in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun yaba shirin "ziri daya hanya daya" na kasar Sin
2016-11-28 12:49:41 cri

A kwanan baya, an kaddamar da taron shekara-shekara na tattalin arzikin kasar Sin da yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, kuma taron "sabon jirgin ruwa na Bashan" a nan Beijing. Babban jigon wannan taro shi ne, "manufofi da matakai kan hanyar siliki dake kan teku ta karnin 21". Masana wadanda suka halarci taron suna ganin cewa, shirin "ziri daya hanya daya" da ake aiwatarwa na samun ci gaba da karfi sosai, musamman a lokacin da ake yunkurin aiwatar da manufofin kare cinikayya da dakatar da shirin bunkasa duk duniya bai daya, shawarar aiwatar da "ziri daya hanya daya" ta kasar Sin na bayyana darajarta.

Yau da shekaru 31 da suka gabata, wasu masanan tattalin arziki na gida da na waje da wasu jami'an gwamnatin kasar Sin sun yi wani taro a cikin wani jirgin ruwa kirar Bashan dake shawagi a kogin Yangtse, inda suka shafe wajen mako daya suna taron da aka kira shi cewa, taro ne aka samu ilmin sauya salon bunkasa tattalin arziki bisa shirin gwamnati zuwa salon bunkasa tattalin arziki bisa bukatar da ake da ita a kasuwa. A shekarar da muke ciki, an sake kiran irin wannan taro, inda ake zura ido kan shawarar "ziri daya hanya daya". Mr. Cao Wenlian, direktan ofishin kula da harkokin yin hadin gwiwa da kasashen waje a kwamitin kula da harkokin yin gyare-gyare da ci gaba na kasar Sin ya bayyana cewa, "Ya zuwa, yawan kasashe da kungiyoyi da suka bayyana niyyarsu ta halartar shirin 'ziri daya hanya daya' ya kai fiye da 100. Gwamnatin kasarmu ta riga ta kai ga daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakaninta gwamnatocin kasashe 50. Sannan kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kasashe fiye da 20 a fannonin samar da makamashi tsakanin kasa da kasa. Sakamakon haka, shawarar bunkasa shirin ziri daya hanya daya tana samun bunkasuwa da karfi sosai."

Mr. Jaewoo Choo, shehun malamin dake nazarin manufofin diflomasiyya a jami'ar Kyung Hee ya kuma bayyana cewa, shawarar bunkasa shirin ziri daya hanya daya sabon karfi ne na yin hadin gwiwar tattalin arziki. Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa kasar Koriya ta kudu ta zama mambar Bankin zuba jari kan muhimman ayyukan yau da kullum. Mr. Jaewoo Choo ya ce, "Sauran shawarwarin da wasu kasashen dake yankin tsakiyar Asiya suka bayar, alal misali, kafa kawancen tattalin arziki tsakanin Turai da Asiya, ko shawarar kafa sabuwar hanyar siliki da dai sauransu, da kuma kasashen Rasha da Japan da Indiya da Amurka ma sun taba gabatar da irin wannan shawara. Idan za a iya hada su tare, shawarar bunkasa shiri ziri daya hanya daya da gwamnatin kasar Sint ta gabatar za ta iya cimma burinta na bunkasa bil Adama."

Amma wasu masana sun kuma bayyana damuwarsu a bayyane, cewar yanzu ana da matsaloli 6, ciki har da odar kasashen duniya ta yanzu, matsalar harhadar kudi dai sauransu wadanda suke kawo cikas ga aikin aiwatar da shirin ziri daya hanya daya. Mr. Liu Jianxing, mataimakin direktan ofishin kula da harkokin yin hadin gwiwa da kasashen waje a kwamitin kula da harkokin yin gyare-gyare da ci gaba na kasar Sin ya bayar da ra'ayinsa cewa, a lokacin da ake kokarin aiwatar da shirin ziri daya hanya daya, ya kamata a mai da hankali kan wasu muhimman yankuna, da muhimman kasashe da kuma muhimman ayyuka. Kada a mai da hankali kan kome da kome. Bugu da kari, Mr. Liu yana fatan a kafa hukumar neman ci gaban kasashen duniya a kasar Sin, yana mai cewa, "Muna fatan za a iya hanzarta kafa hukumar neman ci gaban kasashen duniya a nan kasar Sin, ta yadda za a iya yin amfani da hukumomin neman ci gaba na kasa da kasa, da kwararru, sannan za a iya daidaita wasu ayyukan a cikin gida da kuma a tsakanin kasa da kasa. Idan babu hukumar kwarai, ba za mu iya aiwatar da babban shirinmu kamar yadda ake fata ba."

A cikin nasa jawabi, Mr. Wang Yaohui, direktan wata hukumar ba da tunani ta kasar Sin ya ba da shawara cewa, kasashen dake bakin zirin daya hanya za su iya kafa wata kawancen "ziri daya hanya daya", ko fitar da ka'idojin aiwatar da shirin tare. Mr. Wang ya ce, "yanzu kasar Sin ta zama kasar dake dimbin tsofaffi. Amma kasashen Asean suna da isassun 'yan kwadago. Za a iya yin musayar albarkatun kwadago tsakanin Sin da su domin shigar da kwararru wadanda suke da fasahohin zamani da ilmi."

A lokacin da ake taron, masana sun nuna cewa, yanzu sassa daban saban suna nazarin dalilan da ya sa kasar Britaniya ta fito daga kungiyar EU, kuma sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, kasar Amurka za ta janye daga yarjejeniyar TPP. Har ma yanzu ana adawa da kokarin bunkasa duk duniya bai daya. Sakamakon haka, an gamu da matsalolin raguwar tattalin arziki, da karuwar gibin dake tsakanin masu arziki da marasa arziki. Ana fatan shirin bunakasa ziri daya hanya daya zai iya taka rawa wajen warware wadannan matsaloli. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China