in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar COP22 a birnin Marrakech na kasar Morocco
2016-11-08 11:48:28 cri

A jiya Litinin, aka kaddamar da taron kasashen duniya wadanda suka kulla "yarjejeniyar ka'idojin tinkarar sauyin yanayin ta MDD" karo na 22 a birnin Marrakech, dake kudancin kasar Morocco. Wannan ne karo na farko da kasashe wadanda suka kulla "Yarjejeniyar ka'dojin" suka yi taro bayan "Yarjejeniyar Paris" ta fara aiki. Sakamakon haka, ana ganin cewa, wannan ne taron da za a dauki matakan aiwatar da yarjejeniyar na a zo a gani.

Mahalarta taron wadanda suka fito daga kasashe da yankuna fiye da 190 za su tattauna matakai na a zo a gani na aiwatar da yarjejeniyar Paris a yayin taron. A yayin bikin kaddamar da taron, Malam Salahedine Mezouar, ministan harkokin wajen kasar Morocco, wanda ke shugabantar wannan taro ya bayyana cewa, babban nauyin da ake dorawa wannan muhimmin taron shi ne tsara wasu ka'idodi wadanda za su iya taimakawa aiwatar da yarjejeniyar Paris kamar yadda ake fata. Malam Salahedine Mezouar ya bayyana cewa, "Tarukan kasashe wadanda suka kulla 'yarjejeniyar ka'idojin tinkarar sauyin yanayin duniya ta MDD' karo na 21 da na 22, muhimman taruka ne guda biyu da za su shafi makomar bil Adama. Idan aka ce, gwamnatocin kasashen duniya sun tsara wani shiri da wasu ma'aunai a yayin taro karo na 21, babban burin da ake son cimmawa a yayin wannan taro karo na 22 shi ne, za a kafa wani tsarin da zai shigar da bangarori daban daban baki daya. Wannan ya zama wajibi gare mu domin jikokinmu na nan gaba, kuma nauyi ne da aka dora mana."

A watan Disamban bara, bangarori 197 wadanda suka kulla "yarjejeniyar ka'idojin tinkarar sauyin yanayin duniya ta MDD" sun kai ga daddale "yarjejeniyar Paris" wadda take da muhimmanci matuka. Ya zuwa yanzu, kasashe da yankuna fiye da 100 sun sa hannu kan takardar amincewa da ita. Sakamakon haka, yarjejeniyar Paris ta zama yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin duniya ta biyu, wadda take kasancewa kamar wata doka ga dukkan kasashen duniya bayan "yarjejeniyar Kyoto".

"Yarjejeniyar Paris" ta fara aiki a wannan shekarar ta 2016 kafin lokacin da aka tsara, wannan ya alamta cewa, yawancin gwamnatocin kasashen duniya suna ganin cewa, ana bukatar hadin gwiwa mai karfi a tsakaninsu domin tinkarar sauyin yanayin duniya. Wannan ya zama wani kyakkyawan yanayi ga shawarwari kan matakan aiwatar da yarjejeniyar Paris. Game da burin da ake son cimmawa a yayin wannan taron, madam Kaisa Kosonen, wacce ke kula da manufofin tinkarar sauyin yanayin duniya ta kungiyar "Green Peace" tana sa ran cewa, "Muna fatan a cikin shekaru 2 masu zuwa, za a iya fitar da wani shirin da zai iya ba mu jagoranci kan yadda za mu iya kammala ayyukan da aka tanada a cikin 'yarjejeniyar Paris', da yin aikin share fage na kara daukar sabbin matakan rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. A waje daya, muna fatan za a iya kara tattaunawa kan yadda kasashe masu arziki za su iya samar da karin kudade, da bada karin tallafi ga kasashe masu tasowa domin tinkarar sauyin yanayin duniya."

Mr. Xie Ji, mataimakin shugaban tawagar wakilan kasar Sin, kuma wani jami'in hukumar kula da harkokin yanayin duniya na kwamitin kula da harkokin ci gaba da yin gyare-gyare na kasar Sin, ya bayyana cewa, a matakin farko na wannan taro, za a yi shawarwari kan wasu batutuwan fasaha. Sannan a mako na biyu, za a shirya tarurukan muhimman jami'ai da wasu bukukuwa domin taya murnar fara aiki da "yarjejeniyar Paris", kuma za a shirya taro a karo na farko na bangarori wadanda suka kulla "yarjejeniyar Paris". Mr. Xie Ji ya ce, bangaren Sin yana fatan za a iya yin hakuri da neman daidaito a lokacin da ake yin shawarwari kan batutuwa daban daban a fili ba tare da boye kome ba. A waje daya, ya kamata bangarori daban daban su maida hankulansu wajen daukar matakan tinkarar sauyin yanayin duniya kafin shekara ta 2020. Mr. Xie ya kara da cewa, "Bayan da aka kulla 'yarjejeniyar Paris', kowace kasa ta gabatar da shirinta na ba da gudummawa wajen tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli. Dukkansu za su hanzarta rage fitar da sinadarai masu dumama yanayin duniyarmu. Ko shakka babu, kasashe masu tasowa suna fatan kasashe masu arziki za su iya cika alkawuransu na ba su tallafin, ciki har da alkawarin samar da tallafin kudi kimanin dalar Amurka biliyan 100. Kasar Sin tana samar da irin wannan tallafi ne ta hanyar yin hadin gwiwa tsakaninta da kasashe masu tasowa, ta yadda kasashe masu ruwa da tsaki za su iya cimma burinsu na rage fitar da sinadarai masu dumama yanayin duniya."

A shekarar ta 2015, kasar Sin ta sanar da cewa, ta kebe kudin Sin RMB yuan biliyan 20 ga asusunta na yin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayin duniya. Sannan a shekarar 2016, kasar Sin ta kaddamar da wasu shirye-shirye, wato kafa shiyyoyi 10 na rage yin amfani da makamashi mai dumama yanayin duniya, sannan ta kaddamar da shirye-shirye 100 na sassautawa da kuma dacewa da sauyin yanayin duniya a sauran kasashe masu tasowa. Bugu da kari, ta fitar da wani shirin yin hadin gwiwa na horas da mutane dubu 1 wajen koyon ilmin tinkarar sauyin yanayin duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China