in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
GDP na Sin a rubu'in 3 ya karu da kashi 6.7 cikin dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara
2016-10-20 10:00:06 cri

Bisa alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a jiya Laraba, an ce, a rubu'i na 3 na shekarar nan, wato tsakanin watan Yuli da Satumba, adadin GDP, wato yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa ya karu da kashi 6.7 cikin dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, adadin da ya yi daidai da na rubu'i na farko da na biyu na bana. Game da wannan, kakakin watsa labarai na hukumar kididdigar kasar ta Sin Sheng Laiyun, na ganin cewa a takaice, ana iya cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu bunkasuwa yadda ya kamata, har ya haura hasashen da aka yi a baya.

Alkaluman da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, adadin GDP da kasar Sin ta samu a cikin watanni 9 da suka gabata, wato tsakanin watan Janairu da Satumba ya kai kudin Sin Yuan biliyan dubu 52 da dari 9 da 97, adadin da ya karu da kashi 6.7 cikin dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara, kuma a ko wanen rubu'in, adadin GDP na karuwa da kashi 6.7 cikin dari.

Kakakin watsa labarai na hukumar kididdigar kasar Sin Sheng Laiyun yana ganin cewa, hakan ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata tun farkon shekarar bana, Sheng Laiyun ya bayyana cewa, "Ana iya gano ci gaban tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare daga fannoni da dama. Alal misali, samun karuwarsa, da samar da guraben aikin yi, da raguwar farashin kudi da kuma cinikin waje. A halin da ake ciki yanzu, adadin GDP na kasar Sin ya karu da kashi 6.7 cikin dari, kuma adadin CPI wato yawan farashin kayayyakin da jama'a suke saya ya karu da kashi 2 cikin dari, kana adadin mutanen da suka rasa aikin yi ya kai kashi 5 cikin dari, duk wadannan alkaluman na nuna cewa, tsarin tattalin arzikin kasar Sin yana da inganci. Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Sin ta samu babban sakamako wajen aiwatar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, musamman ma a fannonin tsarin sana'o'i, da tsarin bukatun jama'a. Kaza lika, kasar Sin ta yi nasara a bayyane wajen tsimin makamashi, inda adadin makamashin da aka yi amfani da shi yayin da ake kokarin samun karuwar GDP tsakanin watan Janairu da Satumba, ya ragu da kashi 5.2 cikin dari idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara, kuma wannan adadi zai ragu sannu a hankali a nan gaba."

Alkaluman sun nuna cewa, tun daga farkon shekarar bana, adadin jarin da aka zuba a aikin gina gidajen kwana a fadin kasar Sin, ya kai kudin Sin Yuan biliyan dubu 7 da dari 4 da 59, adadin da ya karu bisa kashi 5.8 cikin dari, idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, aikin gina gidajen kwana ya ba da babbar gudummuwa, yayin da ake kokarin neman samun ci gaban tattakin arziki a nan kasar Sin, har ya kai kashi 8 cikin dari.

Abun da ya fi jawo hankalin jama'a shi ne, tun farkon watan Oktoban da muke ciki, manyan biranen kasar Sin da yawansu ya kai 20, kamar su Beijing da Tianjin da Shenzhen, sun fitar da sabbin manufofi na kara kyautata kasuwar sayar da gidajen kwana, wadanda ke kumshe da manufar kayyaden yawan gidajen kwana da ake iya sayen su, da manufar kayyaden yawan rancen kudin da ake iya samu daga banki domin sayen gidajen kwana da dai sauransu.

Sheng Laiyun ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka fara aiwatar da wadannan manufofin shi ne, domin hana sana'ar gina gidajen kwana ta kawo illa ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

Yayin da ake yin hasashe kan karuwar tattalin arziki a watanni 3 masu zuwa wato rubu'i na 4 na bana, shugaban sashen nazari kan tattalin arziki na cibiyar bunkasa cudanyar tattalin arziki tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin Xu Hongcai ya bayyana cewa, "Ina ganin cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun karuwa sannu a hankali a watanni 3 masu zuwa, kila adadin karuwarsa zai ragu kadan, wato kila adadin zai sauka zuwa kashi 6.6 cikin dari, dalilin da ya sa haka shi ne, domin sabbin manufofin da ake aiwatarwa kan sana'ar gina gidajen kwana."

Game da darajar kudin Sin RMB kuwa, Sheng Laiyun ya bayyana cewa, kwanan baya, darajar kudin musaya tsakanin kudin Sin RMB da dalar Amurka ta ragu, wato kudin Sin Yuan 6.7 bai kai dalar Amurka guda daya ba, wannan ba matsala ba ce, kuma ba zai yiwu darajar kudin Sin ta ci gaba da raguwa ba, ya ce, "Tattalin arzikin kasar Sin yana gudana cikin kwanciyar hanhali yadda ya kamata, tsarin tattalin arzikin kasar yana kyautatuwa, ingancinsa shi ma ya karu, duk wadannan dalilai za su tabbatar da darajar kudin RMB, kana RMB ya riga ya shiga tsarin kudaden ajiya na ketare wato SDR, hakan ma zai kara yawan bukatar RMB a fadin duniya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China