in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Afirka sun yi mu'amala ta fuskar shari'a
2016-10-24 10:32:01 cri

A karshen makon jiya ne, a nan Beijing aka bude taron kara wa juna sani na kasa da kasa kan kalubalen da ake fuskanta a fanni dokoki a yayin da ake kokarin zuba jari da tafiyar da harkokin tattalin arziki da kuma cinikayya da kuma yadda za a daidaita wannan matsala, wanda hukumar tsara dokoki ta kasar Sin ta shirya, tare da taimakon kungiyar kula da dokoki da kungiyar ciniki ta duniya, cibiyar kula,da harkokin shari'a ta kasar Sin. Taron ya samu halartar wakilai kusan dari 2 daga bangarorin shari'a da masana'antu da kasuwanci daga kasar Sin da kasashe 23 na Asiya, Afirka da Turai, inda suka tattaunawa kan yadda za a yi rigakafin barazanar shari'a a fannonin zuba jari, tattalin arziki da cinikayya a fadin duniya, a kokarin zurfafa mu'amala a tsakanin Sin da Afirka ta fuskar shari'a, ta yadda za a ba da tabbaci don ganin Sin da Afirka sun samu hadin gwiwa mai dorewa ta fuskar tattalin arziki da ciniki.

Dangane da wannan taron kawa wa juna sani da ya halarta, Ibrahim Auta, babban alkalin babbar kotun tarayyar kasar Najeriya ya bayyana jin dadinsa da halartar taron, tare da nuna cewa, "A baya, yawancin wadanda suka samu damar halartar wannan mu'amala galibi masana tattalin arziki da harkokin cinikayya ne daga bangaren mahukuntan kasashensu da kuma kamfanoni. Amma yau a madadin takwarorina masana dokoki, na samu damar ziyartar kasar Sin tare da yin mu'amala da takwarorinmu na kasar Sin tare da yin koyi da juna, lamarin da ya kasance tamkar wata alama mai kyau, wato kasashen Sin da Afirka suna ci gaba da hakaba tare da sabunta hadin gwiwarsu. Kana kuma kasar Sin ta bayar da kyakkyawar dama ga kamfanonin kasashen Afirka wadanda suke son hada kai da takwarorinsu na kasar Sin ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, ta yadda za su kara sanin dokokin kasar Sin, da kuma yiwuwar hada kai da kasar Sin."

A kokarin da ake yi na jawo hankalin karin kamfanonin kasar Sin ta yadda za su zuba jari da hakaba ciniki a nahiyar, wasu kasashen Afirka sun riga sun yiwa dokoki da harkokinsu na siyasa gyaren fuska. Madam Elizabeth Mutsoli, mai ba da shawara ta fuskar shari'a a ma'aikatar shari'a ta kasar Kenya ta bayyana cewa, a shekaru 3 da suka gabata, gwamnatinta ta yi gwaje-gwaje da dama, a kokarin kara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari na ketare. Alal misali, saukaka matakan bude kamfani. Idan masu zuba jari na ketare sun gamu da wata matsala ta kasuwanci a kasar ta Kenya, to, za a iya warware wannan matsala ta hanyoyi daban daban. Madam Mutsoli ta ce,"Masu zuba jari na ketare wadanda suka gamu da matsaloli na kasuwanci a kasar ta Kenya za su je kotuna, amma za a dauki tsawon lokaci. Sa'an nan za su mika batunsu game da batutuwan da suka shafi kasuwanci a kotun shari'a. Har wa yau kuma, za su nemi taimako a kotun kasa da kasa ta Kenya, inda za a yi kokarin warware matsalar cikin dan kankanin lokaci, sakamakon gudanar da shari'a kan batun cikin sauri. Mun shawarci kamfanonin kasar Sin da su daidaitaduk wata matsala ko sabani a kotun kasa da kasa ta Kenya. Baya ga haka kuma, akwai wasu hukumomi da ke shiga tsakani a kasarmu ta Kenya."

Ba shakka, kamfanonin kasar Sin su ma suna bukatar kara fahimtar dokokin kasashen Afirka, a kokarin yin ciniki ba tare da wata matsala ba. Deng Song, darektan shari'a na sashen shari'a na kamfanin Star Times na kasar Sin ya dade yana aiki a kasashen Afirka. Ya bayyana mana cewa, "Tun farko har zuwa yanzu, mun sha gamuwa da matsaloli da dama. A fannin shari'a kuma, a baya ba mu san kome game da kasashen Afirka ba, balle ma dokokin kasashen. Muna kara sanin dokokin wurin sannu a hankali. Mun koyi darussa a sakamakon matsalolin da muka gamu da su, lamarin da ya taimaka mana samun nasarar yin ciniki a wurin."

Deng Song ya kuma gargadi kamfanonin kasar Sin da ke kasashen Afirka da su yi kokarin sanin dokokin wuraren da suke gudanar da harkokinsu, ya kuma ba su shawarar kyautata yin cudanya da kamfanonin lauya na wurin, ofishin jakadancin kasar Sin da ke wurin, har ma da hukumomin shari'a yadda ya kamata, a kokarin kiyayeyanci da kuma hakkokinsu. Har wa yau kuma mista Deng ya yi bayanin cewa, idan akwai bukata, to, wajibi ne a nuna sanin ya kamata wajen kai kara a kotu domin daidaita sabani ko wata matsala da ta taso, a kokarin dakile aniyar masu mugun nufi na lalata moriyar kamfanonin kasar Sin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China