in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasannin kwaikwayon Sin sun shiga bikin wasan kwaikwayon Afirka
2016-11-07 11:16:12 cri

An gudanar da bikin nune-nunen wasan kwaikwayon kasashen Afirka na shekarar 2016 a birnin Johnnesburg na kasar Afirka ta Kudu tsakanin ranakun 2 zuwa 4 ga wannan watan da muke ciki. Ita ma kasar Sin ta kafa runfar nune-nunen wasannin kwaikwayon kasar, inda aka gabatar da wasannin kwaikwayo masu farin jini na kasar ta Sin da aka fassara daga Sinanci zuwa harsunen kasashen waje da dama. Kuma wadannan wasannin kwaikwayo sun samu karbuwa sosai daga wajen masu kallon su.  

Muryar da kuka saurara, maganganun da aka yi ne a cikin wasan kwaikwayon nan mai taken "Soyayyar matasan Beijing", wadda aka fassara daga Sinanci zuwa harshen Hausa.

A yayin bikin nune-nunen wasan kwaikwayon kasashen Afirka na bana da aka gudanar da birnin Johnnesburg na kasar Afirka ta Kudu, gidan rediyon kasar Sin wato CRI, da babban gidan rediyon da talabiji na lardin Jiangsu na kasar Sin, da rukunin yada al'adun kasar Sin da rediyo da talabiji na birnin Shanghai na kasar Sin, da kamfanin StarTimes dake birnin Beijing, da sauran manyan kamfanonin samar da wasan kwaikwayon kasar Sin sun halarci wurin nune-nunen tare da wasannin kwaikwayo masu farin jini daga kasar ta Sin.

Mataimakin darektan sashen yada wasan kwaikwayon kasar Sin a kasashen ketare na cibiyar fassara wasan kwaikwayon Sinanci zuwa harshen waje ta gidan rediyon kasar Sin wato CRI Meng Yi ya yi bayani cewa, "Wannan shi ne karo na biyu da gidan rediyon CRI ya shiga bikin nune-nunen wasan kwaikwayon kasashen Afirka, yayin wannan bikin na bana, CRI ya gabatar da wasu wasannin kwaikwayon da aka fassara daga Sinanci zuwa harsunan waje da dama ga masu kallo na kasashen Afirka, alal misali, 'labarin limamin Budha da ya kaura zuwa Indiya' da aka fassara daga Sinanci zuwa harshen Swahili, da 'Bari mu yi aure' da aka fassara daga Sinanci zuwa harshen Larabci, da 'labaran miji da mata' da aka fassara daga Sinanci zuwa Faransanci, duk wadannan wasannin kwaikwayon sun samu karbuwa a kasar Sin, muna fatan za su samu karbuwa a kasashen Afirka."

Mataimakiyar babban manajan sashen watsa labarai na kamfanin StarTimes na birnin Beijing Meng Li ta bayyana cewa, wasannin kwaikwayon da kamfaninsa ya samar a kasuwar kasashen Afirka suna kumshe da labarai iri daban daban, alal misali, labari game da Kongfu na kasar Sin, ko labarin da ya shafi tarihin kasar Sin, amma wadanda suka fi samun karbuwa a kasashen Afirka, saboda labaran suna nuna canjin zaman rayuwar zamani na Sinawa. Meng Li ta ce, "Ana fassara wasannin kwaikwayon kasar Sin da suke nuna sauye-sauyen zaman rayuwar zamani na Sinawa zuwa harsunan waje, kuma ana kokarin yada su a kasashen Afirka. Makasudin yin haka shi ne domin bayyana tunanin Sinawa da sabuwar hanyar zaman rayuwa ta Sinawa, daga baya kuma muna fatan al'ummomin kasashen Afirka za su kara fahimtar zaman rayuwar Sinawa."

Tun daga shekarar 2008 ne aka fara kaddamar da bikin nune-nunen wasan kwaikwayon a kasashen Afirka, bikin da ya yi tasiri a nahiyar Afirka, bikin na bana ya samu halartar kwararru a fannin samar da wasan kwaikwayo da kuma watsa labarai sama da dubu daya da suka zo daga kasashe fiye da dari daya, kuma yawancinsu sun zo ne daga kasashen Afirka.

Manajan sashen raya wasan kwaikwayo na kwamitin kula da wasan kwaikwayon kasar Kenya Timothy Ouwazi ya bayyana cewa, kasuwar kasashen Afirka tana sha'awar wasannin kwaikwayon kasar Sin da kuma al'adun kasar Sin, musamman ma abubuwan dake da nasaba da zaman rayuwar al'ummar kasashen Afirka. Ya ce, "Wasannin kwaikwayon da muka fi sha'awa su ne wasannin kwaikwayon dake da nasaba da zaman rayuwarmu yau da kullum, misali, labaran da suka shafi iyalai, da labarai game da ci gaban kasar, da labarai game da kiwon lafiya da ba da ilmi da sauransu. Ina ganin cewa, duk wadannan za su taimaka mana, musamman ma matasa domin ta haka ne za su kara fahimtar yanayin da duniyarmu ke ciki."

Mataimakin shugaban hukumar kula da wasan kwaikwayo ta babbar hukumar kula da watsa labarai da dab'in da rediyo da talabiji ta kasar Sin Yang Zheng shi ma ya shiga bikin na bana, kuma ya halarci taron da aka shirya game da cudanyar wasan kwaikwayo dake tsakanin Sin da Afirka. Bayan taron, Yang Zheng ya bayyana cewa, idan ana son kara shigar da wasan kwaikwayon kasar Sin cikin kasuwar Afirka, to, wajibi ne a yi kokarin bullo da wata hanyar da ta fi dacewa ta yadda za ta samu karbuwa a wajen al'ummomin kasashen Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China