in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin bukatar neman samun ikon mallakar fasaha a Sin a bara ya kai sahun gaba a duniya
2016-11-24 11:13:56 cri

Jiya Laraba hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta kasashen duniya ta fitar da wani rahoto game da gabatar da bukatar neman samun ikon mallakar fasaha a kasashen duniya a shekarar 2015, inda aka bayyana cewa, gaba daya kwatankwacin adadin bukatar samun ikon mallakar fasahar kera kayayyaki da masu aikin kirkire-kirkire suka gabatar a fadin duniya a bara ya kai kusan miliyan 2 da dubu 900, adadin da ya karu da kashi 7.8 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2014, daga cikin adadin, na kasar Sin ya fi yawa, kuma wannan ne karon farko da adadin ya zarta miliyan 1 a cikin shekara daya, har ya kai sahun gaba a duniya.

Rahoton game da adadin neman samun ikon mallakar fasaha a kasashen duniya, rahoto ne da hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta duniya take fitarwa sau guda a kowace shekara, inda ake yin kididdiga kan adadin bukatar da ake gabatarwa domin samun ikon mallakar fasaha, da kuma yin bincike kan sakamakon da aka samu a fannin. Irin ikon mallakar fasahar da muke tattauna a nan ya hada da fannoni uku, wato ikon mallakar fasahar kera kayayyaki, da ikon lambar shaidar mallakar fasaha, da kuma ikon mallakar zane-zanen siffar kayan masana'antu. Rahoton ya nuna cewa, gaba daya adadin bukatar mallakar fasahar kera kayayyakin da aka gabatar a bara ya kai miliyan 2 da dubu 900, adadin da ya karu da kashi 7.8 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2014, kana adadin neman samun ikon lambobin shaidar mallakar fasaha a bara ya kai miliyan 6, adadin da ya karu da kashi 15.3 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2014, kazalika, adadin neman samun ikon mallakar zane-zanen siffofin kayayyakin masana'antu shi ma ya karu da kashi 2.3 cikin dari, wato ya kai sama da dubu 870.

Babban jami'in hukumar kula da ikon mallakar fasaha ta duniya Francis Gurry, ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, amma adadin neman samun ikon mallakar fasaha a fadin duniya ya karu cikin sauri, dalilin da ya sa hakan shi ne domin adadin da aka samu a kasar Sin ya karu zuwa babban mataki. A yayin taron ganawa da manema labaran da aka gudanar a Geneva, a lokuta da dama Gurry yana yabawa kasar Sin, inda ya bayyana cewa, sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin ya ba su mamaki, saboda a karo na farko ne adadin bukatar neman samun ikon mallakar fasaha da aka gabatar a wata kasa a cikin shekara guda ya zarta miliyan 1, lallai kasar Sin ta ba su matukar mamaki, kuma abu mafi muhimmanci shi ne adadin yana karuwa cikin sauri.

Gurry ya ci gaba da cewa, yanzu gwamnatocin kasashen duniya suna kokarin raya tattalin arziki, shi ya sa aka samu babban ci gaba a fannin neman samun ikon mallakar fasaha a bara, saboda yawancin kasashen duniya suna amfani da sabbin fasahohi, hakan shi ma ya nuna cewa, kasashen duniya suna kara ba da muhimmanci kan sabbin fasahohi.

Rahoton ya nuna cewa, a fannin neman samun ikon mallakar kera kayayyaki, kasar Sin tana sahun gaba a duniya a bara bisa adadinta na miliyan 1, kana kasar Amurka ta kai matsayi na biyu da adadin sama da dubu 520, daga baya, kasar Japan ta kai na uku bisa adadinta na dubu 450.

Idan aka kidayar adadin ikon mallakar fasahar kera kayayyaki bisa tushen GDP na wata kasa, to, yanayin zai sauya, tun daga shekarar 2004, har kullum kasar Korea ta Kudu ta kai sahun gaba a duniya, a bayan ta kuwa, sai su ne Japan da Sin. Amma karuwar adadin na Sin ya fi sauri ne a shekarar 2005, adadin Sin ya kai kusan 1200 kawai, amma ya zuwa shekarar 2015, adadin ya kai fiye da 5200.

Daga fannonin da aka gabatar da bukatar, ana iya fahimta cewa, adadin bukatar samun ikon mallakar fasaha a fannin na'ura mai kwakwalwa ya fi yawa har ya kai kashi 7.9 cikin dari, daga baya, adadin a fannin injunan lantarki da kuma iskar gas ya kai matsayi na biyu da kashi 7.3 cikin dari. A fannin fasahar sadarwa ta zamani kuma, adadin ya kai kashi 4.9 cikin dari. A kasashen Sin da Japan da kuma Korea ta Kudu, an fi mai da hankali kan fannin injunan lantarki da iskar gas, a kasashen Faransa da Jamus kuwa, an fi mai da hankai kan fannin sufuri, game da kasashen Amurka da Canada kuma, an fi mai da hankali kan fasaha game da na'ura mai kwakwalwa, kana kasar Rasha ta fi mai hankali kan fasahar sarrafa abinci da albarkatun man fetur.

A bara, gaba daya adadin bukatar neman samun ikon lambar shaidar mallakar fasaha a duniya ya kai miliyan 6, a ciki, adadin na kasar Sin ya kai miliyan 2 da dubu 830, kana adadin rokon mallakar zane-zanen siffar kayan masana'antu ya kai dubu 870, yawancinsu suna da nasaba da kayayyakin da ake amfani da su a cikin gida da tufafi da kuma kayayyakin da ake amfani da su domin kintsa abubuwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China