in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Japan ta nuna rashin jin dadi saboda Trump ya ce Amurka za ta fice daga TPP
2016-11-23 13:08:58 cri

Kwanan baya, bayan da aka zabi Donald Trump da ya kasance sabon shugaban kasar Amurka sai ya bayyana cewa, Amurka za ta fice daga yarjejeniyar huldar abokantaka tsakanin kasashen dake bakin tekun Pasifik wato TPP, za ta kuma yi kokarin neman samun irin wasu shawarwarin ciniki dake tsakanin sassa biyu wadanda za su fi dacewa da moriyar kasar ta Amurka. Sai dai da alama wannan matakin na Trump, bai yiwa gwamnatin kasar Japan dadi ba.

Ranar 21 ga wata, agogon kasar Agentina, firayin ministan kasar Japan Shinzo Abe, wanda ke yin ziyarar aiki a kasar ya sake bukatar kasar Amurka da ta kammala ayyukan da suke shafar amincewa da yarjejeniyar TPP tun da wur wuri, Shinzo Abe ya bayyana cewa, "Idan kasar Amurka ta fice daga yarjejeniyar TPP, to hakan yarjejeniyar ba ta da ma'ana ko kadan, ana iya cewa, ya zama tamkar za a sake gudanar da shawarwarin, lamarin da zai lahanta babbar moriyar daukacin kasashen da suka shiga yarjejeniyar."

Yawancin kafofin watsa labarai na Japan suna ganin cewa, tun bayan da Trump ya yi nasara a babban zaben Amurka, nan take Shinzo Abe ya yi wata ganawa da shugaban Amurka mai jiran gado, haka kuma gwamnatin Japan ta bayyana cewa, shawarwarin dake tsakanin su ya samu babban sakamako, shi ya sa ana sa ran Trump zai sauya matsayin da ya dauka a baya, wato kin amincewa da yarjejeniyar TPP, har zai bukaci majalisar dokokin kasarsa da ta amince da yarjejeniyar cikin sauri.

Amma yanzu awa guda akwai bayan da Abe ya bayyana hakan, sai Trump ya gabatar da wani jawabi ta yanar gizo, jawabin da ya rushe mafarkin gwamnati da kafofin watsa labarai na kasar Japan. Trump yana mai cewa, "Ina son sanar da kasashe daban daban cewa, za mu fice daga yarjejeniyar TPP saboda kila ne za ta kawo babbar illa ga kasar Amurka, a maimakon haka, za mu ci gaba da yin kokari domin neman samun damammakin daddale yarjejeniyar ciniki dake tsakanin sassa biyu da kasashe daban daban, ta yadda za mu cimma burin kara bunkasa masana'antu a kasarmu, tare kuma da kara samar da guraben aikin yi ga al'ummar kasar ta Amurka"

Jawabin na Trump ya tayar da hankalin manema labarai na Japan, har wasu shahararrun manema labarai suka gabatar da tambayoyi a cikin shirye-shiryensu a gidajen talebijin, inda suka gabatar da shakkunsu cewa, mene ne wadannan shugabannin biyu suka tattauna a yayin da suke ganawa? A daidai wannan lokaci, Shinzo Abe yana cikin jirgin sama daga Agentina zuwa Japan, shi ya sa bai bayyana ra'ayinsa kan wannan batu cikin lokaci ba. A karkashin irin wannan hali, babban sakataren gwamnatin kasar Yoshihide Suga ya bayyana cewa, "A halin da ake ciki yanzu, Trump shi ne shugaba mai jiran gado, lokaci bai yi ba da gwamnatin Japan ta yi sharhi kan jawabin da ya bayar, game da manufofin da zai aiwatar bayan da ya hau kan kujerar shugaban kasar Amurka, mu ma ba mu son yin sharhi yanzu. A saboda haka ina son in bayyana cewa, a yayin taron kolin kungiyar APEC da aka gudanar kwanan baya, an gudanar da wasu shawarwarin a tsakanin shugabannin kasashen mambobin kungiyar game da yarjejeniyar TPP, inda gwamnatin Amurka ta bayyana cewa, za ta ci gaba da shawo kan al'ummar kasar domin su kara fahimtar muhimmancin TPP. Yanzu sabon shugaban zai rike mulkin kasar Amurka, shi ya sa kamata Japan ta kara taka rawa kan wannan batu, nan gaba Japan za ta ci gaba da kokarin zawarcin Amurka da sauran kasashe da su amince da yarjejeniyar TPP cikin sauri."

Shahararren mai yin sharhi kan al'amuran kasashen duniya na Japan Kenji Goto, yana ganin cewa, sanarwar fice daga TPP da Trump ya bayar ta kawo babbar illa ga mulkin Abe. Yana mai cewa, "Jawabin Trump game da TPP ya kawo babbar illa ga gwamnatin Japan, haka kuma ya kawo babbar illa ga mulkin Abe, ko shakka babu Trump zai fitar da Amurka daga TPP bayan da ya fara mulki a kasar. Nan gaba kuma idan ana son maido da Amurka cikin yarjejeniyar, tabbas ne Trump zai gabatar da wasu sharudan da ba zai yiwu ba a amince da su, Ana iya cewa, gwamnatin Abe za ta gamu da wahala."

Masu bincike kan al'amuran kasa da kasa suna ganin cewa, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, wato tun bayan da aka zabi Trump da ya kasance sabon shugaban Amurka, da kuma jawabin da ya yi na ficewar kasar daga TPP, gwamnatin Japan ta shiga mawuyacin hali, saboda Abe ba ya so ya fuskanci sauye-sauyen duniya kafin ya tsai da kuduri, idan Abe ba zai canja tunaninsa, to, da kyar Japan ta kubutar da kanta daga mawuyacin halin da take ciki.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China