in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afirka suna da sabuwar damar bunkasa tattalin arziki na teku
2016-10-19 10:59:15 cri

Yanzu haka manazarta na ganin cewa, tattalin arzikin teku na bude wata sabuwar dama ga kasashen Afirka a fagen samar da ci gaba. Kuma ko da yake matsalolin 'yan fashin teku, da sana'ar su ba bisa ka'ida ba, da fitar da gurbatattun kayayyaki cikin teku da dai makamantansu, suna kawo cikas ga kokarin bunkasa tattalin arzikin teku a Afirka, a kwanan baya, an zartas da "kundi game da wanzar da zaman lafiya da tsaro, da bunkasa harkokin teku na kungiyar AU", wato "kundin Lome". Manazarta suna ganin cewa, wannan mataki da AU ta dauka ya samar da ka'idojin shari'a kan yadda za a bunkasa tattalin arzikin teku, har ma ya samar da sabuwar damar bunkasa shi.

Kasashe 38 daga jimillar kasashe 54 na Afirka suna da iyaka da teku, kuma kaso 90 bisa dari na yawancin kayayyakin da ake shige da ficen su a kasashen Afirka na bi ta ruwa ne. Kaza lika wasu muhimman hanyoyin kasuwanci suna yankunan teku na Afirka. Bugu da kari, akwai albarkatun teku iri iri da za su zama muhimman tushen bunkasa tattalin arzikin yankunan tekun Afirka.

Madam Dlamini Zuma, shugabar kwamitin AU ta bayyana cewa, tattalin arzikin yankin teku suna kasancewa a ko'ina. Yawan kudin tattalin arzikin teku da zai shafi harkokin sufurin kayayyaki da ba da hidima, zai kai dalar Amurka biliyoyin dubu, kuma za su iya samar da miliyoyin guraban aikin yi wadanda za su shafi lodi, da sufurin kayayyaki, da hidimar inshorar kaya, da gudanar da tasoshin ruwa, da sha'anin yawon shakatawa, da kamun kifi da dai sauransu. Amma har yanzu, kasashen Afirka ba su zuba isassun kudi wajen bunkasa tattalin arzikin teku ba.

A cikin wani jawabin da ya gabatar, sakataren zartaswa na kwamitin tattalin arzikin Afirka na MDD Mr. Carlos Lopez ya ce, yawan yankunan teku da ke karkashin mulkin kasashen Afirka ya kai murabba'in kilomita miliyan 13. Sabo da haka, za a iya bayyana cewa, ana da wata Afirka ta daban dake yankunan teku.

A da, kasashe mambobin AU suna hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin tsaro kan yankunan teku a yayin da ake hadin gwiwa a tsakanin wasu kasashe kawai wajen bunkasa tattalin arzikin teku. Amma, bayan da aka fitar da wannan "kundi na Lome", irin wannan hadin gwiwar bunkasa tattalin arzikin teku zai zama wani muhimmin matakin da kasashe mambobin AU za su dauka cikin hadin gwiwa.

A cikin "rahoto na shekarar 2016, na hasashen yadda ake samar da guraban aikin yi da bunkasa zamantakewar al'ummomin duniya", wanda kungiyar kwadago ta kasa da kasa ta fitar, an bayyana cewa, yawan guraban aikin yi na wucin gadi da aka bayar a kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara, ya kai kashi 70 cikin kashi dari. Wannan kundi na Lome zai taka muhimmiyar rawa ga kokarin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka wajen bunkasa sana'o'in kamun kifi, da sarrafa kayayyakin kifi, da samar da kayayyakin guba na teku, da tasoshin ruwa da dai sauransu.

Ba ma kawai kasashen Afirka dake da iyaka da teku za su ci gajiyar tattalin arzikin teku ba, har ma kasashen dake nesa da teku za su ci moriyar tattalin arzikin teku. Mr. Uhuru Kenyatta, shugaban kasar Kenya ya bayyana cewa, kundin Lome da aka amincewa ya alamta cewa, kasashen Afirka suna da karfin yin tasiri ga sauran sassan duniya, wajen kulla muhimman manufofin neman ci gaba.

Bisa wannan "Kundi na Lome" da aka fitar, an ce, kasashen Afirka za su kara yin hadin gwiwa wajen sa ido, kan yadda ake aiwatar da shi, da kuma yaki da laifuffukan 'yan fashin teku, da na cinikayya a yankunan tekun Afirka ba bisa doka ba. Irin wadannan matakan da za su dauka, za su taimakawa duk duniya wajen kare hanyoyin sufurin kayayyaki na kasa da kasa, da kasashen dake da iyaka da teku, wajen bunkasa tattalin arzikin tekun su.

Mr. Faure Essozimna GNASSINGBE, shugaban kasar Togo wadda ita ce ta karbi bakuncin shirya wannan taron koli na AU, ya ce, wani mataki da wata kasa ko wani zai dauka shi kadai, ba zai iya magance matsalolin da ake fuskanta a yankunan teku kamar yadda ake fata ba, a hannu guda matakan da aka dauka cikin hadin gwiwa ne kadai zai iya kare arzikin teku da albartakun teku.

A yayin taron tattaunawa na mata da aka shirya na wannan taron koli, madam Zuma ta shawarci kasashen Afirka da su bunkasa sana'ar kamun kifi kamar yadda ake bunkasa masana'antu, tare da bunkasa sana'o'in kiwon kayayyakin ruwa da yawon shakatawa a teku. Ta kuma kirayi mata da samari, da su halarci harkokin bunkasa tattalin arzikin teku. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China