in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fatan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka za ta kara samun ci gaba
2016-11-10 11:53:27 cri

A jiya Laraba 9 ga watan Nuwamba ne, aka kawo karshen babban zaben kasar Amurka na shekarar 2016, inda Mr. Donald Trump, dan jam'iyyar Republican ya lashe zaben da ya ba shi damar zama sabon shugaban kasar Amurka na 45. Sakamakon haka, yanzu dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ta shiga wani muhimmin lokaci. A jiyan ne kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika wa Donald Trump sakon taya murnar lashe zaben, inda ya bayyana fatan hada kai tare da shi don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashensu biyu gaba a kokarin da ake yi na kawo alheri ga al'ummomin kasashensu, da ma duniya baki daya.

A lokacin da Mr. Donald Trump zai hau kan mukamin shugabancin kasar Amurka a farkon shekara mai zuwa, shekaru 45 ke nan da marigayi shugaban kasar Amurka Richard Milhous Nixon ya kawo ziyara nan kasar Sin, inda gwamnatocin kasashen biyu suka kulla "Sanarwar Shanghai". Sabili da haka, kasashen biyu suna da wata kyakkyawar damar kara bunkasa dangantakar dake tsakaninsu har zuwa wani sabon mataki. "Sanarwar ta Shanghai" ta kasance tarihi ga kokarin sake dawo da dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka yadda ya kamata. A cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata, ko da yake an fuskanci matsaloli iri daban daban, amma a hakika dai, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba matuka. Kasashen biyu sun yi hadin gwiwa irin ta a zo a gani bisa hakikanin halin da ake ciki a fannonin tattalin arziki da cinikayya, sun kuma tattauna tare da yin cudanya da juna, kan batutuwan da suka shafi warware kalubalolin shiyya-shiyya da duniya baki daya. Sakamakon haka, kasashen biyu sun fahimci cewa, suna dogara da juna sosai, a saboda haka, idan suka hada gwiwa, za su samu moriya tare, amma idan suka yi adawa da juna, to, kowa zai ji a jikinsa.

Kasashen Sin da Amurka tamkar kasa ce mai tasowa mafi girma, da kuma kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya. Haka kuma kasashen biyu kamar kungiyoyin tattalin arziki mafi girma a duk duniya ne. Sannan hakkin kasashen Sin da Amurka ne na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasa duniyarmu. Bugu da kari, suna da moriya iri daya a tarin fannoni daban daban. Bunkasa wata dawaumammiyar dangantaka a tsakanin Sin da Amurka cikin dogon lokaci mai zuwa, ba ma kawai ya dace da babbar moriyar al'ummominsu ba, har ma yana dacewa da moriyar duk duniya.

A lokacin da yake yakin neman zaben shugabancin kasar ta Amurka, Mr. Donald Trump ya ce zai "baiwa kasar Amurka muhimmanci", ya kuma nuna adawa da manufofin kasancewar Sin daya tak a duniya. Har ma ya alkawarta cewa, zai sa kasar Sin a cikin "kasashe wadanda suke sarrafa farashin cinikin kudin musaya", kuma ya ce, ya kamata a biya haraji ga kayayyakin kasar Sin da ya kai kashi 45 cikin kashi dari. Sannan ya ce, yana da shirin karfafa jibge sojojin Amurka a yankin Asiya da dai sauransu.

Ko shakka babu, ana ganin kalaman da ya furka na neman kuru'un jama'a ne kawai. Amma kuma, bayan da aka samu ci gaba cikin shekaru da yawa da suka gabata, yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya ta zama abun da ya fi jawo hankulan jama'a ga dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu tamkar wani babban harsashi ne dake iya tabbatar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ko wata kafar dake ciyar da irin wannan dangantaka gaba.

A waje daya kuma, abubuwan tarihi sun shaida cewa, tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen waje ta hanyar soja ya riga ya kawo illa sosai ga kasar Amurka a fannonin siyasa da tattalin arziki. Ya kamata kasashen Sin da Amurka su karfafa hadin gwiwa da daidaita wasu matsaloli da kalubalolin da ake fuskanta a wasu shiyyoyi da ma duniya baki daya, ta yadda za su iya hada kan sauran kasashen duniya wajen daidaita matsaloli kamar yadda ake fata, ta yadda za su taka rawa a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwar duk duniya.

Hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Amurka zai kawo musu har ma da duniya baki daya moriya. Ana fatan sabuwar gwamnatin kasar Amurka wadda za ta soma aiki a watan Janairu mai zuwa za ta iya nazarin hakikanin halin da ake ciki da kuma daukar matakai da suka dace. Ya kamata kasashen biyu, wato Sin da Amurka su yi amfani da ka'idodin dakatar da nuna adawa da juna, su girmama juna da yin hadin gwiwar neman samun nasara tare, ta yadda za a iya tabbatar da ganin an inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tare da kara ciyar da ita gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China