in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin Xi Jinping a taron shugbannin masana'antu da kasuwancin APEC ya sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki a shiyyar
2016-11-21 12:15:46 cri

A ranar 19 ga wata, aka gudanar da taron shugabannin masana'antu da kasuwancin APEC, kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen Asiya da tekun Pasifik na shekarar 2016 a Lima, babban birnin kasar Peru, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi mai taken "kara zurfafa huldar abokantaka, da kuma kara karfafa ci gaba."

A cikin jawabin da ya yi, shugaba Xi ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen dake shiyyar su taka rawa wajen farfado da kuma ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya, kana shugaba Xi ya gabatar da shawarwari guda hudu game da batun.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ya kamata a kara ingiza aikin gina yankin ciniki maras shinge a shiyyar Asiya da tekun Pasifik domin tsara wani shirin tattalin arziki irin na bude kofa a shiyyar. To, ta yaya za a fahimci shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar mana? Wane irin sauyi ne da yunkurin kafa yankin ciniki maras shinge a shiyyar zai kawo wa ci gaban tattalin arziki a shiyyar? Ko kuma wane irin yanayin huldar dake tsakanin kasar Sin da kungiyar APEC ke cike a halin yanzu? Game da wannan, wakilinmu ya yi hira da mataimakin shugaban cibiyar nazarin batutuwan kasashen duniya ta kasar Sin Ruan Zongze.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwari guda hudu game da yadda kasashen dake shiyyar Asiya da tekun Pasifik za su taka rawa wajen farfado da tattalin arziki a fadin duniya, wadannan shawarwari sun shafi fannoni hudu, na farko, kara habaka dungulewar tattalin arziki, tare kuma da tabbatar da tsarin tattalin arziki ba tare da rufa-rufa ba, na biyu, kara karfafa cudanyar dake tsakanin kasashen shiyyar domin samun ci gaba tare, na uku, sa kaimi kan kwaskwarima da kirkire-kirkire domin kara karfafa karfin kawo albarka, na hudu, sa kaimi kan hadin gwiwa domin cimma burin samun dauwamammen ci gaba a shiyyar.

Mataimakin shugaban cibiyar nazarin batutuwan kasashen duniya ta kasar Sin Ruan Zongze ya bayyana cewa, ra'ayin da shugaba Xi ya nuna game da tabbatar da dungulewar tattalin arziki da kuma tsara tsarin tattalin arziki ba tare da rufa-rufa ba yana da babbar ma'ana yayin da ake kokarin raya tattalin arzikin duniya. Yana mai cewa, "A halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin kasashen duniya bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, kuma wasu kasashen nahiyoyin Turai da Amurka suna kafa shinge wajen ciniki, a karkashin irin wannan hali, shugaba Xi ya gabatar da shawara game da kara habaka dungulewar tattalin arziki, tare kuma da tsara tsarin tattalin arziki ba tare da rufa-rufa ba, ana iya cewa, yana da babbar ma'ana, dalilin da ya sa haka shi ne domin wasu kasashe ba su so su yi hadin gwiwa da sauran kasashe, hakan ya kawo illa ga bunkasuwar tattalin arziki a fadin duniya. Kana shugaba Xi ya ce, ya kamata a kara karfafa cudanyar dake tsakanin kasashen shiyyar domin samun ci gaba tare, a yayin taron APEC da aka gudanar a birnin Beijing a shekarar 2014, aka taba bullo da irin wannan shiri, sai yanzu za a ci gaba da aiwatar da wannan babban shiri, ban da wannan kuma, ra'ayin game da kara yin kwaskwarima da kirkire-kirkire shi ma yana da nasaba da ra'ayin da shugaba Xi ya gabatar a yayin taron kolin G20 da aka shirya a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang na kasar Sin a watan Satumban bana. Kazalika abu mafi muhimmanci shi ne kara hadin gwiwa domin samun ci gaba tare, idan ana son cimma burin nan, wajibi ne a kafa wata huldar abokantaka tsakanin kasa da kasa. Ana iya cewa, shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar a fannoni hudu sun sa kaimi mai karfi kan ci gaban tattalin arziki a nan gaba."

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya sake jaddada matsayin kasar Sin na kafa yankin ciniki maras shinge a shiyyar Asiya da tekun Pasifik, Ruan Zongze yana ganin cewa, ci gaban kasashen Asiya da tekun Pasifik yana da muhimmanci ga ci gaban kasashen fadin duniya, kuma ci gaban kasar Sin yana da muhimmanci ga ci gaban shiyyar Asiya da tekun Pasifik. Yana mai cewa, "Da farko dai, shiyyar Asiya da tekun Pasifk tana da muhimmanci, ci gaban shiyyar zai kawo tasiri ga ci gaban duk fadin duniya, a saboda haka, kamata ya yi a kafa yankin ciniki maras shinge domin ba da jagoranci ga sauran kasashe, ta yadda za a samu ci gaban tattalin arziki a fadin duniya. Kana game da kasar Sin, ko shakka babu ci gaban kasar Sin yana da nasaba da ci gaban shiyyar da kuma duk fadin duniya baki daya, shi ya sa yana da muhummanci matuka."

Shugaba Xi ya ce, ci gaban kasar Sin zai samar da damammaki ga kasashen dake Asiya da tekun Pasifik domin su samu moriya daya, kana shekarar bana ita ce ta cikon shekaru 25 da kasar Sin ta shiga kungiyar APEC, kan batun game da tasirin da ci gaban kasar Sin zai kawo wa ci gaban shiyyar, Ruan Zongze ya bayyana cewa, "Ana iya gano tasirin daga fannoni biyu, na farko, wajen tunanin tsara shirin tattalin arziki ba tare da rufa-rufa ba, na biyu, wajen daukan matakai, misali, shirin ziri daya da hanya daya ya zama abin koyi da jagoranci ga sauran kasashe a shiyyar."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China