in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi nasarar harba sabon nau'in rokan dakon kaya kirar "Changzheng-5"
2016-11-04 14:18:55 cri

A jiya Alhamis da karfe 8 da mintoci 43 na dare, kasar Sin ta harba wani sabon nau'in rokan dakon kaya kirar Changzheng mai lamba 5 a filin harba roka na Wenchang a lardin Hainan dake kudancin kasar. Bayan mintoci 30, bangaren dakon kaya da rokar sun rabu cikin nasara, sa'an nan ya shiga hanyarsa kamar yadda aka tsara, lamarin da ya sheda cewa, an harba rokan dakon kaya kirar Changzheng mai lamba 5 cikin gagarumar nasara.

Roka kirar Changzheng mai lamba 5, wani sabon nau'in roka ne maras guba wadda kuma ba ya gurbata muhalli, kuma tsawonsa ya kai kimanin mita 57, wato kimanin tsayin bene mai hawa 20. Kuma nauyinsa ya kai kimanin ton 870, karfin harba rokar zuwa sama ya zarce ton 1000. Wang Jue, babban mai ba da jagoranci a aikin kera rokan kirar Changzheng mai lamba 5 ya bayyana cewa, an kera rokar ce ta hanyar amfani da sabbin fasahohin zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin. Wang Jue ya kara da cewa,

"Roka kirar Changzheng mai lamba 5 wata sabuwar roka ce kuma mai girma da kasar Sin ta kera, wadda ta hada da dukkan sabbin fasahohin da kasar Sin ta ke da su a fannin zirga-zirgar sararin samaniya, wadanda yawansu ya zarce 240. Yawan sabbin kayayyakin da aka yi amfani da su wajen yin nazari da kera rokar ya zarce kashi 92.5 cikin dari, wanda ya sa rokar ta zarce sauran nau'o'in rokoki a fannin fasaha."

Babban injiniya na hukumar kula da harkokin kimiyya da fasaha da masana'antu a aikin tsaron kasar Sin Mr. Tian Yulong ya bayyana cewa, aikin kera rokar kirar Changzheng mai lamba 5 ya sa kasar Sin ta samu sabon ci gaba a fannin kera rokar dakon kaya da ke amfani da sabon nau'in makamashi da ke matukar karfin daukar kaya a duniya, wanda ya kai mita biyar, wanda a baya ba ta taba zarce mita 3.35 ba. Don haka aikin harba wannan roka cikin nasara ya alamanta cewa, an maye gurbin tsoffin fasahohin dake kushe a nau'o'in rokoki kirar kasar Sin, ya kuma tabbatar da matsayin kasar Sin na kasancewa a kan gaba a duniya, a fannin kera rokan dakon kaya, kuma ya shaida cewa, kasar ta kai ga mallakar fasahar ci gaba ta fuskar zirga-zirga a sararin samaniya, a maimakon harba rokoki masu yawa kawai. Mr. Tian Yulong yana mai cewa,

"Roka kirar Changzheng mai lamba biyar ta zama tamkar wata shaidar sabbin fasahohin dake kunshe a cikin aikin kera rokokin dakon kaya na kasar Sin, wadda ta shaida matsayin koli na kasar Sin na kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a bangaren aikin kera rokan dakon kaya. Kaza lika kuma yadda aka harba sabon nau'in rokar cikin nasara, ya sa kasar Sin tabbatar da samun fasahar kera inji mai ruwa-ruwa maras guba da ke da matukar karfin daukar kaya, kuma mai aiki ba tare da gurbata muhalli ba. Karfin sabon wannan nau'in rokar na daukar kaya ya kai matsayin koli na kasar Sin, kuma yana sahon gaba a duk duniya. Lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin ta kai ga mallakar fasahar ci gaba ta fuskar zirga-zirga a sararin samaniya, a maimakon harba rokoki da yawa kawai. Haka zakila, aikin harba wannan roka cikin nasara ya aza harsashi mai inganci da kuma ba da tabbaci sosai ga wasu manyan ayyukan zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin a nan gaba, ciki har da mataki na uku na aikin binciken duniyar wata, tashar binciken sararin samaniya da kuma aikin farko na binciken duniyar Mars."

Bugu da kari Mr. Tian Yulong ya fayyace cewa, yanzu kasar Sin ta riga ta kaddamar da aikin nazari da kera roka dakon kayayyaki masu yawa. Nan gaba, za ta yi mayar da hankali ga jerin muhimman fasahohin da abin ya shafa.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China