in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babbar jami'ar kasar Sin da ake zarginta da laifin cin hanci ta mika kanta ga 'yan sandan kasar
2016-11-17 13:37:19 cri

A jiya Laraba ne, Madam Yang Xiuzhu, tsohuwar babbar jami'a mai kula da aikin gini ta lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, wadda ake zarginta da cin hanci da karbar rashawa, ta koma kasar Sin daga kasar Amurka don mika kanta ga 'yan sanda, bayan ta shafe shekaru 13 tana buya a kasashen waje.

Yang Xiuzhu tana kan gaba ta fuskar matsayi cikin jerin sunayen tsaffin manyan jami'an kasar Sin da ake cigiyarsu, saboda zargin aikata laifuka, sa'an nan suka gudu zuwa kasashen waje. Dawo da ita nan kasar Sin wani babban ci gaba ne a hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Amurka a kokarin dakile cin hanci da rashawa.

A jiya Laraba, da karfe 3 na yamma agogon Sin ne wani jirgin sama da ya taso daga birnin Dallas na kasar Amurka ya sauka a filin saukar jiragen sama na birnin Beijing, dauke da Yang Xiuzhu, tsohuwar babbar jami'ar kasar Sin da ake zirginta da laifin cin hanci, wadda aka dade ana nemanta ruwa a jallo, ta fito daga jirgin tare da rakiyar wasu 'yan sanda mata 2. Daga bisani, wani ma'aikacin hukumar gabatar da kararraki ta lardin Zhejiang ya sanar da umarnin kotu na kama Yang Xiuzhu.

Ma'aikacin ya nuna wa Madam Yang Xiuzhu sammacin kotu, daga baya Yang ta ce ta ga sammacin. Daga bisani kuma ta sanya hannu a kai. Bisa wannan mataki, an kawo karshen gudun da Yang ta yi, inda ta kwashe shekaru 13, a kasashe 6.

Yang, wadda aka haife ta a shekarar 1946, ta taba rike mukaman mataimakiyar magajin birnin Wenzhou, da maitaimakiyar shugaban hukumar gine-gine ta lardin Zhejiang. A lokacin da take rike da wadannan mukamai, saurin ci gaban wuraren da suka kasance karkashin ikonta, ya ba ta damar lakume makudan kudi, wanda yawansa ya kai kudin Sin Yuan miliyan 253. Sakamakon tsoron fuskantar shari'a, a watan Afrilu na shekarar 2003, Yang ya arce zuwa ketare, inda ta buya a kasashen Singapore, Italiya, Faransa, Holland, Canada, gami da Amurka.

A shekarar 2014, kasar Sin ta kaddamar da cigiyar mutanen da suka gudu zuwa kasashen waje, inda aka tsaurara matakan neman kama Yang Xiuzhu. A nata bangare, Yang, wadda ta gudu kasar Amurka, ta taba rokon gwamnatin kasar don neman samun kariya bisa dalilai na siyasa a shekarar 2014. Sai dai zuwa lokacin kasashen Sin da Amurka sun riga sun fara kokarin hadin kai, musamman ma ta bangaren dakile cin hanci da rashawa. Karkashin wannan tsari ne, aka kara mayar da hankali wajen neman kafa Yang Xiuzhu, har ma aka kwace kadarorinta, da kuma dawo da kudin da ta sata zuwa kasar Sin.

Cai Wei, mataimakin shugaban sashi mai kula da hadin gwiwa da kasashen waje na kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya yi bayani kan yanayin da Yang take ciki a lokacin, ya ce,

"Bayan da ta gudu zuwa Amurka a shekarar 2014, bisa hadin gwiwar da ake yi tsakanin bangarorin Sin da Amurka, nan da nan aka gano wurin da take buye, kuma an tsare ta bisa bukatar kasar Sin. Saboda haka, lokacin da take kasar Amurka, ba ta da 'yanci, kuma ta fuskanci matsalar rayuwa."

Matakan da Sin da Amurka suka dauka, a yunkurin dakile cin hanci da rashawa, sun sa Yang Xiuzhu ta yi watsi da aniyyarta ta farko, wai "ko mutuwa za ta yi, za ta mutu a kasar Amurka". Ta yi nadama, ta bukaci a dawo da ita kasar Sin inda za ta mika kai ga 'yan sanda.

Dangane da yadda ta sauya aniyyarta, Zhuang Deshui, mataimakin darektan cibiyar nazarin aikin dakile cin hanci da rashawa ta jami'ar Peking ta kasar Sin, ya ce,

"Lokacin da aka fara lura da batun, za a ce Yang ta mika kai ne bisa radin kanta, amma a hakika, kokarin da bangarorin Sin da Amurka suka yi tare ne ya sa hakan ya tabbata. Bisa bayanan da kasar Sin ta mika mata, kasar Amurka ta taimakawa fannin shari'a sosai, wanda ya kunshi kama wannan mata, da kokarin gurfanar da ita a gaban kotu. Wannan yana nuna cewa, irin hadin gwiwar da ake yi tsakanin bangarorin 2 ya yi amfani."

Ya zuwa watan Satumba na shekarar 2016, kasar Sin ta yi nasarar dawo da wasu mutane 2210 wadanda suka gudu zuwa kasashe fiye da 70 don magance fuskantar shari'a gida.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China