kasar za ta fitar zuwa kasashen ketare, wato adadin ba zai zarta dalar Amurka miliyan 400 ba, lamarin da zai rage kudin shiga na kasar a fannin fitar da kwal zuwa kasashen ketare da kashi 60 cikin dari. Kana, kudurin shi ma ya tanadi cewa, za a hana Korea ta Arewa da ta fitar da wasu sinadarai kamar su tagulla da azurfa da dai sauransu zuwa kasashen ketare. Ban da haka kuma, kudurin ya tanadi cewa, za a kayyade ayyukan tawagogin wakilan diplomasiya na kasar a nan gaba.

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana cewa, Korea ta Arewa ta kasa kula da ra'ayin kiyayya da kasashen duniya suka nuna mata, ta yi gwajin nukiliya sau da dama, game da wannan, kasar Sin ita ma ta nuna adawa, a sa'i daya kuma, Liu Jieyi ya bukaci bangarori daban daban da abin ya shafa da su yi hakuri da juna, kuma su maido da shawarwarin dake tsakanin bangarori shida tun da wur wuri, saboda hakan zai taimaka wajen daidaita rikicin lami lafiya. Liu Jieyi yana mai cewa, "A ranar 9 ga watan Satumban bana, Korea ta Arewa ta yi biris da adawar kasashen duniya, ta sake gudanar da gwajin nukiliya, game da wannan, gwamnatin kasar Sin ta nuna kiyayya, yanzu kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri kan batun, hakan ya nuna cewa, kasashen duniya sun riga sun cimma matsaya daya kan batun."

Kana, Liu Jieyi ya jaddada cewa, kasar Sin ta nuna kiyayya ga kafa tsarin kakkabo makamai masu linzami THAAD a zirin Korea, saboda lamarin zai kawo illa ga zaman lafiya a yankin. Liu Jieyi ya bayyana cewa, "Sin makwabciyar kasa ce ta Korea ta Arewa, cikin dogon lokaci kasar ta Sin tana nace ga manufar hana kera makaman nukiliya a zirin Korea, tare kuma da kiyaye zaman lafiya a yankin. Kasar Sin ta na adawa sosai da shirin kafa tsarin THAAD a yankin, saboda lamarin zai kawo babbar illa ga moriyar kasar Sin, dama moriyar sauran kasashen dake yankin. Kasar Sin ta bukaci bangarorin da abin ya shafa da su daina gudanar da aikin nan take."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China