Mr. Liu wanda ya yi wannan tsokaci a jiya Laraba, a taron MDD wanda mai jiran gadon majalissar Antonio Guterres ya halarta, ya kara da cewa akwai bukatar MDDr ta tallafawa kasashen duniya, wajen bada kariya ga rukunonin mutane dake da rauni. Daga nan sai ya yiwa majalissar fatan samun nasarori a ayyukan da ta sanya gaba, yana mai cewa ko shakka babu, kasar Sin za ta ci gaba da bada gudummawar da ta dace da kudurorin majalissar na bunkasa tsaro, da samar da ci gaba mai dorewa, tare da inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya.
Kaza lika Mr. Liu ya yi fatan MDDr za ta kara himma, wajen ganin an samu nasarar fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, bisa tsarin shugabanci mafi dacewa, wanda zai bada damar cimma moriyar juna bisa adalci. (Saminu)