in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yunkurin kasashen Afrika na ficewa daga ICC lamari ne mai sarkakiya
2016-11-01 13:57:46 cri

Matakin da kasar Afrika ta kudu ta dauka na bayyana matsayinta game da ficewa daga kotun hukunta manya laifukka ta kasa-da-kasa wato ICC, wata alama ce dake gwadawa duniya cewa, kasashen Afrika a shirye suke su janye wakilcinsu daga kotun hukunta laifukan yakin ta duniya.

Uganda ce kasa ta farko da ta shigar da kara a gaban kotun ta birnin Hague, sai dai an fara samun cece kuce tun a watan Janairu a lokacin da shugabannin Afrika suka gudanar da taron koli a Addis Ababa na kasar Habasha, inda kasashen na Afrika da dama suka fara bayyana anniyarsu ta ficewa daga kotun, bisa zargin da suke yiwa kotun ta ICC cewa, ta fi mayar da karfinta kan nahiyar Afrika, tana kau da kai daga abubuwan da ake tafkawa a sauran kasashen duniya.

Cikin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan harkokin wajen kasar Uganda Okello Oryem, ya bayyana cewa;

"Muna sa ran kasar Uganda za ta sanar da matsayinta na janye wakilci daga kotun ICC a lokacin taron kolin kungiyar tarayyar Afrika AU, wanda za'a gudanar a watan Janairun shekarar 2017 a Addis Ababa. Muna sa ran kasashe da dama za su dauki irin wannan mataki. Muna bukatar dukkannin kasashen Afrika su fice daga kotun ta ICC."

A wani taron kolin na kungiyar tarayyar Afrika da ta gudanar a kasar Rwanda a watan Yuli, shugabannin kasashen Afrika sun kada kuri'a mafi rinjaye game da kudirin janyewar kasashen mammobin kungiyar daga wakilcin kotun hukunta manyan laifukan ta kasa da kasa. Bayan daukar wannan mataki ne, kasar Afrika ta kudu, wacce ke da matukar tasiri a nahiyar, ta aikewa MDD wasika, game da matsayinta na ficewa daga kotun ta ICC.

Kasashen Gambiya da Burundi su ma tuni suka ambata matsayinsu na ficewar, sai dai har yanzu ba su cika ka'idojin daukar wannan mataki ba.

Kasashen Afrika suna taka gagarumar rawa wajen amincewa da yarjejeniyar da aka cimma a birnin Rome, wacce daga nan ne aka kafa kotun ta ICC. Da farko kasashen Afrika na kallon yunkurin kafa ICC a matsayin abu mai muhimmancin gaske wajen farauto tare da hukunta shuagabanni masu hankoron haddasa yake yake a duniya.

Tun daga lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa kotun a shekarar 2002, Uganda ce kasa ta farko da ta shigar da kara a gaban kotun, inda ta bukaci a hukunta manyan kwamandojin sojin 'yan tawayen kasar wadanda aka zarga da aikata laifukan yaki a arewacin kasar.

Tun daga wancan lokacin aka dinga tururuwar gabatar da shugabanni da ake zargi da haddasa yaki, musamman madugun yaki na jamhuriyar demokaradiyyar Congo. Bayan da kotun ta ICC ta fara farautar wasu daga cikin shugabannin Afrika, alal misali, kotun ta aike da takardar sammaci ga shugaban Sudan Omar al-Bashir, da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da su bayyana a gabanta.

Bayan daukar wannan mataki ne, shugabannin kasashe da dama suka fara zargin kotun ta ICC da mayar da karfinta kan nahiyar Afrika, tana kau da kai daga abubuwan da ake tafkawa a sauran kasashen duniya.

Ministan harkokin wajen kasar Ugandan ya kara da cewa, "mun sha fadawa kotun ICC cewa, ta saurari bahasi daga shugabannin kasashen Afrika, amma ta yi kunnen uwar shegu. Idan da a ce ta saurari hanzarin shugabannin, da wannan lamari na janyewa daga kotun bai faru ba. Sun ki sauraro, sun yi gaban kansu, suna sauraron maganar shugabannin da suka yi mana mulkin mallaka ne kadai."

"Ba mu da wata matsala game da rahotannin da hukumomin sa'ido na kasa da kasa suke bayarwa game da take hakkin bil adama, ko cin zarafi, ko haddasa yaki, ko kisan kiyashi. Amma yadda matsalar take shi ne, dole ne a yi adalci tsakanin shugabannin Afrika, da na Turai, da na gabas ta tsakiya, da na Asiya, da na yankin Amurka. ICC ba ta yi abin da ya dace. Tana yin bita da kulli ne ga shugabannin Afrika kadai." In ji Oryem.

Ko da yake, ba dukkanin kasashen Afrika ba ne suke da muradin janyewa daga wakilcin na ICC. Kasashen Senagal da Botswana sun soki lamirin matakin da Afrika ta kudu ta dauka na ficewa daga kotun.

Sai dai masu sharhi kan al'amurran na ganin cewa, matakin janyewa da kasashen na Afrika ke dauka, zai iya haddasa a fuskanci rashin tantance hakikanin shugabannin da suka cancanci hukunci a gaban kotun na hakika. Sannan mataki zai iya haifar da a samu rashin gaskiya da son zuciya, kasancewar ba za'a iya hukunta shugabannin dake kan madafun iko ba.

Alex Fielding, wani mai sharhi kan al'amurran siyasa dake aiki a wani kamfani na Max Security Solution ya bayyana cewa, "gaskiya ne babu wasu matakai da za'a dauka wadanda za su iya yin tasiri a matsayin kotu a shiyyar Afrika, da yawansu ba za su iya tuhumar manyan shugabannin siyasa ba, da kuma wadanda suke kan madafun iko".

Phil Clark, wani masani kan harkokin hulda da kasashen waje a sashin nazarin kan Afrika na jami'ar London, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, shugabanin dake kan mulki za su iya yin amfani da damarsu wajen kaucewa duk wata tuhuma daga kasashen waje, sannan za su kare kansu daga duk wani matsin lamba na cikin gida.

Alex Fielding ya kara da cewa, ya kamat a kyautata tsarin ICC domin gudanar da aikinta bisa adalci yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China