in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Saliyo na fatan kara yin hadin gwiwa da kasar Sin
2016-11-30 11:14:59 cri

Tun daga yau Laraba 30 ga watan Nuwamba zuwa ran 6 ga watan Disamba mai zuwa, shugaban kasar Saliyo Ernest Koroma zai fara ziyararsa a nan kasar Sin. Kafin ya tashi daga kasarsa, bi da bi ne shugaba Koroma da jakada Wu Peng na kasar Sin dake zaune a kasar Saliyo suka gana da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin dake kasar Saliyo.

A lokacin da yake ganawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua, da farko dai Mr. Koroma ya gode wa kasar Sin da ta tallafawa kasar Saliyo a lokacin da kasarsa take fama da cutar Ebola, kuma yana fatan kasarsa za ta ci gaba da kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban da kasar Sin.

Mr. Koroma ya bayyana cewa, kasar Sin ta dade tana kasancewa tamkar wata abokiyar arziki ta kasar Saliyo. A cikin shekaru 45 da suka gabata bayan kafa dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, kasar Sin ta samar da dimbin tallafi ga kasar Saliyo a fannonin samar da kayayyakin yau da kullum, da aikin gona, da aikin likitanci da kuma na ba da ilmi. Musamman a lokacin da cutar Ebola ta barke a kasar Saliyo, cikin sauri sosai kasar Sin riga sauran kasashen duniya ta samar wa kasar Saliyo magunguna da kayayyakin abinci da likitoci.

Sannan, Mr. Koroma ya bayyana cewa, dangantakar sada zumunta dake kasancewa tsakanin kasashen Saliyo da Sin a kullum ne take kasancewa bisa ka'idojin amincewa da kuma girmama wa juna a fannin siyasa. Sakamakon haka, wannan dangantaka ta kawo wa al'ummomin kasashen biyu moriyar abin a zo a gani. Kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a karin fannoni daban daban yana da muhimmanci matuka ga kasar Saliyo.

A ganin Mr. Koroma, ya kamata kasashen Saliyo da Sin su kara yin hadin gwiwa a fannonin cinikayya da zuba jari a nan gaba. Bugu da kari, kasashen biyu suna da damar yin hadin gwiwa a fannonin aikin gona da yawon shakatawa.

Dadin dadawa, Mr. Koroma ya ce, a cikin dimbin shekarun da suka gabata, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba sosai, har ma yanzu ta zama daya daga cikin kungiyoyin tattalin arziki mafi samun saurin bunkasa a duk duniya. Mr. Koroma yana fatan kasarsa za ta iya koyon fasahohin neman ci gaba da kasar Sin ta samu, yana kuma fatan kasarsa za ta iya yin amfani da salon kafa shiyyar musamman ta bunkasa tattalin arziki, ta yadda za a iya aiwatar da shirin sake gina kasarsa bayan cutar Ebola.

Bugu da kari, a kwanan baya, a lokacin da yake ganawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin a birnin Freetown na kasar Saliyo, Mr. Wu Peng, jakadan kasar Sin dake zaune a kasar Saliyo ya bayyana cewa, kasashen Sin da Saliyo za su kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban domin kokarin samun nasara tare da kuma moriyar juna.

Jakada Wu Peng ya nuna cewa, yanzu, kasar Sin tana neman damar zuba jari a ketare da yin hadin gwiwa da kasashen waje a lokacin da take aiwatar da shirin neman bunkasuwa a ketare. Kasar Saliyo kuma tana neman tallafi da taimakon kasashen duniya sabo da yanzu tana kokarin farfado da tattalin arzikinta da zaman al'ummarta bayan cutar Ebola. Sakamakon haka, hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen biyu, ba ma kawai zai kawo wa juna moriya ba, har ma zai iya karfafa dangantakar dake kasancewa tsakanin kasashen biyu. A nan gaba, kasar Sin za ta yi hadin gwiwa da bangaren kasar Saliyo a fannonin samar da makamashi, gina filin tashi da saukar jiragen sama, da tasoshin ruwa da shimfida hanyoyin mota da kuma samar da ruwan famfo.

Jakada Wu Peng ya jaddada cewa, kasashen Sin da Saliyo suna yin hadin gwiwa ne bisa ka'idar yin shawarwari cikin lumana, suna zaman daidai wa daida. Kasar Sin ba za ta tilasta kasar Saliyo da ta yi wani abun da ba ta so ba, kuma kasashen biyu suna yin hadin gwiwa ba tare da kowane sharadin siyasa ba. Wu Peng ya kara da cewa, kasar Sin ta dade tana bin ka'idoji biyar na zaman tare cikin lumana a lokacin da take kafa da kuma bunkasa dangantakar diflomasiyya da sauran kasashen duniya. Makomar kasar Saliyo tana cikin hannun gwamnati da al'ummar Saliyo, kasar Saliyo tana tsara manufofin neman bunkasuwa bisa hakikanin halin da kasar take ciki. Kasashen Sin da Saliyo za su ci gaba da kara yin hadin gwiwa tsakaninsu domin tabbatar da amincewa da juna da zumuncin da ke kasancewa a tsakaninsu da kuma neman nasara tare. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China