in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta harba rokar dakon kaya ta Changzheng-5 a watan Nuwamba
2016-10-28 13:36:33 cri

A yau Juma'a ne aka kammala ayyukan fasaha, na sabuwar rokar dakon kaya ta Changzheng-5, a filin harbar rokoki dake birnin Wenchang na lardin Hainan na kasar Sin, inda kuma aka yi jigilar rokar zuwa yankin harba kumbuna, domin shirin harba ta a watan Nuwamba.

Wannan sabuwar rokar dake dauke da kaya mai kuma karfi gaske, an kera ta ne ta hanyar amfani da wasu sabbin fasahohi, kuma fadin ta ya kai mita biyar.

Rahotanni sun nuna cewa za a harba rokar ne ta hanyar amfani da makamashi maras guba ko gurbata muhalli, kana tsarin sarrafa ta na da sauki sosai, don haka ana da tabbacin cewa za ta kafa sabon tarihi na gudanar da managarcin aiki, a fannin amfani da rokokin dakon kayan binciken sararin samaniya na kasar Sin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China