in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu ci gaba a yakin Mosol, in ji firayin ministan Iraki
2016-10-21 10:45:34 cri

A jiya Alhamis ne firaministan kasar Iraki Haider al-Abadi ya bayana cewa, karkashin goyon bayan kasashen duniya, yakin da ake yi a kasar da nufin sake kwato birnin Mosol, babban birnin na biyu na kasar dake karkashin mamayen kungiyar IS na samu ci gaba, sama da yadda aka yi hasashen a baya.

Al-Abadi wanda ya bayyana hakan yayin taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa, ya ce ministocin harkokin wajen kasashen Faransa da iraki, sun kira wani taron hadin gwiwa na kasa da kasa a matsayin koli a Paris, inda suka tattauna game da yadda za a wanzar da zaman lafiya a birnin Mosol, bayan kwato shi daga hannun mayakan IS.

Taron dai ya samu halartar wakilai daga kasashe da kungiyoyi sama da 20, kamar su Amurka, da Faransa, da Jamus, da Turkiyya da sauransu, sai dai kuma ba a gayyaci wakilan kasashen Iran da Rasha ba.

Firayin minista Abadi ya halarci wannan taro ne a birnin Bagadaza ta hanyar sadarwa ta bidiyo. Yayin taron, ya jaddada cewa makasudin kwato wannan yaki na Mosol shi ne, domin kiyaye cikakken yankin kasar ta Iraki.

Wakilan da suka halarci taron sun bayyana cewa, idan ana son dakile kunigyar IS cikin nasara, kamata ya yi gwamnatin Iraki, da dakarun wurare daban daban dake kasar su sulhunta ta hanyar siyasa, saboda hakan ne kawai zai kara kyautata yanayin da Mosol da sauran yankunan da abin ya shafa ke ciki. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China