in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da intabiyu kan kamfanonin Sin a Afirka
2016-11-29 13:12:26 cri

Jiya Litinin bisa agogon wurin kasar Tanzaniya, aka kaddamar da intabiyu kan kamfanonin kasar Sin dake kasashen Afirka cikin hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labarai na kasar Sin da kasashen Afirka a Dares Salam, babban birnin kasar ta Tanzaniya, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ne ya jagoranci wannan aiki.

Tsakanin ranakun 28 ga wata da 4 ga wata mai zuwa, manema labarai sama da 40 da suka zo daga kafofin watsa labarai kusan 30 na kasar Sin da kasashen Afirka za su kai ziyara a kamfanonin ciniki da cibiyoyin nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin dake kasashen Tanzaniya da kuma Kenya domin zantawa da ma'aikatan dake aiki a wadannan wurare, inda kuma za su yi hira kan batutuwan dake shafar aikin zuba jari da kamfanonin kasar Sin suke yi a kasashen Afirka, da rawar da suke takawa a fannin cigaban wadannan kasashen, kana za su yi hira kan kokarin da suke domin kara karfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomin sassan biyu wato na Sin da kasashen Afirka, kazalika, za su tattauna kan batun da ya shafi kan yadda kamfanonin kasar Sin suke sa kaimi kan aikin yada manufofi da al'dun kasar Sin a nahiyar Afirka, tare kuma da samun babban sakamako wajen hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu.

Yayin bikin kaddamar da aikin, mataimakin ministan ma'aikatar yada manufar kasar Sin Sun Zhijun ya bayyana cewa, "Hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labarai zai sa kaimi kan fahimtar juna a tsakanin al'ummomin Sin da Afirka, shi ma zai ingiza hadin gwiwa da sada zumunta dake tsakanin sassan biyu. Makasudin shirya wannan aikin shi ne domin kara gano kokarin da kamfanonin kasar Sin suke yi a kasashen Afirka, tare kuma da nuna wa kasashen duniya, musammam ma kasashen Afirka babban sakamakon da aka samu a fannin hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirika. Ana iya cewa, hakan shi ma zai samar da damammaki ga al'ummar kasar Sin da su kara fahimtar kokarin da kamfanonin kasar Sin suke a Afirka. Ban da wannan kuma, ana sa ran aikin intabiyu kan kamfanonin Sin a Afirka cikin hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labarai na Sin da Afirka zai kara karfafa wa 'yan kasuwan kasar Sin kwarin gwiwa domin su kara zuba jari a kasashen Afirka, ta yadda za a kara zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki dake tsakanin Sin da Afirka yadda ya kamata."

Sun Zhijun shi ma ya gabatar da shawarwari guda uku game da yadda za a kara zurfafa hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labarai na Sin da Afirka. Yana mai cewa, "Zurfafa hadin gwiwa na moriyar juna tsakanin Sin da Afirka zai kawo babban tasiri ga tsarin siyasar duniya da kuma tsarin tattalin arzikin duniya, shi ma zai kawo tasiri ga ci gaban wayewar kai a tsarin ra'ayin bainal jama'a na duniya. Domin kara ciyar da aikin gaba, a nan ina son in gabatar da shawarwari guda uku, na farko, kara zurfafa zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka, na biyu, kara habaka hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labarai na sassan biyu, na uku, kamata ya yi kafofin watsa labarai na kasar Sin su yi kokari tare da takwaransu na kasashen Afirka domin samun ci gaba tare."

Ministan kula da watsa labarai da al'ada da fasaha da wasannin motsa jiki na kasar Tanzaniya Nape Nnauye shi ma ya halarci bikin, inda ya yi maraba da aikin, tare kuma da taya murna kansa, yana mai cewa, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasashen biyu wato Sin da Tanzaniya sun gudanar da huldar dake tsakaninsu yadda ya kamata, kamfanonin kasar Sin da yawan gaske suna zuba jari a kasar ta Tanzaniya, kana sun samar da tallafi a bangaren ilimi da fasahohi ga al'ummar kasar. Ana iya cewa, kafofin watsa labarai suna taka muhimmiyar rawa a fannin, saboda suna yada labaran da suke faruwa a nahiyarmu ta Afirka, Ina ganin cewa, manema labarai na kasar Sin za su sa kaimi kan yalwatuwar huldar abokantaka da ta hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka tare da takwaransu na kasashen Afirka."

Manema labaran kasar Sin da suke shiga wannan aiki sun zo ne daga manyan kafofin watsa labarai kamar su jaridar People's Daily, da kamfanin dillancin labarai na Xinhua da gidan talebijin na tsakiyar kasar Sin wato CCTV, da kamfanin watsa labarai na kasar Sin da dai sauransu, takwaransu na kasashen Afirka kuwa sun zo ne daga gidan rediyon kasar Tanzaniya, da jaridar The Guardian ta Tanzaniya, da gidan rediyon kasar Kenya, da jaridar Nation ta kasar Kenya da dai sauransu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China