in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya
2016-10-21 18:53:02 cri
Majalisar dattawan Najeriya ta yi kashedin cewa,muddin gwamnatin tarayyar kasar ta gaza hanzarta daukar matakan da suka wajaba na magance matsalar da sashen jiragen kasar ke fuskanta,babu tantama Najeriyar za ta iya fuskantar haduran jiragen sama.(Vanguard)

Hukumar yaki da fasa-kwauri ta Najeriya ta sanar da korar wasu manyan jami'anta guda 29,ciki har da masu mukamin mukaddashin kwanturola 4 da mataimakin kwanturola 5. Wannan kora na zuwa ne kasa da mako guda, bayan da hukumar ta kori wasu kananan jami'ai 17.

Sauran wadanda korar ta shafa sun hada da manyan sifuritanda 7 da masu mukamin sifuritanda 4. Sai kuma wasu jami'ai 10 da aka yiwa ritaya daga aiki.(The Punch)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China