in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Layin dogo a tsakanin Abuja da Kaduna ya zamo tamkar sanya danba ga burin raya zirga zirgar jiragen kasa a nahiyar Afirka
2016-11-14 13:37:51 cri

A ranar 26 ga watan Yulin bana ne, aka fara aiki da layin dogo a tsakanin Abuja, babban birnin kasar Nijeriya, da kuma Kaduna da ke arewacin kasar, layin da ya kasance na farko a Afirka da aka gina da fasahohin zamani na kasar Sin. A kwanan nan, jakadan kasar Sin a Nijeriya, Mr.Zhou Pingjian ya shiga jirgin, don gane ma idonsa yadda layin dogon ya kasance.

Wannan shi ne karo na farko da jakadan Zhou Pingjian ya shiga jirgin kasa a nahiyar Afirka, abin da ya sa shi farin ciki sosai, ya ce, "Tuni na so shiga wannan layin dogo, don in ji burin al'ummun kasashen Afirka game da ci gaban zirga-zirgar jiragen kasa. A yayin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya kai ziyara hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka a shekarar 2014, ya gabatar da manufar bunkasa zirga-zirgar jiragen kasa da motoci da jiragen sama na zamani da kuma masana'antu na zamani a Afirka, kuma zirga-zirgar jiragen kasa ya kasance wani muhimmin bangare ne a cikin wannan manufa. Baya ga haka, bunkasa layukan dogo na zamani wani muhimmin bangare ne na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka ta fuskar raya muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, kuma layin dogo tsakanin Abuja da Kaduna wata babbar nasara ce da aka cimma a wannan fanni. Wannan layin dogo ya kasance layin dogo na zamani na farko da aka gina a nahiyar Afirka bisa fasahohin kasar Sin da kuma kayayyadon haka an gina shi bisa la'akari da sigar 'yan Afirka da kuma matakan tsaron nahiyar."

Layin dogon na da tsawon kilomita 186.5, kuma akwai tashoshi 9 a layin. Baya ga haka, jirgin yana gudun da ya kai kilomita 150 a kowane sa'a. Kamfanin CCECC da ya gina wannan layin dogo ya tanadi wasu fannoni hudu kan yadda Nijeriya za ta kula da layin yadda ya kamata. Mataimakin babban manajan kamfanin kuma babban darektan zartaswa na reshen kamfanin da ke Nijeriya, Yan Xuebin ya ce, "Na farko, mun kafa makarantar horaswa a kasar, don horar da ma'aikata da suka hada da matuka da masu gyara da sauransu a kan fasahohin gudanar da layin Na biyu shi ne tsarin gudanar da layin. Na uku, kamfaninmu ya samar da na'urorin samar da wuta biyu da injunan jiragen kasa da suka dace da wannan layin dogo. Na hudu, mun kuma samar da na'urorin da ake bukata a layin da suka hada da tashoshi da sadarwa da sakwanni da binciken tsaro da sauransu."

Kasancewar layin dogo shi ne na zamani na farko a Nijeriya, an yi amfani da ma'aikata da dama a aikin gina wannan layi baya ga samar da dimbin guraben ayyukan yi. Haka kuma kayayyaki da yawa da aka bukata wajen gina layi ma an saye su ne a kasar ta Najeriya, matakin da ya taimaka ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar. Ali Usman, wani fasinja ne da ya ke shiga wannan layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna a kowane mako, ya ce, "Ina aiki a Kaduna, amma iyalaina suna Abuja, kowane karshen mako ina tafiya Abuja, amma ranar Lahadi da safe, kafin karfe goma, ina Kaduna, har na je ofis. Layin dogo yana tafiya a kan lokaci, akwai inganci da tsaro da kuma araha."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China