in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara zuba jari don raya harkokin kiwon lafiya
2016-11-22 12:49:37 cri

An kaddamar da babban taron inganta harkokin kiwon lafiya na duniya karo na 9 a birnin Shanghai na kasar Sin a jiya Litinin, kuma za a kammala shi a ranar Alhamis. Taken taron shi ne "Raya aikin kiwon lafiya yayin da ake samun ci gaba mai dorewa: kowa na da lafiyar jiki, kome ake yi shi ne domin kiwon lafiya".

A yayin kaddamar da taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi jawabi inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana tsayawa kan manufar raya aikin kiwon lafiya ka'in da na'in. Tun kafuwar sabuwar kasar Sin, duk da cewa ba a samu ci gaban tattalin arziki sosai a lokacin ba, amma ta yi kokarin raya aikin kiwon lafiya da harhada magunguna, gami da kyautata lafiyar jama'arta sosai. A cewarsa,

"Mun kafa wani cikakken tsarin inshora a fannin kiwon lafiya, wanda ya shafi dukkan al'ummar kasar da yawansu ya kai fiye da biliyan 1.3. Yanzu matsakaicin tsawon rayukan Sinawa ya kai fiye da shekaru 76, kana yawan mutuwar mata masu juna biyu da matan dake mutuwa a loakcin haihuwa ya ragu zuwa kimanin mutane 20 cikin dubu 100, yayin da yawan mutuwar jarirai shima ya ragu zuwa jarira 8 cikin dubu. Idan aka lura da wadannan alkaluma za a ga har sun fi na wasu kasashe da ke da sukuni. Wannan wani ci gaba ne da ba za a iya samunsa cikin sauki ba, a wata kasa mai tasowa, wadda yawan al'ummarta ya zarta biliyan 1.3."

A cewar firaministan kasar Sin, kasar ta sanar da wani tsari mai taken "shirin kasar Sin game da cigaban aikin kiwon lafiya nan da shekarar 2030", da nufin samun wani tsarin kiwon lafiya mai inganci sosai, wanda zai shafi sassa daban daban na rayuwar mutane, kuma zai samar da matsakaicin tsawon rayuwar Sinawa ya kai shekaru 79, da sanya ma'aunin aikin kiwon lafiya na kasar ya kai matsayin kasashe masu cikakken sukuni, nan da shekarar 2030. Don cimma wannan buri, kasar Sin za ta yi kokarin kyautata wasu fannoni, in ji firaministan,

"Bangaren da bai samu ci gaba sosai ba, dangane da aikin kiwon lafiya a kasar Sin, ya shafi kauyuka da yankuna masu fama da kangin talauci. Za mu yi amfani da manufar raya yankin karkara, don kara zuba kudi ga aikin kiwon lafiya a kauyuka. Za mu horar da likitoci, da raya shirin ganin likita ta hanyar Intanet, da kara ba da tallafi ga wasu wurare, ta yadda za a daidaita aikin kiwon lafiya a kauyuka. Haka zalika, za mu taimakawa aikin samar da magungunan gargajiya, da kara tallafawa wurare masu fama da kangin talauci, ta yadda za a samu damar rage gibin da ake samu tsakanin birane da kauyuka."

Ban da wannan kuma, firaministan kasar Sin ya ce, kasarsa ta dade tana taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, a kokarin raya aikin kiwon lafiya. Ya ce,

"Cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce, mun tura likitoci fiye da dubu 20 zuwa kasashe da yankuna 67, inda suka yi kokarin kulawa da majiyyata fiye da miliyan 260. Bayan bullar annobar Ebola a wasu kasashen dake yammacin Afirka a shekarar 2014, nan take kasar Sin ta aike da likitoci fiye da 1200 zuwa kasashen, inda suka yi kokari tare da jama'ar kasashen don bada kulawa ga wadanda suka kamu da cutar, inda ta ba da gudummawa wajen dakile yaduwar cutar. Ganin yadda hukumar lafiya ta duniya wato WHO take taka muhimmiyar rawa a kokarin hana yaduwar cututtuka, da daidaita al'amuran kiwon lafiya a duniya, kasar Sin tana nuna mata babban yabo, kuma tana son aiki a karkashin tsarin MDD da na kungiyar WHO, don samar da tallafi gwargwadon karfinta ga kasashe dake tasowa."

Duk a wajen taron kaddamarwa, shugabar hukumar WHO,Margaret Chan Fung Fu-chun, ta yabawa matakan da kasar Sin ta dauka, gami da yadda take kulawa da lafiyar dukkan al'ummar kasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China