in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Rwanda tana neman kudaden gina tashar samar da wutan lantarki
2016-11-11 07:16:54 cri

Kasar Rwanda tana neman kamfanonin cikin gida da na waje wadanda za su samar da kudaden gina tashar samar da wutan lankarkin kasar wadda ake fatan za ta kara samar da megawatts 80 a kan wadda ake da shi tun farko.

Ministan harkokin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin na kasar Rwanda Claver Gatete ya bayyana cewa, kasar tana neman kimamin dala miliyan 255 don gina babbar tashar samar wutar lantarkin kasar.

Mr. Claver Gatete ya ce, suna fatan idan aka kammala wannan aiki, tashar za ta iya samar da megawatts 563 na wutan lantarki nan da shekarar 2018. Sannan kuma tashar za ta iya samar da isasshen wutan lantarkin da kasar take bukata sakamakon ci gaban tattalin arzikin kasar.

Ma'aikatar samar da kayayyakin more rayuwar kasar ta bayyana cewa, a na sa ran da zarar an kammala gina tashar wadda ke yankin Akanyaru marshland a gundumar Giagara da ke gabashin kasar, za ta samar wa babbar tashar samar da wutan lantarki ta kasar karin megawatts 80.

Kasar Rwanda dai tana neman kudaden gudanar da wannan aiki ne daga bankin kungiyar 'yan kasuwa, da hukumar kula da harkokin kudi ta Afirka, da bankin raya Rwanda da kuma Afreximbank.

Kasar Rwanda wadda ke tsakiyar Afirka, ta kuduri aniyyar kara yawan wutan lantarki da ake amfani da shi ne zuwa megawatts 563 nan da shekara biyu masu zuwa, matakin da ke bukatar kara zuba jarin da ya kai biliyoyin dalaloli a bangaren makashin kasar.

Bayanai na nuna cewa, a halin yanzu kasar Rwanda tana samar da abin da bai gaza megawatts 161 ba, wato ta samu karin megawatts 50 ne kacal a shekarar 2008.

Shugaban hukumar samar da wutan lantarki ta kasar Rwanda Jean Bosco Mugiraneza ya ce, kasar tana bukatar wutan lantarki ne sakamakon bunkasuwar kasar cikin sauri, sabanin tafiyar hawainiyar da ake fuskanta a bangaren samar da wutan lantarkin kasar.

Ya kara da cewa, a saboda haka ne, muka kuduri aniyyar gina babbar tashar samar da wutan lantarki, domin rage gibin da kasar take fuskanta a bangaren wutan lantarki. Idan muka gina wannan tashar sannan muka kammala ayyukan da ke gabanmu, babu tantama za mu cimma nasarar wannan buri da muka sanya a gaba.

Mugiraneza ya kuma jaddada cewa, idan har aka kara yawan wutan lantarkin da ake samarwa a kasar, hakan zai kara jawo samu sha'awar zuba jari a cikin kasar, baya ga inganta rayuwar 'yan kasar ta Rwanda.

Kashi 86.3 cikin 100 na makamashin da kasar Rwanda ke samarwa dai yana fitowa ne daga tsirrai. A saboda haka, a kokarin da mahukuntan kasar ke yi na kara yawan makamashin da kasar ta ke sanarwar, ya sa a watan Disamban shekarar da ta gabata, bankin duniya ya samar wa sashen makamashin kasar dala miliyan 956.

Sannan a watan Mayun wannan shekara, kasar ta kaddamar da aikin gina tashar samar da wutan lantarki ta hanyar amfani da Methane da ke Kivu, tashar da ake sa ran za ta samar da megawattas 100 na hasken wutar lantarki daga tafkin Kivu da ke gundumar Karongi.

Yanzu haka kasar Rwanda ta kulla wata yaryeyejiyar ta shekarau biyar da kasar Kenya, wadda a karkashinta Rwandan za ta shigo da karin megawatts 30 na wutar lantarki daga kasar Kenya. Ana sa ran wannan yarjejeniya za ta fara aiki a wani lokaci a wannan shekara da muke ciki. Bugu da kari, Rwanda tana shirin shigo da karin megawatts 400 na wutan lantarki daga kasar Habasha nan da shekarar 2018.

A watan Fabrairun da ya gabata, Rwanda ta kaddamar da aikin gina tashar samar da wutan lantarki mai amfani da hasken rana, aikin da zai lashe dala miliyan 23.7. Wannan aiki dai shi ne irinsa na farko a yankin kana na uku a nahiyar Afirka, bayan wadanda aka gudanar a kasashen Afirka ta Kudu da Maurituius.

Kamfanin samar da wutan lantarki na Gigawatts Global da ke kasar Netherlands ne dai ya ke gudanar da wannan aiki a gundumar Rwamagana, da ke lardin gabashin kasar. Ana kuma sa ran zai samar wa babbar tashar samar da wutan lantarki ta kasar karin megawatts 8.5 na wutar lantarki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China