in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa na cin gajiyar inshorar cututtuka mafiya tsanani
2016-10-20 10:05:04 cri

Shugaban hukumar dake kula da harkokin inshorar lafiya ta kasar Sin Huang Hong, ya ce yawan Sinawa dake cin gajiyar inshorar cututtuka mafiya tsanani a kasar ya haura mutum biliyan guda. Hakan a cewar sa mataki ne na rage adadin kudade da marasa lafiya ke kashewa wajen jiyya.

Mr. Huang ya ce an tanaji inshorar lafiya ga mazauna birane, da kauyuka, da daliban makarantu, tsarin da yanzu haka ya hade dukkanin sassan al'ummun da a baya ba sa cin gajiyar sa.

Shugaban hukumar ta CIRC ya kara da cewa, an fara aiwatar da wannan tsari na inshora ne a matakin gwaji a shekarar 2009, kana aka fadada shi a shekarar 2015, ta yadda aka fara biyan marasa lafiya kudaden da suke kashewa wajen jiyya, sama da mizanin kudaden inshorar lafiya na gama-gari. Ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne da nufin dakile matsalar talauci dake karuwa tsakanin al'umma sakamakon fama da cututtuka.

A daya bangaren kuma, Mr. Huang ya bayyana kalubalen da tsarin inshorar lafiyar cutuka masu tsanani ke fuskanta, ciki hadda batun rashin kayyade yawan kudaden da za a iya mayarwa marasa lafiya dake cin gajiyar sa, kan cutuka da yawan su ya zarta rabin cutuka 605 da shirin ya kunsa.

Daga nan sai ya jaddada aniyar mahukuntan kasar ta Sin, game da ci gaba da daukar matakan kafa managarcin tsarin inshorar lafiya mafi dacewa, da samar da kudaden mayarwa ga marasa lafiya, tare da bada kariya mafi nagarta ga al'ummun dake zaune a birane da karkara, a fannin kula da lafiya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China