in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da taron TWAS karo na 27 a Ruwanda
2016-11-15 13:39:41 cri

A jiya Litinin 14 ga wata ne aka kaddamar da babban taron kwararru a fannin kimiyya, na kungiyar nazari kan kimiyya ta kasashe masu tasowa ko TWAS karo na 27 a birnin Kigali, fadar mulkin kasar Ruwanda, taron da ya zamo na biyu na kungiyar a nahiyar Afirka, tun bayan da aka gudanar da irin sa na farko a kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2009.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya halarci bikin bude taron, inda ya gabatar da jawabi. Kaza lika shugaban cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin Bai Chunli, ya bai wa fitattun masana kimiyya lambobin yabo iri daban daban, a matsayinsa na shugaban kungiyar TWAS wato kungiyar manazarta kimiyya ta kasashe masu tasowa.

Yayin bikin bude taron, shugaba Kagame ya yi maraba da zuwan masanan na kasashe daban daban, yana mai cewa, "A kasashe masu tasowa, kimiyya da fasaha suna taka muhimmiyar rawa, wajen sauya tsarin tattalin arziki, da kuma rage ratar dake tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaba. Kungiyar masu nazarin kimiyya ta kasashe masu tasowa, ta ba da babbar gudumawa wajen samar da manyan gine-ginen more rayuwar jama'a, da kuma kwararru a wannan fanni. Haka kuma tana kokari domin kara kyautata hadin gwiwa tsakanin masana kimiyya da jami'an gwamnatocin kasashe. Banda wannan kuma, ta nuna mana cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa yana kara karfafa sannu a hankali."

A nasa bangare, shugaban cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin Bai Chunli, ya gabatar da wani jawabi, inda ya yaba wa shugaba Kagame, bisa jagorancin taron kungiyar TWAS da ya yi a kasarsa. Hakan ya nuna irin basira da hangen nesa na shugaban. Bai Chunli ya gaya wa manema labarai cewa, abu mafi muhimmanci yayin da ake gudanar da hadin gwiwa tsakanin kungiyar TWAS da kasashen Afirka shi ne, horas da kwararru a fannin kimiyya a nahiyar ta Afirka. Yana mai cewa, "Kwararru suna da muhimmanci. A halin da ake ciki yanzu, ana fama da matsalar karancin kwararru a kasashe masu tasowa, musamman ma a kasashen Afirka. Alal misali, malaman makaranta, da masana kimiyya, da injiniyoyi da dai sauransu. Don haka ya kamata a kara maida hankali kan aikin horas da kwararru. Kungiyar TWAS tana fatan za ta kara karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka domin horas da kwararru."

Bisa alkaluman da aka fitar, an ce kawo yanzu, masana kimiyya matasa sama da 1000 ne suka samu digirin koli, ta hanyar samun damammakin da kungiyar TWAS ta samar musu. Bai Chunli ya bayyana cewa, samar da dammamakin karatu a jami'o'i ga masana kimiyya matasa na kasashe masu tasowa, shi ne miuhimmin matakin da kungiyar ta dauka, yayin da take kokarin kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa. Yana mai cewa, "A hakika dai, kasashen Afirka sun samu ci gaba cikin sauri a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kana kasashe masu tasowa suna kara mai da hankali kan kimiyya da fasaha, kuma suna kara zuba jari kan kan aikin nazarin kimiyya da fasaha, da kuma aikin horas da kwararru. Ban da wannan kuma, kungiyar TWAS ta kan samar da tallafin kudi ga kasashen Afirka domin horas da kwararru, hakan ba ma kawai zai daga matsayin ilmi na kasashen ba ne, har ma zai samar da damammaki ga kwararrun domin su ba da gudumawa wajen gina kasashensu."

Yayin taron, Bai Chunli da ministan kula da aikin ba da ilmi na kasar Ruwanda Papias Musafiri, sun ba da lambobin yabo ga kwararrun masana kimiyya da dama. Kuma a madadin kungiyar TWAS, sun mika wa shugaba Kagame lambar yabo ta kungiyar, bisa muhimmiyar rawar da ya taka wajen cimma burin samun dauwamammen ci gaba a kasar ta Ruwanda, dama kasashen Afirka baki daya, ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasahohin zamani da kuma kirkire-kirkire.

Yayin taron da ake gudanarwa a Kigali, za a sanar da kafa tsarin masana kimiyya matasa na kungiyar TWAS, wanda zai samun tallafin kudi daga rukunin Legend na kasar Sin, domin nuna goyon baya ga hadin gwiwa dake tsakanin masana kimiyya matasa.

An kafa kungiyar TWAS mai hedkwatarta a Trieste dake kasar Italiya ne a watan Nuwamban shekarar 1983, makasudin kafuwarta shi ne samar da goyon baya, tare da sa kaimi kan nazarin kimiyya a kasashe masu tasowa. Shugaban cibiyar nazari kan kimiyya ta kasar Sin Bai Chunli ya hau karagar mulkin kungiyar a watan Janairun shekarar 2013, ya kuma yi nasarar rike wannan mukami a shekarar 2015.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China