in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu da Burundi sun fice daga ICC
2016-10-25 14:00:08 cri

Wata takardar da aka fitar a ranar 21 ga wata wadda ministar hulda da hadin gwiwa da kasa da kasa ta kasar Afirka ta kudu Madam Maite Nkoana-Mashabane ta rattabawa hannu ta shaida cewa, kasar Afirka ta Kudun ta fara shirin ficewa daga kotun hukunta manyan laifuffuka na kasa da kasa, wato ICC. Kafin wannan kuma, a ranar 18 ga wata, shugaban kasar Burundi ya sa hannu a kan wata takardar umurni, inda a hukunce ya sanar da ficewar kasar daga kotun, abin da ya sa kasar ta zama kasa ta farko da ta fice daga kotun.

Afirka ta Kudu ta sanar da shirin ficewa daga kotun hukunta manyan laifuffuka na kasa da kasa a yayin da shugaban kasar Sudan Omar Hassan Ahmed Al-Bashir ya halarci taron kolin kungiyar tarayyar Afirka karo na 25 da aka gudanar a watan Yunin shekarar bara a birnin Johannesburg, Amma kasancewar kasar Afirka ta kudu kasar da ta daddale yarjejeniyar Roma, wadda ta kafa kotun ta ICC, shi ya sa kotun ta bukaci gwamnatin Afirka ta kudun da ta kama shugaba al-Bashir bisa zarginsa da aikata laifin yaki da kisan kare dangi domin mika shi ga kotun. Sai dai gwamnatin Afirka ta kudun ta yi fatali da bukatar, a maimakon ta kama shi, sai ta bar shi ya halarci taron tare kuma da ficewa daga kasar ba tare da wata matsala ba. Daga baya kuma, babbar kotun kasar Afirka ta kudu ta yanke hukuncin cewa, abin da gwamnatin kasar ta yi ya keta tsarin mulkin kasar. Amma gwamnatin kasar Afirka ta kudu daga nata bangaren ta yi kukan cewa, ya zama dole ta martaba yarjejeniyar da abin ya shafa wajen gudanar da taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, idan har Afirka ta Kudun ta kama shugaba Al-Bashir kamar dai yadda kotun ICC ta bukata, lalle da wuya ta samu amincewa daga tarayyar Afirka a nan gaba. Kafin wannan, kungiyar tarayyar Afirka ta bukaci kotun ICC da ta daina kama duk wani shugaba na kasashe mambobinta, haka kuma ba za ta bar kasashe mambobinta su taimaka wa kotun wajen kama shugabanninta ba.

Sanarwar da kasar Afirka ta kudu ta mika wa MDD ta nuna cewa, an amince da kasar ta Afirka ta kudu ta zama mamba a kotun ICC, amma a cikin shekaru 10 da suka biyo baya, duk da kokarin da kasar ta Afirka ta kudu ta yi wajen aiwatar da yarjejeniyar Roma, amma ta gano cewa, nauyin da ke bisa wuyanta na daidaita rikici cikin lumana ya kan saba wa bayanin da kotun ta gabatar game da yarjejeniyar kasancewa mamba a cikin ta. Don haka, ba yadda za ta yi illa ta yanke shawarar ficewa daga kotun. Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, bisa yarjejeniyar Roma, kudurin ficewa daga kotun zai fara aiki ne shekara guda bayan da babban sakataren MDD ya samu sanarwar.

Kwana daya kafin ma'aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudun ta samu sanarwar, shi ma shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya sa hannu a kan wani shirin doka, inda aka sanar da ficewar kasar daga kotun ICC, lamarin da kuma ya sa kasar ta zama kasa ta farko da ta fice daga kotun tun bayan kafuwarta.

Tun bayan kafuwar kotun ICC a shekarar 2002, kasashen Afirka sun nuna himma wajen daddale yarjejeniyar Roma, wadanda yawansu har ya kai kimanin kashi 1/3 na kasashen da suka daddale yarjejeniyar. Sai dai bayan da aka fara aiki da yarjejeniyar, kararraki 9 da aka alakanta su da kasashe 8 dukkansu sun shafi kasashen Afirka ne. Baya ga Sudan, akwai kuma kasashen jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da Kenya da Libya da Uganda. A ganin shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, ana amfani da kotun ICC ne wajen yakar kasashen Afirka. Shugaban kasar Ruwanda ma ya zargi kotun ICC da nuna adalci ga wasu ne kawai, wato "an karkasa duniya zuwa sassa daban daban, wasu mutane suna da ikon sukar wasu da sunan nuna adalci ko kuma fakewa da sunan dokokin duniya." (Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China