in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kayayyakin yaki da talauci da aka fara samarwa ya kai 98%
2016-10-18 13:14:14 cri

Jiya, ranar 17 ga wata "rana ce ta yaki da talauci ta kasar Sin" ta karo na 3, kuma "ranar kawar da talauci ta kasa da kasa" ce karo na 24. Har zuwa yanzu, akwai mutane masu fama da talauci kimanin miliyan 10 da suke zaune a yankuna inda babu isassun kayayyakin more rayuwar dan Adam a nan kasar Sin. Sabo da haka, a bara, gwamnatin kasar Sin ta fitar da shirin "sake tsugunar da mutane masu fama da talauci zuwa yankuna mafi dacewa" domin kawar da talauci da wadannan mutane suke fama da shi. A kwanan baya, jami'an kwamitin kula da harkokin bunkasa da yin gyare-gyare na kasar Sin sun bayyana cewa, yawan kayayyakin yaki da talauci da aka fara samarwa ya kai kashi 98 cikin dari. Bisa shirin da aka tsara, a nan gaba ba dadewa ba, za a tabbatar da kowane iyali wanda ke fama da talauci yanzu zai iya fito daga halin fama da talauci kwata kwata.

A cikin "kudurin neman samun nararar kawar da talauci gaba daya" da gwamnatin kasar Sin ta fitar a watan Nuwamban shekarar bara, an nuna cewa, za a hanzarta kaurar da mutane wadanda har yanzu suke zaune a yankunan da babu kakkyawan yanayin zaman rayuwa, da kuma inda bala'u daga indallahi su kan faru a kai a kai zuwa yankuna mafi dacewa ga zaman rayuwarsu. Bayan da hukumomin matakai daban daban suka tantance sau da dama, an tabbatar da cewa, yawan mutanen da za a komar da su zuwa yankuna mafi dacewa ga zaman rayuwarsu kafin shekarar ta 2020 ya kai kusan miliyan 10. A watan Maris na bana, gwamnatin kasar Sin ta nemi a komar da mutane masu fama da talauci kusan miliyan 2 da dubu 500 wadanda suke zaune a yankunan karkara na larduna da jihohi 22 a shekarar 2016. Mr. Yang Qian, wani jami'in hukumar kwamitin kula da harkokin bunkasa da yin gyare-gyare na kasar Sin ya bayyana cewa, "An kaddamar da dukkan ayyukan sake tsugunar da mutane masu fama da talauci a yankuna mafi dacewa ga zaman rayuwarsu a larduna 22 a shekarar 2016, kuma ya zuwa yanzu an riga an kammala ayyuka 2093 daga cikinsu, wato yawan mutanen da suke koma yankuna mafi dacewa ya kai dubu 360. A lokacin da aka tara shirin sake tsugunar da mutane masu fama da talauci a yankuna masu dacewa na shekarar 2016, an fara tsara shirin bunkasa masana'antu wadanda za su iya samar da guraban aikin yi ga wadanda suka fito daga yankuna masu fama da talauci. Sannan a lokacin da ake samar da ayyuka iri iri, an kuma fara horas da mutane masu fama da talauci. Bisa kididdigar da aka yi, yawan mutanen da suka samu horaswa ya kai dubu 620, har ma wadanda suka samu aikin yi suka kai dubu 424. A waje daya, mutane dubu 817.3 za su samu aikin yi a sauran yankuna. Bugu da kari, za a taimaka wa mutane miliyan 1 da dubu 176 ta hanyar bunkasa masana'antu."

Bisa shirin da aka tsara, kasar Sin za ta sake tsugunar da mutane miliyan 10 wadanda har yanzu suke fama da kangin talauci a yankunan karkara zuwa sauran yankuna masu dacewa da yin zama a cikin shekaru 5 masu zuwa. Wannan ne matakin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin yaki da talauci ko tarihin kaurar da jama'a duk fadin duniya. Wannan kuma sabon tunani ne na yaki da kangin talauci da kasar Sin ta samar wa duk duniya. Mr. Bert Hofman, direktan hukumar kasar Sin ta Bankin Duniya ya bayyana cewa, bankin duniya yana kula da yadda kasar Sin take taimaka wa mutane wadanda suke fama da kangin talauci a yankuna dake nesa da garuruwa, kuma zai yi hadin gwiwa da kasar Sin wajen fama da talauci ta sabon salo. Mr. Bert Hofman ya ce, "A kullum muna kula da yadda kasar Sin take taimaka wa mutane wadanda suke zaune kuma suke fama da kangin talauci a yankunan duwatsu dake nesa da manyan birane. Ba su da muhimman kayayykin yau da kullum da ake bukata idan ana son yin zama a can. Sabo da haka, kaurar da su zuwa yankuna masu dacewa da yin zama wata muhimmiyar hanya ce ta daban ga kokarin kawar da talauci. Yanzu bankinmu da ofishin kula da harkokin kawar da talauci na kasar Sin da sauran hukumomin da abin ya shafa muna tattauna ko za a iya shigar da irin wannan salon kawar da talauci a cikin aikin bankinmu domin kokarin cimma nasarar kawar da talauci gada daya a nan kasar Sin. Zamanintar da harkokin ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta, taimaka wa wadanda suke fama da talauci a fannin koyon ilmi, dukkansu sabon salon yin hadin gwiwa a tsakaninmu da hukumomin kasar Sin wajen fama da talauci." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China