in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Kano na son inganta hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin
2016-11-11 07:31:53 cri

 


Yau Alhamis 10 ga wata, jakadan Sin dake Nigeria Mista Zhou Pingjian, kwamishina mai kula da harkokin kasuwanci Mista Zhao Linxiang da dai sauran wakilan ofishin jakadancin kasar Sin sun kai ziyara a Kano, inda sun gana da mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar. Wakiliyarmu dake Abuja Amina Xu ta yi rakiya ga jadaka ita kuma ta halarci wannan biki, ga rahoton da ta hada mana.

Jakadan kasar Sin dake Nigeria Mista Zhou Pingjian ya isa birnin Kano ne a daren ran 9 ga wata, ba da jimawa ba Mista Zhou ya gana da wakilan 'yan kasuwa mutanen Sin dake Kano, a safiyar ran 10 ga wata kuma, ya gana da mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar, sun yi musanyar ra'ayi kan yadda Sin da jihar Kano za su iya hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban musamman ma a sha'anin noma, kasuwanci, kimiyya da fasaha da dai sauransu, ni kuma na zanta da mai alfarma mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar, ga cikakkiyar hirarmu.

Amina, wakiliyar sashin Hausa na CRI, daga Kano, Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China