in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin JKS da KMT sun yi ganawa a Beijing
2016-11-02 12:13:27 cri

Jiya Talata da yamma, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS Xi Jinping, ya gana da tawagar wakilan jam'iyyar Kuomindang ta kasar Sin KMT, wadda ke karkashin jagorancin shugabar jam'iyyar Hong Xiuzhu a nan birnin Beijing. Yayin ganawar ta su Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi game da ci gaban huldar dake tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan, wato babban yankin kasar Sin da lardin Taiwan na kasar Sin.

Masanan dake nazari kan huldar dake tsakanin gabobin biyu na zirin Taiwan sun bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, ya kamata jam'iyyun biyu wato JKS da KMT su kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin su, bisa tushen siyasa na ra'ayi daya da aka cimma a watan Nuwamban shekarar 1992, wato su nace ga ka'idar "kasar Sin daya tak a duniya", kana su yaki "ra'ayin samun 'yancin mulkin kan Taiwan" tare, domin ciyar da huldar dake tsakanin gabobin biyu gaba cikin kwanciyar hankali yadda ya kamata.

Shehun malami dake aiki a jami'ar koyar da al'adun kasar Sin Pang Jianguo ya bayyana cewa, shugabar hukumar lardin Taiwan a yanzu Tsai Ing-wen, ba ta nuna ra'ayin da ya dace ba kan huldar dake tsakanin gabobin biyu tun bayan da ta hau karagar mulki, kana ba ta bayyana amincewa da ra'ayin "kasar Sin daya tak a duniya" da aka cimma a shekarar 1992 ba, lamarin da ya katse cudanyar dake tsakanin hukumomin sassan biyu. Yanzu dai ganawar da aka yi tsakanin shugabannin jam'iyyun biyu za su bude wata taga ga cudanya tsakanin gabobin biyu a nan gaba. Pang Jianguo ya bayyana cewa, "Kawo yanzu, ba a maido cudanya tsakanin hukumomin sassan biyu wato babban yankin kasar Sin da lardin Taiwan na kasar Sin bisa dalilin Tsai Ing-wen ba, amma shugabannin jam'iyyun biyu wato Xi Jinping da Hong Xiuzhu, sun gana a birnin Beijing, wanda hakan ya nuna cewa, suna maraba da daukacin kungiyoyi ko mutane wadanda suka amince da ra'ayin 'kasar Sin daya tak a duniya', wanda aka cimma a shekarar 1992, da kuma yaki da ra'ayin samun mulkin kan Taiwan. Nan gaba kuma ana iya kara yin cudanya tsakanin jama'ar gabobin biyu, da haka kuma ana iya gano cewa, babban yankin kasar Sin yana kokari domin maido da cudanya dake tsakanin hukumomin gabobin biyu."

Yayin ganawar, babban sakatare Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, an fuskanci banbance-banbance da dama tsakanin jam'iyyun biyu wato JKS da KMT, amma a sa'i daya kuma, jam'iyyun sun taba gudanar da hadin gwiwa tsakanin su yayin da al'ummar kasar Sin ta gamu da matsala, don haka ana iya cewa, sun taka muhimmiyar rawa tare, domin ciyar da al'ummar kasar Sin gaba.

A shekarar 2005, jam'iyyun biyu sun sake maido da cudanya tsakanin su, bayan da suka warware matsaloli da dama, shugabannin jam'iyyun biyu sun tabbatar da buri daya na samun bunkasuwar gabobi biyu na zirin Taiwan cikin kwanciyar hankali tare.

Ya zuwa shekarar 2008, jam'iyyun biyu da 'yan uwan gabobi biyu sun yi kokari matuka tare, domin bude wani sabon babi na raya huldar dake tsakanin gabobi biyu a karkashin sabon yanayi, hakan shi ma ya kawo moriya ga 'yan uwan gabobi biyu.

Darektan cibiyar nazari kan huldar dake tsakanin gabobi biyu na zirin Taiwan Qiu Kaiming, ya bayyana cewa, jam'iyyar Kuomintang ta ba da babbar gudumawa kan aikin raya huldar tsakanin gabobi biyu, kuma a yanzu ya kamata ta ci gaba da yin kokari, musamman ma a cikin tsibirin Taiwan. Ya ce, "Samun ci gaba cikin kwanciyar hankali ya fi dacewa da moriyar 'yan uwan gabobi biyu, kuma ya fi dace da ra'ayin jama'ar Taiwan, saboda 'yan uwan gabobi biyu suna fatan za a bunkasa tattalin arziki, da zaman takewar al'umma cikin kwanciyar hankali. To, idan ana son cimma burin hakan, dole ne a nace ga ra'ayin kasar Sin daya tak a duniya."

Qiu Kaiming yana ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu, abu mafi muhimanci shi ne jam'iyyun biyu su dauki nauyin tarihi bisa wuyansu, domin kara karfafa cudanya da hadin gwiwa tsakanin su bisa tushen amincewar juna, yana mai cewa, "Ya kamata a nace ga ra'ayin kasar Sin daya tak a duniya, domin ciyar da huldar dake tsakanin gabobi biyu gaba cikin kwanciyar hankali, musamman ma wajen yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki, da musanyar jama'a, saboda hakan zai samar da damammaki ga al'ummar Taiwan na samun moriya daga hakan."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China