in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin kasa ce mafi tsimin makamashi a duniya
2016-10-14 11:01:43 cri

A jiya Alhamis ne a na birnin Beijing na kasar Sin, aka kaddamar da dandalin tsimin makamashi na kasashen Sin da Amurka karo na 7 wanda kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin da ma'aikatar makamashin kasar Amurka suka shirya cikin hadin gwiwa. Yayin dandalin, mataimakin daraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Zhang Yong ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta samu nasarori a fannin tsimin makamashi, kuma ta kasance a kan gaba a wannan fannin a fadin duniya, kuma a nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da kokarin kara kyautata wannan fanni yadda ya kamata.

Dandalin tsimin makamashin da aka shirya tsakanin Sin da Amurka muhimmin dandali ne da sassan biyu suke gudanarwa a fannin tsimin makamashi tare, haka kuma wani muhimmin mataki ne da aka dauka yayin da ake kokarin cimma burin tabbatar da sakamakon shawarwarin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin Sin da Amurka. Ana gudanar da dandalin ne sau daya a kowace shekara, kuma kasashen biyu wato Sin da Amurka su kan shirya dandalin ne ta hanyar karba-karba.

A yayin dandalin, mataimakin daraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Zhang Yong ya bayyana cewa, a cikin shekaru goma da suka gabata, kasar Sin ta samu babban sakamako ta fuskar tsimin makamashi da kuma rage fitar da gurbatacen iska. Zhang Yong ya ce, "Gaba daya adadin makamashin da aka yi amfani da su yayin da ake kokarin samun kudade daga sarrafa dukiyar kasa wato GDP a nan kasar Sin tsakanin shekarar 2006 zuwa 2015 ya ragu da kashi 34 cikin dari, wato adadin makamashin da aka yi tsimin su ya kai tan biliyan 1 da miliyan 570 na kwal, lamarin da ya nuna cewa, an rage fitar da iskar Carbon Dioxide har tan biliyan 3 da miliyan 580, ana iya cewa, gwamnatin kasar Sin ta cimma burinta na karuwar GDP da ta kai kashi 9.6 cikin dari a kowace shekara ta hanyar karuwar amfanin makamashi da ta kai kashi 5.2 cikin dari a kowace shekara."

Alkaluman da bankin duniya ya fitar ya nuna cewa, a cikin shekaru 20 da suka gabata, adadin makamashin da kasar Sin ta yi tsimin su ya kai sama da kashi 50 cikin dari na adadin makamashin da daukacin kasashen duniya suka yi tsimin su, hakan ya nuna cewa, kasar Sin ta kasance kasa ta farko ta fannin tsimin makamashi.

Game da wannan, daraktan ofishin huldar kasa da kasa na sashen makamashi na ma'aikatar makamashin Amurka Robert Sandoli ya yi nuni da cewa, a shekarar 2015 da ta gabata, adadin makamashin da aka tsimin su a fadin duniya ya karu da kashi 1.8 cikin dari, Kuma kasar Sin ce ta fi ba da gudummuwa a wannan fanni. Sandoli ya ce, "An cimma burin kara kyautata hanyar yin amfani da makamashi a fadin duniya, ana iya cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa, saboda adadin makamashin da kasar Sin ta yi tsimin su ta hanyar kara kyautata hanyar yin amfani da su ya kai kashi 5.6 cikin dari a shekarar bara, yanzu dai, ana yin amfani da ma'aunin tsimin makamashi a wuraren fadin duniya da yawansu ya kai kashi 30 cikin dari, amma a shekarar 2010 kuwa, ya kai kashi 11 cikin dari ne kawai."

A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 13 na kasar Sin, gwamnatin kasar ta Sin ta tsai da kudurin cewa, za ta kayyade adadin makamashin da za a yi amfani da su, wato ya zuwa shekarar 2020, kwatankwacin adadin makamashin da za a yi amfani da su ba zai zarta tan biliyan 5 na kwal ba.

Mataimakin daraktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Zhang Yong ya bayyana cewa, hakan ya alamanta cewa, kasar Sin za ta tabbatar da burinta na karuwar adadin GDP da yawansa zai kai kashi 6.5 cikin dari bisa la'akari da karuwar adadin makamashin da za a yi amfani da su da yawansu ba zai wuce kashi 3.1 cikin dari ba a kowace shekara a cikin shekaru biyar masu zuwa. Ana iya cewa, kasar Sin za ta iya fuskantar matsala, Zhang Yong ya jaddada cewa, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari domin kara tsimin makamashi. Yana mai cewa, "Kasar Sin za ta kara kokari matuka domin kara kyautata hanyar yin amfani da makamashi yayin da take kokarin raya tattalin arziki da zaman takewar al'umma a kasar, musamman ma wajen kyautata tsarin makamashi da na sana'o'i. Muddin ana son cimma wannan burin, kamata ya yi a kara mai da hankali kan aikin kirkire-kirkiren fasahohi, tare kuma da raya sana'o'I ta hanyar kiyaye muhalli."

Mai ba da taimako ga ministan makamashin Amurka David Frienman ya bayyana cewa, a watan Satumban bana ne, kasashen Amurka da Sin suka amince da yarjejeniyar Paris a hukumance, wannan yana da muhimmancin matuka, saboda hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka da sauran kasashen ta fannin dakile matsalar sauyin yanayi zai kyautata yanayin kiyaye muhalli da ake ciki yanzu a fadin duniya.

Dandalin ya samu halartar wakilai sama da 200 da suka zo daga hukumomin gwamnatoci da hukumomin nazari da kamfanoni na kasashen biyu wato Sin da Amurka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China