Game da wannan lamarin, a yayin wani taron manema labaru da aka shirya yau Jumma'a a nan Beijing, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, bangaren Sin ya sha bayyana matsayinsa kan yadda ake nuna adawa da lamarin, kuma babu abin da zai hana bangaren kasar Sin daukar matakan da za su wajaba na kare moriyar tsaron kanta. Madam Hua ta nemi bangarorin da abin ya shafa da su mai da hankali kan abubuwan da kasar Sin ke kulawa kamar yadda ya kamata, kuma su gaggauta dakatar da shirinsu na jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami samfurin Thaad. (Sanusi Chen)